Raphinha ya yi martani kan jita-jitar da ake ci gaba da yaɗawa cewa zai bar FC Barcelona, inda ya bayyana rahotannin a matsayin ƙarairayi marasa tushe.
A wata hira da shafin ESPN, tauraron ɗanwasan na Brazil ya ce tun ranar da ya koma Barcelona ake ta hasashen zai bar ƙungiyar.
Raphinha ya ce, “Akwai wani ƙato da ba shi da aiki sai ƙarya… Tun da na zo Barcelona ake ta hasashe kan tafiyata daga kulob ɗin tun ran farko da na zo.”
Duk da cewa bai ambaci sunan wanda yake nufi ba, kalamansa sun nuna rashin jin daɗinsa kan rahotannin da ake yaɗawa game da makomarsa a ƙungiyar.
Ɗanwasan mai shekaru 29 yana da kwantiragi da FC Barcelona har zuwa shekarar 2028, lamarin da ke nuna cewa babu wata tattaunawa ta gaggawa kan tsawaita zamansa a yanzu.
Tun bayan zuwansa Barcelona, Raphinha ya taka rawar gani duk da yawan raunin da ya riƙa fuskanta. Ya zura ƙwallaye 19 tare da bayar da taimakon ƙwallo takwas a wasanni 31 da ya buga.