Hukumar Tara Haraji ta Jihar Kano, ta ƙaddamar da sabon ginin ofisoshin sashen bin doka da tabbatar da biyan haraji domin inganta aikin ma’aikata da Ƙarfafa tsarin tattara haraji a fadin jihar.
Sshugaban hukumar, Dakta Zaid Abubakar, ne ya bayyana hakan yayin bikin Ƙaddamar da ginin da aka gudanar jiya Talata.
Ya ce samar da sabbin ofisoshin na daga cikin ƙoƙarin hukumar na samar da ingantaccen wajen aiki ga ma’aikata domin ƙara musu ƙwarin gwiwa wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Shugaban hukumar ya ƙara da cewa sabon ginin zai taimaka wajen inganta tsarin bin diddigi da tabbatar da biyan haraji tare da bunƙasa ayyukan gudanarwa a hukumar.