Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci dukkan Ma’aikatun gwamnati na ƙasa, wato MDAs, da su sauya tsarin aikinsu zuwa na zamani ta hanyar amfani da fasahar dijital tare da daina amfani da takardu a harkokin gudanarwa.

Tinubu ya bayar da wannan umarni ne yayin bikin buɗe taron International Civil Service Conference 2026 da aka gudanar a Abuja.