Iran ta yi gargaɗin cewa za ta ɗauki matakan mayar da martani idan kwamitin gudanarwa na Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya, IAEA, ya amince da sabon daftarin ƙudurin da ƙasashen Turai suka gabatar kan shirin nukiliyarta.
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya ce ƙudurin na iya sake kai batun shirin nukiliyar Iran gaban Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya.
Baghaei ya zargi ƙasashen Turai da komawa ga batun shirin nukiliyar Iran a duk lokacin da suka kasa cimma wasu daga cikin manufofinsu, yana mai cewa hakan wata hanya ce ta ƙara matsin lamba kan Tehran.
Ya kuma soki matsayin babban daraktan IAEA, yana zargin cewa wasu daga cikin matakansa na ƙara matsin lamba na siyasa ne kan Iran.
A cewarsa, wannan sabon mataki ya ƙara ƙarfafa matsayin Iran, China da Rasha na cewa tsarin dawo da takunkuman da aka fi sani da “snapback” ba bisa doka yake ba, kuma ba za a iya aiwatar da shi yadda ake shirin yi ba.
Baghaei ya bayyana sabon daftarin ƙudurin a matsayin “maimaita wata hanya mai cutarwa”, yana mai cewa ƙasashen Turai uku da ke jagorantar batun sun rasa tasirinsu sosai wajen warware rikicin shirin nukiliyar Iran.
Ya kuma ce hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan wasu cibiyoyin nukiliyar Iran sun kawo cikas ga ayyukan IAEA, lamarin da ya sa, a halin yanzu, ba zai yiwu hukumar ta gudanar da cikakken bincike a wasu daga cikin cibiyoyin ba.
Sai dai ƙasashen Turai da IAEA na matsa lamba domin a ci gaba da gudanar da bincike a cibiyoyin nukiliyar Iran, musamman waɗanda hare-hare suka shafa.
Baghaei ya jaddada cewa idan kwamitin gudanarwa na IAEA ya amince da ƙudurin, Iran za ta ɗauki matakan da ta kira na mayar da martani, domin nuna adawarta da matakin.