Ministan Ilimi na Najeriya, Maruf Tunji Alausa, ya ce sama da yara miliyan ɗaya da ba sa zuwa makaranta sun koma ajujuwa cikin watanni 20 da suka gabata.

Ministan ya kuma ce kusan ’yan mata miliyan 6.7 sun amfana da shirye-shiryen gwamnati da aka ƙaddamar domin ƙara yawan yaran da ke shiga makaranta da kuma rage yawan waɗanda ke barin karatu.

Alausa ya bayyana hakan ne a Abuja yayin da yake karɓar wakilin UNESCO a Najeriya, Farfesa Isaiah Barreto Da Rosa, wanda ya kai masa ziyara.

Ministan ya buƙaci ƙara haɗin gwiwa tsakanin Ma’aikatar Ilimi da UNESCO domin tallafa wa shirin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na sauya fasalin fannin ilimi.

Ya ce shirin gwamnatin ya fi mayar da hankali kan fannoni shida, ciki har da koyar da sana’o’i, amfani da fasahar kirkirarriyar basira (AI), dawo da yaran da ba sa zuwa makaranta, inganta ilimin ’ya’ya mata da tabbatar da ingancin ilimi.

Alausa ya ce gwamnati na kuma saka hannun jari wajen inganta ƙwarewar malamai, inda ya bayyana burin horas da malamai miliyan ɗaya.

Sai dai ministan ya yi kira da a ƙara mai da hankali kan ilimin yara maza, tare da ci gaba da samun nasarorin da aka samu wajen inganta ilimin ’ya’ya mata.