Mijin shugabar ƙasar Tanzania, Samia Suluhu Hassan, Hafidh Ameir Hassan, ya rasu a yau Litinin, 7 ga watan Satumban 2026.
Mataimakin shugaban ƙasar Tanzania, Deogratius Ndejembi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a yau.
Sanarwar ta ce Hafidh Ameir Hassan ya rasu ne yayin da yake karɓar magani a Asibitin Emilio Mzena Memorial da ke Zanzibar, sakamakon wata matsalar lafiya da ta shafi zuciya.
An ce ya rasu ne da misalin ƙarfe 8:00 na safe.
Sanarwar ta ƙara da cewa tuni aka fara shirye-shiryen jana’izarsa, wadda za a gudanar a yankin Kizimkazi da ke Zanzibar.