Shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin ya fara ziyarar aiki ta kwanaki biyu a ƙasar China a yau Talata, kwanaki kaɗan bayan ziyarar da Donald Trump ya kai birnin Beijing, wadda aka fi mayar da hankali kan harkokin kasuwanci amma ba tare da cimma matsaya kan yaƙin Ukraine ko rikicin Iran ba.

A yayin ziyarar, Putin zai gana da shugaban China, Xi Jinping domin tattauna yadda za a ƙara ƙarfafa alaƙa da haɗin kai tsakanin Moscow da Beijing, kamar yadda fadar Kremlin ta bayyana.

Ana sa ran shugabannin biyu za su tattauna batutuwan da suka shafi siyasar duniya da yankuna daban-daban, tare da sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyi da matsayoyi na bai ɗaya.

Haka kuma, Putin zai gana da Firaministan China, Li Qiang domin tattauna haɗin gwiwa a fannonin tattalin arziƙi da kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu.

Ziyarar na zuwa ne yayin bikin cika shekaru 25 da kafa yarjejeniyar ƙawance tsakanin China da Rasha a shekarar 2001, da kuma ƙungiyar Shanghai Cooperation Organisation, wadda Beijing ke jagoranta tare da wasu ƙasashen Asiya.

Ko da yake Trump ya bayyana cewa ya cimma yarjejeniya kan kasuwanci da China a ziyararsa ta baya-bayan nan, Beijing ba ta tabbatar da hakan a hukumance ba, kuma babu wata alama da ke nuna cewa China ta sauya matsayarta game da yaƙin Ukraine.

Tattaunawar da ake yi domin kawo ƙarshen yaƙin Ukraine ta samu tsaiko musamman bayan ɓarkewar rikicin Iran, yayin da Kyiv ke neman Amurka ta matsa wa Beijing lamba domin amfani da alaƙarta da Moscow wajen taimakawa wajen kawo ƙarshen yaƙin.

Putin ya kai ziyara China sau 13 tun bayan hawansa mulki, yayin da Xi Jinping ya kai ziyara Rasha sau 11, amma sau uku kacal ya ziyarci Amurka.

China dai na ci gaba da bayyana kanta a matsayin ƙasar da ba ta da hannu kai tsaye a yaƙin Ukraine, tana mai kira ga tattaunawa da tsagaita wuta. Sai dai ƙasashen yammaci sun sha zargin wasu kamfanonin China da taimaka wa Rasha ta fuskar kayan aiki da tallafin yaƙi — zargin da Beijing ke ci gaba da musantawa.