A rana ta biyu da Kamfanin samar da baƙin mai na Ammasco, ya shirya taron bayar da horo ga shugabannin makanikai daga sassa daban-daban na ƙasar nan, domin ƙara musu ilimi kan sabbin dabaru amfani da injina.

A yau ƙungiyar matuka babura masu ƙada Uku da dangogin su ne aka baiwa horo domin sanin hanyoyin amfani da fasahar CNG.

Taron wanda ya gudana da ya haɗa ƙwararru a fannin baƙin mai da kula da injinan ababen hawa, ya baiwa mahalarta damar sanin sabbin hanyoyi da dabarun da za su taimaka wajen inganta ayyukansu

Da yake jawabi a wajen taron, manajan darakta na rukunin kamfanonin Ammasco, Alhaji Ibrahim Mustapha Ado, ya ce dalilin shirya wannan taron bayar da horo shine tabbatar da cewa makanikai da direbobin baburan adaidaida sahu sun samu ilimin da ya dace kan amfani da ingantaccen baƙin mai da fasahar CNG, domin tabbatar da lafiyar injinan ababen hawa.

Ya ce kamfanin Ammasco na ci gaba da jajircewa wajen samar da baƙin Mai, da binciko sabbin fasahohi na zamani da zasu taimaka wajen ingantuwar lafiyar ababen hawa.

Masana da suka jagoranci horon sun yi bayani kan muhimmancin amfani da ingantaccen baƙin mai, inda suka bayyana cewa amfani da man da ya dace na taimakawa wajen rage matsalolin injina da kuma ƙara wa ababen hawa juriya.

A nasa jawabin, sakataren ƙungiyar kanikawa masu gyaran babura ta jihar Kano, Ibrahim Yusuf Mai Hula, ya yabawa shugaban rukunin kamfanonin Ammasco Alhaji Mustapha Ado Muhammad, bisa shirya wannan horo, da ya ce ya cire su daga cikin duhun rashin sanin yadda ake amfani da baƙin mai da wasu sabbin fasahohi na zamani.

Suma a nasu bangaren direbobin baburan adaidaida sahu da sauran mahalarta taron, da suka amfana da wannan taron bayar da horo sun bayyana farin cikin su da kuma abubuwan da suka koya a wannan taro.