Aljeriya ta sanar da yanke hulɗar diflomasiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), tana zargin ƙasar da aiwatar da matakai da ta bayyana a matsayin “na tsokana da ƙiyayya.”
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, Aljeriya ba ta bayyana takamaiman matakan da take zargin UAE da aikatawa ba.
Jim kaɗan bayan sanarwar Aljeriya, mai ba shugaban UAE shawara kan harkokin diflomasiyya, Anwar Gargash, ya bayyana a shafinsa na X cewa dangantakar diflomasiyya ya kamata ta ginu kan hikima, sadarwa da bayyana muradu a sarari, ba kan “alamomi da ishara masu buƙatar fassara” ba.
Dangantaka tsakanin ƙasashen biyu ta ƙara tsami a cikin 'yan shekarun nan, inda kafafen yaɗa labarai na Aljeriya suka sha sukar UAE tare da zarginta da ƙoƙarin haddasa rikice-rikice a yankin.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Aljeriya ta ce ayyukan UAE sun kai wani matakin da ba za a ƙara ɗaukar su a matsayin abin karɓa ko jurewa ba.
Ma'aikatar ta kuma ce Aljeriya ta “gama amfani da duk hanyoyin da za a bi domin ci gaba da kare dangantakar ƙasashen biyu.”
A nasa martanin, Gargash, ba tare da ambaton Aljeriya kai tsaye ba, ya ce nasarar diflomasiyya tana dogara ne kan bayyana matsayi a sarari, da kuma yadda ake gudanar da muradu da saɓanin ra'ayi cikin hikima.
A cewar Ma'aikatar Harkokin Wajen Aljeriya, an gayyaci jakadan UAE zuwa ma'aikatar, inda aka sanar da shi matakin yanke hulɗar diflomasiyyar.
An kuma ba jakadan wa'adin sa'o'i 48 domin kammala matakan da suka shafi wannan hukunci.