Rundunar ƴansandan jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon sashen yaƙi da manyan laifuka irin su fashi da makami, garkuwa da mutane da kuma ƙwacen motoci.

Kwamishinan ƴansandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori ne ya ƙaddamar da sashen, mai suna: ‘Violent Crime Response Unit’ (VCRU), a ranar Litinin.

Ya bayyana cewa an kafa rundunar ce bisa umarnin Sufeto-Janar na ƴansanda, Olatunji Rilwan Disu, da kuma tanadin dokar ƴansanda ta shekarar 2020.

Ya ce rundunar zata yi aiki ne bisa tattara bayanan sirri cikin gaggawa tare da haɗin-kan al’umma domin magance matsalolin tsaro da ke ƙaruwa a wasu sassan jihar.

Bakori ya bayyana cewa an zaɓi jami’an rundunar ne bayan horaswa ta musamman kan dabarun yaƙi da manyan laifuka tare da mutunta haƙƙin bil’Adama.

Ya kuma gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa goyon-bayan da yake baiwa harkokin tsaro, tare da kira ga sarakuna da shugabannin al’umma da su riƙa baiwa jami’an tsaro bayanan masu aikata laifi.