Rundunar ’yan sandan jihar Yobe ta kama wasu mutane da ake zargi da aikata laifuka daban-daban tare da kwato babur da saniyar sata a wasu samame da ta gudanar a Garin Alkali da ke karamar hukumar Bursari.


‎A wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Dungus Abdulkarim, ya fitar, ya ce jami’an rundunar sun kama wani mutum mai suna Abubakar Haruna mai shekaru 30 daga Lafiya Lamurde a jihar Adamawa, wanda ake zargi da kwarewa wajen satar babura a kasuwanni da wuraren taruwar jama’a.

‎Bayan faruwar lamarin, wasu mutane sun bi sawunsa domin kama shi, inda a yayin gudun tsira ya buge wani dattijo mai suna Sabo Yahaya mai shekaru 72 daga kauyen Garin Goje a karamar hukumar Jakusko.

‎Sanarwar ta ce dattijon ya samu karaya a kafarsa ta hagu, kuma an garzaya da shi zuwa Asibitin Kwararru na Gashua kafin daga bisani a mayar da shi FMC Nguru domin ci gaba da kula da lafiyarsa.