Duk da kasancewar Premier League na daga cikin gasannin ƙwallon ƙafa mafi samun kuɗaɗen shiga a duniya, wani sabon rahoto ya nuna cewa ƙungiyoyin gasar sun yi asarar kusan dala biliyan ɗaya a kakar 2024/25.

Rahoton ya bayyana cewa duk da tara fam biliyan 6.8 na kuɗaɗen shiga, yawan kashe kuɗi kan sayen ’yan wasa, albashi da kuɗaɗen dillalai ya sa kuɗaɗen fita suka zarce abin da ake samu.

Chelsea FC ta kafa tarihin asarar kuɗi mafi muni a tarihin gasar, bayan ta yi asarar fam miliyan 262 kafin haraji a shekarar kuɗin da ta ƙare ranar 30 ga Yunin 2025. Salon ƙungiyar na sayen matasan ’yan wasa daga sassa daban-daban na duniya ya zama abin da ake ganin ya ƙara ta’azzara matsalar kashe kuɗi a gasar.

Haka kuma Tottenham Hotspur FC ta yi asarar fam miliyan 121 duk da karin kuɗaɗen shiga daga sabon filin wasanta da kuma nasarar lashe kofin Europa.

Masanin harkokin kuɗi a ƙwallon ƙafa, Kieran Maguire, ya ce matsalar Gasar Firimiya ita ce ƙungiyoyi suna shiga gasar kashe kuɗi domin neman nasara.

Ya ce, “A ƙarshe abin ya koma tamkar takarar tara makamai wajen gogayya kan sayen ’yan wasa da biyan albashi.”

Rahoton ya nuna cewa ƙungiyoyin gasar sun kashe kusan fam biliyan 3 wajen sayen ’yan wasa a kasuwar bazarar bara, inda sayen Alexander Isak da Liverpool FC ta yi kan fam miliyan 125 ya kafa sabon tarihin cinikin ɗan wasa a Ingila.

Albashin ’yan wasa ya kuma haura zuwa fam biliyan 4.4, yayin da kuɗaɗen dillalai suka kai sabon matsayi mafi girma, lamarin da ya jawo ƙorafi daga magoya baya kan yadda kuɗaɗe ke fita daga wasan yayin da farashin tikiti ke ƙaruwa.

Ana sa ran sabbin ƙa’idojin kashe kuɗi da za a fara amfani da su a kakar wasa mai zuwa za su takaita yawan kuɗin da ƙungiyoyi za su iya kashewa kan albashi, canja ’yan wasa da dillalai domin rage asarar kuɗi.