Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz, ya ce ƙasar na fuskantar wani gagarumin sauyi a tsarin siyasar jam’iyyu, bayan da jam’iyyar AfD ta masu tsattsauran ra’ayi ta samu gagarumar nasara a zaɓen jihar Saxony-Anhalt da ke gabashin ƙasar.

Merz ya ce sakamakon zaɓen ya zama babban abin damuwa ga jam’iyyar CDU mai ra’ayin mazan jiya, yana mai cewa akwai buƙatar jam’iyyar ta gudanar da nazari mai zurfi kan dalilan da suka haifar da wannan sakamako.

Da yake magana kamar yadda jaridar Bild ta ruwaito, Merz ya ce akwai buƙatar jam’iyyar ta ƙara kusantar jama’a tare da ƙara ƙoƙari wajen fahimtar matsalolinsu.

Ya ce a matsayinsa na shugaban gwamnatin ƙasar, zai ɗauki nauyin tunkarar ƙalubalen da sakamakon zaɓen ya haifar, yana mai cewa ba zai guje wa wannan nauyi ba.

Jam’iyyar AfD ta samu kusan kashi 44 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa, abin da ya sa ta yi kusa da samun cikakken rinjaye a jihar.

A nata ɓangaren, shugabar jam’iyyar AfD ta ƙasa, Alice Weidel, ta yaba da sakamakon, inda ta ce burinsu shi ne samun aƙalla kashi 40 cikin 100 na ƙuri’u a babban zaɓen tarayyar Jamus mai zuwa.

Weidel ta kuma soki Shugaban Gwamnati Friedrich Merz, inda ta zarge shi da kasancewa cikin abubuwan da ke hana Jamus samun ci gaba.