Sanarwar haɗin gwuiwar tsakanin sojin Najeriya da kuma rundunar sojin Amurka dake Afirka ta ce, al-Minuki da aka kashe ne ke taimakawa wajen harkokin kafofin yaɗa labaran ƴan ta’addan da kuma kuɗaɗen da ake amfani da su wajen samar da makamai tare da jirage marasa matuƙa.
Kwamandan rundunar Amurkar Janar Dagvin Anderson ya tabbatar da wannan nasarar lokacin da yake yiwa majalisar dokokin Amurka bayani dangane da aikin da suke yi na haɗin gwuiwa, inda ya kuma bayyana irin taimakon da suke samu daga sojojin Najeriya wajen gabatar musu da bayanan asiri da kuma taimaka musu wajen aikin.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya jinjinawa shugaban Amurka Donald Trump dangane da goyan bayan da ya ke bai wa ƙasar, tare da buƙatar ci gaba da kai munanan hare hare a yankunan da ƴan ta'addan su ke a fadin ƙasar.