Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Nijeriya (NCDC) ta sanar da tsaurara matakan sa ido da bincike a dukkan iyakokin ƙasar da filayen jiragen sama, domin hana cutar Ebola shigowa Nijeriya.
Babban Daraktan NCDC, Dr. Jide Idris, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Lahadi. Ya ce hukumar tana ƙara sanya ɗakunan bincike cikin shirin ko-ta-kwana, da shirin hana yaɗuwar cutar, da wayar da kan jama’a a duk faɗin ƙasar.
Matakin ya biyo bayan ayyana cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo (DRC) da makwabciyarta Uganda a matsayin "babbar matsala ta lafiya da ta shafi duniya baki ɗaya" daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO). Wannan kuma ya faru ne sakamakon mutuwar mutane akalla 88 da sama da 300 da ake zargin sun kamu da cutar.
Babban Daraktan WHO, Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus, ne ya sanar da matakin gaggawa. Cutar wacce ta fara daga lardin Ituri a gabashin Congo, ta riga ta bazu har zuwa birnin Kampala na Uganda.
Matakan da Nijeriya ta ɗauka:
Duk da cewa kawo yanzu ba a samu wani mai cutar a Nijeriya ba, NCDC ta ce ba za ta yi sakaci ba saboda yawan zirga-zirgar mutane tsakanin kasashen Afirka.
Dr. Jide Idris ya umarci kwamishinonin lafiya na jihohi da su gaggauta farfaɗo da cibiyoyin agajin gaggawa. Matakan sun haɗa da:
- Tsananta binciken lafiyar matafiya a filayen jiragen sama na ƙasa da ƙasa, iyakokin ƙasa, da gaɓar teku.
- Tura kayan aiki da bincike, da samar da kayan kariya na musamman da na’urorin auna zafin jiki ga ma’aikatan lafiya.
- Tanadin wuraren killace marasa lafiya da dabarun binne gawawwakin cikin aminci.
Gargadi ga jama’a:
NCDC ta bukaci al’ummar Nijeriya da su kwantar da hankula, guji yada jita-jita, kuma su kiyaye matakan kariya masu zuwa:
- Wanke hannaye akai-akai da ruwa da sabulu.
- Guje wa taɓa jini, amai, gumi, ko sauran ruwan jikin wanda ke da alamun rashin lafiya.
- Guje wa cin naman daji ko taɓa gawar dabbobin da ba a san sanadin mutuwarsu ba.
- Kai rahoton duk wanda ke da alamun zazzabi mai tsanani, ciwon kai, amai, ko zubar jini, musamman idan yana da tarihin tafiya ƙasashen da cutar ta yaɗu.