AMMASCO RADIO NEWSROOM

Duniya

Nico Páz ba zai koma Inter ko wata ƙungiya ba a wannan bazarar, kamar yadda Cesc Fabregas ya bayyana!

Nico Páz ba zai koma Inter ko wata ƙungiya ba a wannan bazarar, kamar yadda Cesc Fabregas ya bayyana! “Zan iya tabbatar muku cewa Nico Páz zai buga wa 𝐑𝐄𝐀𝐋 𝐌𝐀𝐃𝐑𝐈𝐃 ko kuma 𝐂𝐎𝐌𝐎 kawai, babu wata ƙungiya daban,” in ji Fabregas. Real Madrid na da damar dawo da shi kan €9m a wannan bazarar, sannan kuma akwai damar €10m a shekarar 2027. Real Madrid tare da sabon koci José Mourinho ne za su yanke hukunci nan ba da jimawa ba.

Shugaban kasar Kenya William Ruto ya ce gwamnatinsa za ta rage farashin man dizel a ƙasar

Shugaban kasar Kenya William Ruto ya ce gwamnatinsa za ta rage farashin man dizel a ƙasar domin tallafa wa masu amfani da shi, biyo bayan zanga-zangar da aka yi kan tsadar makamashi sakamakon rikicin Gabas Ta Tsakiya. A cikin makon nan, masu motocin sufurin haya a Kenya sun gudanar da yajin aikin kwanaki biyu, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu tare da jikkata wasu kusan 30. Wannan mataki ya faru ne saboda fushin jama’a kan tsadar man fetur da ta janyo tsadar rayuwa. A cikin jawabin nasa a talabijin, Ruto ya ce ya bayar da umarnin rage farashin dizel a tsarin farashi na watannin Yuni z

Ministan kiwon lafiya na Jamhuriyar demokkuradiyyar Congo,Samuel Kamba ya bayyana cewa cutar da ta bullu a ƙasar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 153

Ministan kiwon lafiya na Jamhuriyar demokkuradiyyar Congo,Samuel Kamba ya bayyana cewa cutar da ta bullu a ƙasar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 153,daga cikin mutane 626 da aka gano sun kamu da ita. Ministan ya bayyana yankunan Ituri dake karkashin ikon jihar Bunia da yankin Mongwalu ida lamarin ya fi kamari,duk da cewa akwai wasu yankuna da cutar ta bullu. Ya zuwa wannan lokaci,arewacin Kivu ne cutar ta bayyana inda aka gano mutum daya da ya kamu da ita a Goma,biyu a Butembo,wacce ba ta tsaya a nan ba,ta kuma bazu zuwa kudancin Kivu. Rahotanni daga yankunan da ke karkashin ikon ƴan tawayen M

Shugaban ƙasar amurika Donald Trump ya sanar da cewa tattaunawar zaman lafiya da Iran ta kai matakin karshe

Shugaban ƙasar amurika Donald Trump ya sanar da cewa tattaunawar zaman lafiya da Iran ta kai matakin karshe, inda ya ba wa kasar wa’adin kwanaki biyu zuwa uku kacal domin ta amince da yarjejeniyar, ko kuma ta fuskanci mummunan harin soja. Wannan sanarwa ta zo ne bayan matakin da Trump ya ɗauka na dakatar da wani babban harin bam da Amurka ta shirya kai wa Iran. Shugaban ya bayyana cewa ya janye harin ne bayan buƙata da shawara daga shugabannin ƙasashen Larabawa na yankin Gulf, waɗanda ke ganin akwai alamun samun maslaha. Trump ya jaddada cewa lokaci yana ƙure wa Iran, yana mai barazanar cewa

Jirgin tankar man ƙasar Koriya da ke ɗauke da ɗanyen mai ya ratsa ta mashigar Hormuz tare da haɗin kan hukumomin Iran.

Ministan harkokin wajen Koriya ta Kudu, Cho Hyun, ya ce a ranar Laraba wani jirgin tankar man ƙasar Koriya da ke ɗauke da ɗanyen mai ya ratsa ta mashigar Hormuz tare da haɗin kan hukumomin Iran. Sai dai bai bayar da ƙarin bayani game da jirgin ba yayin jawabinsa a wani zaman sauraron majalisa a birnin Seoul. Bayanan jigilar jirgin daga kamfanin LSAG sun nuna cewa babban tankar man mai suna Universal Winner mai ɗauke da tutar Koriya ta Kudu, wanda ke ɗauke da ganga miliyan biyu na ɗanyen man Kuwait, yana barin mashigar Hormuz. Ratsawar wannan tankar mai tare da haɗin kan hukumomin Iran na zuwa

China Da Rasha Sun Haɗa Baki Wajen Sukan Manufofin Amurka A Duniya

Bayan wata gagarumar tattaunawa da ta gudana tsakanin Shugaba Xi Jinping da takwaransa Vladimir Putin, kasashen China da Rasha sun fito fili sun kalubalanci dabarun siyasa da na soja da Amurka ke amfani da su, musamman a kasashe irin su Iran da Venezuela. Abubuwan Da Kasashen Biyu Suka Soki Katsalandan Cikin Gida: Shugabannin biyu sun nuna adawa da yunkurin kifar da gwamnatoci ko rura wutar fitina a cikin kasashen da ke cin gashin kansu. Keta Dokokin Duniya: Sun bayyana cewa matakan barazanar soja ko farmakin ba-zata da Amurka ke yi, suna gurbata tsarin da Majalisar Dinkin Duniya ta shimfida t

Masu Sayen Motocin Lantarki Sun Ƙaru Da Kashi 28% Sanadiyyar Rikicin Iran

Hukumar kula da makamashi ta duniya ta ce yaƙin Iran ya janyo ƙaruwar sayen motoci masu amfani da lantarki a duniya da kusan kashi 28 cikin 100. Hukumar ta danganta wannan ƙaruwa da hauhawar farashin mai da ya biyo bayan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila. Rahoton ya ce tsadar mai ya sa mutane da dama sun koma amfani da motocin lantarki domin rage kashe kuɗin sufuri. A cewar hukumar, kusan ƙasashe 30 sun samu ƙarin masu sayen motocin da ke amfani da lantarki a watan Maris, ciki har da ƙasashen Latin Amurka inda aka samu ƙaruwa da kashi 75 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

Mutane huɗu sun mutu a zanga-zangar tsadar man fetur a Kenya

Aƙalla mutane huɗu ne suka rasa rayukansu sakamakon zanga-zangar adawa da tsadar man fetur da hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar Kenya. Rahotanni sun bayyana cewa dubban mutane ne suka fito kan tituna a manyan biranen ƙasar domin nuna rashin jin daɗinsu kan matsin rayuwa da kuma ƙarin kuɗin man fetur. An kuma samu rikici tsakanin masu zanga-zangar da jami’an tsaro, inda aka yi amfani da barkonon tsohuwa da harsasai wajen tarwatsa masu zanga-zangar a wasu yankuna. Masu zanga-zangar na zargin gwamnatin shugaban ƙasar, William Ruto da gaza magance matsalolin tattalin arziƙi da hauhawar farashin

Ebola ta kashe mutum 131 a Congo

Ɓarkewar cutar Ebola mai saurin yaɗuwa ta kashe aƙalla mutane 131 a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, kamar yadda jami’an ƙasar ta tsakiyar Afirka suka bayyana bayan sabunta adadin daga mutum 118 da aka sanar a baya. Likitoci na ci gaba da bibiyar sama da mutum 500 da ake zargin sun kamu da cutar. Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) za ta gudanar da zaman kwamitin gaggawa a ranar Talata domin tattauna yadda cutar ke ƙara yaɗuwa. “An shirya zaman kwamitin gaggawa nan gaba a yau,” in ji wani mai magana da yawun WHO ga AFP, kwanaki biyu bayan shugaban hukumar lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya ya ayyana

An kama wata mata a Kenya bisa zargin damfarar dala 431,000

Yansanda a Kenya sun kama wata mata da ake zargi da damfarar wani Ba’amurke dala 431,000 bayan ta yi masa alkawarin samar masa da sandunan zinare na gaske masu nauyin kilo 400. Hukumar binciken manyan laifuka ta Kenya, Directorate of Criminal Investigations, ta bayyana a ranar Lahadi 17 ga Mayu, 2026 cewa an kama matar mai suna Mildred Kache, wadda aka fi sani da Sabreena Ayesha, a unguwar Kilimani da ke birnin Nairobi, babban birnin ƙasar. Hukumar ta bayyana Kache a matsayin mace mai iya jan hankali da magana, tana mai cewa ita da wasu abokan haɗinta sun shawo kan Ba’amurken ne ta hanyar tabb

‎Hukumomin lafiya na Afirka sun tabbatar da ɓullar cutar Ebola a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo.

‎Hukumomin lafiya na Afirka sun tabbatar da ɓullar cutar Ebola a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo , lamarin da ya janyo mutuwar mutane da dama. ‎Cibiyar Kula da Cututtuka ta Afirka ta bayyana cewa an samu mutane 246 da ake zargin sun kamu da cutar, yayin da mutum 65 suka rasu, ciki har da mutum huɗu da gwaje-gwaje suka tabbatar sun kamu da Ebola. ‎Hukumar ta ce an tabbatar da ɓullar cutar ne a lardin Ituri da ke gabashin ƙasar, inda ake ci gaba da sa ido tare da shirya taron gaggawa da ƙasashen Uganda da Sudan ta Kudu domin ƙarfafa matakan sa ido da dakile yaduwar cutar a yankunan. ‎Cu

Yau juma’a ake cika shekaru 78 da fara mamayar da Isra’ila ke yiwa yankunan Falasɗinawa.

Yau juma’a ake cika shekaru 78 da fara mamayar da Isra’ila ke yiwa yankunan Falasɗinawa, ranar da ake yiwa laƙabi da Naƙba ko kuma ranar baƙin ciki ga yankin na Falasɗinu. A ranar 15 ga watan Mayun shekarar 1948 ne, Isra’ilar ta fara mamaye yankunan Falasɗinawa tare da mayar da su mallakinta, inda a rana guda ta tayar da jumullar mutanen da yawansu ya kai dubu 700 zuwa miliyan guda baya ga rushe garuruwa fiye da 530, kuma tun daga wancan lokaci har kawo yanzu miliyoyin Falasɗinawa ke rayuwa a matsugunan wucin gadi ko sansanonin ƴan gudun hijira yayin da da dama ke rayuwa a ƙasashen maƙwabta ba

An rantsar da C Joseph Vijay a ministan Tamil Nadu

An rantsar da tauraron fina-finan Indiyan nan da ya jagoranci jam’iyyarsa wajen lashe zaɓen majalisar dokokin jihar Tamil Nadu a kudancin Indiya, a matsayin babban ministan jihar. C Joseph Vijay, jagoran jam’iyyar TVK (Tamilaga Vettri Kazhagam), ya sha rantsuwar kama aiki a gaban dubban magoya bayansa a Chennai, babban birnin jihar. Mista Vijay zai jagoranci gwamnatin haɗaka, wadda jam’iyyarsa ta lashe kujeru 108 a majalisar dokokin jihar. Jam’iyyarsa ta TVK ta ƙulla ƙawance da wasu jam’iyyun uku domin samun rinjayen kujeru 118 da take buƙata domin kafa gwamnati.

Hukumomi a Chad sun ayyana dokar ta ɓaci na tsawon kwanaki 20 a yankin Lake Chad sakamakon matsalolin tsaro da hare-haren da ake samu a yankin.

Chad ta ayyana dokar ta ɓaci a yankin Lake Chad kwanaki kaɗan bayan da mayakan Boko Haram suka kashe jami’an soji aƙalla 24 a wani sansanin soji da ke Barka Tolorom. Dokar ta ɓacin za ta fara aiki daga daren 7 zuwa daren 27 ga watan Mayun 2026. Hukumomi sun bayyana cewa za a rufe iyakokin yankin tare da sanya dokar hana zirga-zirga domin ƙarfafa matakan tsaro. A wata sanarwa da ya gabatar ta gidan talabijin na ƙasar, mai magana da yawun gwamnatin Chadi, Gassim Cherif, ya ce ɗaukar matakin zai taimaka wajen kamo waɗanda ake zargi da kai harin, tare da dakile zirga-zirgar mutane, motoci da mashi

Ba za mu tsaya muna kallon yadda ake cin zarafi da wulakanta ’yan ƙasarmu ba, in ji Bianca Odumegwu Ojukwu.

Ministar harkokin wajen Najeriya ta bayyana cewa ƙasar ba za ta amince da ci gaba da cin zarafi da wulakanta ’yan Najeriya a South Africa ba. Ta bayyana hakan ne yayin tattaunawa kan dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu da kuma ƙalubalen da wasu ’yan Najeriya ke fuskanta a ƙasar. Ojukwu ta jaddada cewa gwamnatin Najeriya za ta ci gaba da kare mutunci da haƙƙin ’yan ƙasarta a duk inda suke a duniya, tare da kira da a mutunta su kamar sauran al’ummomi. Kalaman nata na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun koke-koke kan hare-hare, cin zarafi da sauran matsalolin da wasu ’yan Najeri

Donald Trump ya dakatar da wani shiri da aka gabatar domin taimaka wa jiragen ruwa su rika wucewa cikin kariya ta mashigar Strait of Hormuz,

Rahotanni sun nuna cewa an dakatar da shirin ne bayan tattaunawa da jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki kan yiwuwar tasirin sa ga harkokin siyasa da tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya. Mashigar Hormuz na da muhimmanci matuƙa ga kasuwancin man fetur na duniya, kuma duk wata matsala a yankin kan haifar da tashin farashin mai da fargaba a kasuwannin duniya. Matakin na Trump ya zo ne a lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan tsaro da zaman lafiya a yankin Gulf, musamman dangane da hulɗar Amurka da Iran

Afirka ta Kudu ta nuna damuwa kan shirin Najeriya na kwashe ƴan kasarta

Afirka ta kudu ta bayyana damuwarta kan shirin Najeriya na kwaso ƴan ƙasarta da ke son komawa gida. Ministan harkokin wajen ƙasar Ronald Lamola ya tattauna da takwararsa ta Najeriya domin lalubo hanyoyin da za a kawo ƙarshen zaman tankiyar da ke tsakanin ƙasashen biyu. '' Mun san cewa Najeriya ƙasa ce mai ƴancin ɗaukr irin wannan mataki na kwashe ƴan ƙasarta da ke son tafiya, amma muna ganin cewa yin hakan ba zai magance matsalar shigar baƙi ta hanyar da ba ta dace ba.'' a cewar Ronald Lamola. A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, ministar harkokin wajen Najeriya Bianca Odumegwu - Ojukwu