Hukumar kula da makamashi ta duniya ta ce yaƙin Iran ya janyo ƙaruwar sayen motoci masu amfani da lantarki a duniya da kusan kashi 28 cikin 100.


Hukumar ta danganta wannan ƙaruwa da hauhawar farashin mai da ya biyo bayan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila.


Rahoton ya ce tsadar mai ya sa mutane da dama sun koma amfani da motocin lantarki domin rage kashe kuɗin sufuri.


A cewar hukumar, kusan ƙasashe 30 sun samu ƙarin masu sayen motocin da ke amfani da lantarki a watan Maris, ciki har da ƙasashen Latin Amurka inda aka samu ƙaruwa da kashi 75 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.