Jigo a jam'iyyar ADC Dele Momodu ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels.

Inda ya ce, muddin ‘yan adawa na son kayar da Tinubu a 2027, dole su haɗa kai maimakon rarrabuwa a doron yanki-yanki.

Dele Momodu ya shawarci ‘yan takarar Kudu irin su Goodluck Jonathan, Peter Obi da Seyi Makinde da su zauna su cimma matsaya kan ɗan takara guda domin gujewa raba ƙuri’un Kudu.

Momodu ya jaddada cewa tsarin maslaha (consensus) shi ne mafi dacewa idan har ‘yan adawa suna son kafa hamayya mai ƙarfin da za ta kayar da Tinubu a zaɓen 2027