Iran ta gargadi Koriya ta Kudu kan duk wani shiri na tura dakarunta ko shiga ayyukan soji a Tekun Fasha da mashigar Hormuz, tana mai cewa hakan zai haifar da mummunan sakamako.
Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmail Baghaei, ne ya yi gargadin a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X da harshen Koriya.
Baghaei ya ce Iran za ta ɗauki duk wani kasancewar sojojin Koriya ta Kudu ko shiga ayyukan soji a yankin a matsayin goyon bayan Amurka, tare da yin gargadin cewa hakan zai haifar da mummunan sakamako.
Gargadin na Iran na zuwa ne yayin da gwamnatin Koriya ta Kudu ke nazarin hanyoyin da za ta iya taimakawa wajen tabbatar da tsaron jiragen ruwa da kuma ’yancin zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz.
Rahotanni sun ce Seoul na fuskantar matsin lamba daga Amurka domin ta ƙara taka rawa wajen ayyukan tsaro a yankin, amma har yanzu ba ta yanke shawarar karshe kan tura sojojinta ba.