Gwamnatin Jihar Nasarawa ta umarci Hukumar Ilimi ta Bai Ɗaya ta jihar (SUBEB) da ta fara wayar da kan jama’a domin ƙarfafa gwiwar iyaye su mayar da yaran da suka kai shekarun makaranta amma ba sa zuwa ajujuwa.
Gwamnatin ta kuma ce tana shirin kafa kotunan tafi-da-gidanka domin gurfanar da iyayen yaran da aka samu suna yawo a tituna a lokacin karatu.
Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamna Abdullahi Sule kan harkokin jama’a, Peter Ahemba, ne ya bayyana hakan a Lafia ranar Laraba.
Ahemba ya ce SUBEB za ta yi aiki tare da Ma’aikatar Shari’a wajen duba hanyoyin kafa kotunan, sai dai ya ce za a fara da wayar da kan jama’a kafin a fara aiwatar da matakin.
Ya ce daga bisani za a kafa wata tawaga ta musamman da za ta gano yaran da ke yawo a lokacin karatu, tare da bibiyar iyayensu domin ɗaukar matakin shari’a idan ya zama dole.
A wani mataki na tallafa wa ɗalibai, gwamnatin jihar ta ce ta tanadi kayan makaranta sama da 10,000, ciki har da littattafan rubutu, kayan makaranta da takalma, domin rabawa ɗalibai.
Haka kuma, Ahemba ya ce jihar ta kammala ɗaukar malaman makarantun firamare 1,000, waɗanda za a tura musamman zuwa makarantun da ke yankunan karkara.
Ya ce an zaɓi malaman ne bisa cancanta daga cikin sama da mutane 10,000 da suka nemi aikin.