Ministan harkokin wajen Koriya ta Kudu, Cho Hyun, ya ce a ranar Laraba wani jirgin tankar man ƙasar Koriya da ke ɗauke da ɗanyen mai ya ratsa ta mashigar Hormuz tare da haɗin kan hukumomin Iran.

Sai dai bai bayar da ƙarin bayani game da jirgin ba yayin jawabinsa a wani zaman sauraron majalisa a birnin Seoul.

Bayanan jigilar jirgin daga kamfanin LSAG sun nuna cewa babban tankar man mai suna Universal Winner mai ɗauke da tutar Koriya ta Kudu, wanda ke ɗauke da ganga miliyan biyu na ɗanyen man Kuwait, yana barin mashigar Hormuz.

Ratsawar wannan tankar mai tare da haɗin kan hukumomin Iran na zuwa ne bayan da wani jirgin dakon kaya na Koriya mai suna HMM Namo ya fuskanci hari daga “jirage marasa matuƙa guda biyu da ba a san ko su wanene ba” a kusa da mashigar Hormuz kimanin makonni biyu da suka gabata, wato ranar 4 ga watan Mayu.