Amurka ta sanar da cewa za ta aika wa Najeriya wasu kayan aikin soja domin taimakawa ƙasar wajen yaƙi da ta’addanci da sauran barazanar tsaro.

Rundunar sojin Amurka mai kula da ayyukan soji a Afirka, AFRICOM, ta ce wani jirgin dakon kaya na rundunar sojin saman Amurka kirar C-17 zai kawo kayan aikin ga Rundunar Sojin Saman Najeriya a ƙarshen wannan mako.

A cewar AFRICOM, kayan aikin na cikin wata yarjejeniyar sayar da kayan aikin soja tsakanin Amurka da Najeriya, wadda ke ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu.

Isar da kayan aikin na zuwa ne yayin da Najeriya ke ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi, ’yan bindiga da sauran ƙungiyoyin da ke barazana ga tsaron ƙasar.

Duk da cewa rundunar sojin Najeriya ta samu wasu nasarori a watannin baya-bayan nan, hare-haren ’yan bindiga da sace mutane domin neman kuɗin fansa na ci gaba da faruwa a wasu sassan ƙasar.

A baya-bayan nan, Amurka da Najeriya sun ƙara haɗin gwiwa wajen musayar bayanan sirri, horas da jami’an tsaro da kuma samar da kayan aikin soja.

A watan Janairu, dakarun Amurka sun kuma kai wasu kayayyakin soja Najeriya domin tallafa wa ayyukan tsaron ƙasar.

Kimanin sojojin Amurka 200 da aka tura Najeriya a farkon shekarar nan domin wani aikin yaƙi da ta’addanci sun koma gida bayan kammala aikin da aka tura su.

Sai dai haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu na ci gaba, inda Amurka ta kuma horas da jami’an Najeriya kan sarrafawa da amfani da jirage marasa matuƙa, yaƙi da abubuwan fashewa da kuma kula da sojojin da suka jikkata a fagen daga.