AMMASCO RADIO NEWSROOM

Wasanni

Wanene Zai Maye Gurbin Kieran McKenna a Ipswich Town?

Ƙungiyar Ipswich Town na neman sabon koci bayan tsohon mai horar da ita, Kieran McKenna, ya yi murabus duk da nasarar da ya samu wajen dawo da ƙungiyar gasar Premier League bayan shekara guda a waje. A halin yanzu, tsohon kocin Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer, da kuma tsohon kocin Wolverhampton Wanderers, Gary O'Neil, na daga cikin waɗanda ake ganin suna kan gaba wajen karɓar aikin horar da ƙungiyar ta Portman Road. Duk da rashin koci a halin yanzu, magoya bayan Ipswich na ɗokin ganin yadda ƙungiyar za ta fara kakar wasanta a Premier League. Wasan farko na Ipswich zai kasance a gida da

Manchester City Za Ta Kara da United da Liverpool Tun Farkon Kaka

Ƙungiyar Manchester City na ci gaba da shirye-shiryen sabon kakar wasa yayin da ake rade-radin neman magajin kocinta, Pep Guardiola. Rahotanni na nuna cewa City na nazarin yiwuwar ɗaukar Enzo Maresca domin jagorantar ƙungiyar, kuma ana sa ran sabon kocin zai fara aiki kafin fara kakar wasa mai zuwa. Duk wanda zai karɓi ragamar horar da Manchester City, zai fuskanci gwaji mai tsauri tun daga farkon kakar wasa, domin ƙungiyar za ta kara da manyan abokan hamayyarta biyu cikin wasanni shida na farko. Jadawalin wasannin farko na Manchester City ya haɗa da: Bournemouth (Gida) Crystal Palace (Waje) C

Coventry Ta Koma Premier League Bayan Shekaru 25

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Coventry City za ta fara sabon babi a tarihinta yayin da ta koma gasar Premier League bayan shafe shekaru 25 ba ta buga gasar ba. A wasan buɗe kakar wasa, Coventry za ta karɓi baƙuncin Arsenal, wanda ke daga cikin manyan ƙungiyoyin gasar. Wasan zai haɗa ƙungiyar da ta lashe gasar Championship da kuma ɗaya daga cikin fitattun ƙungiyoyin Premier League. Bayan wannan wasan, Coventry za ta fuskanci ƙalubale masu tsauri, inda za ta yi wasa da Manchester City, kafin daga bisani ta ziyarci Hull City. Duk da wahalar wasannin farko da ke gabanta, komawar Coventry Premier League

Ƙungiyoyin Premier League da Suka Cancanci Gasar Turai a Kakar Wasa Mai Zuwa

An tabbatar da ƙungiyoyin Premier League da za su wakilci Ingila a manyan gasar ƙwallon ƙafa na Turai a kakar wasa mai zuwa. Ƙungiyoyi biyar sun samu tikitin shiga Gasar Zakarun Turai (UEFA Champions League), wato: Arsenal Manchester City Manchester United Aston Villa Liverpool A Gasar Europa League kuwa, ƙungiyoyi uku ne za su fafata, waɗanda suka haɗa da: Bournemouth Sunderland Crystal Palace Yayin da Brighton & Hove Albion za ta wakilci Ingila a Gasar UEFA Conference League. Hakan na nufin ƙungiyoyi tara daga Premier League ne za su shiga gasannin Turai daban-daban a kakar wasa mai zuwa, ab

Canada ta hana Thomas Partey shiga ƙasar, zai rasa wasan Ghana da Panama

Rahotanni sun nuna cewa hukumomin Canada sun ƙi amincewa da takardar izinin shiga ƙasar da ɗan wasan tsakiyar Ghana, Thomas Partey , ya nema, lamarin da zai hana shi buga wasan farko na Ghana a gasar cin kofin duniya da za ta yi da Panama a birnin Toronto ranar 17 ga Yuni. Hukumar FIFA ta tabbatar da cewa Partey ba zai samu damar tafiya daga sansanin tawagar Ghana da ke Boston a Amurka zuwa Canada ba, bayan da gwamnatin Canada ta ƙi amincewa da buƙatar takardar izinin shigarsa. FIFA ta jaddada cewa ba ta da hannu a harkokin ba da biza, domin hakan na ƙarƙashin ikon ƙasashen da ke karɓar baƙunc

Shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid, Florentino Pérez, ya sake lashe zaɓen shugabancin ƙungiyar ba tare da hamayya ba

Shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid, Florentino Pérez, ya sake lashe zaɓen shugabancin ƙungiyar ba tare da hamayya ba, wanda hakan ya ba shi damar ci gaba da jagorantar kulob ɗin a karo na shida. Pérez, mai shekaru 79, zai ci gaba da zama shugaban Real Madrid har zuwa shekarar 2030, bayan da babu wani ɗan takara da ya cika sharuddan tsayawa takara a zaɓen. Tun bayan komawarsa shugabancin ƙungiyar a shekarar 2009, Pérez ya taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarori masu yawa, ciki har da lashe kofunan gasar zakarun nahiyar turai da dama da kuma bunƙasa tattalin arzikin kungiyar. Magoya

FIFA 2026: Ƙasashen Turai da Amurka da Aka Fi Hasashen Zasu Lashe Kofin Duniya

Gasar ƙwallon ƙafa mafi girma a duniya za ta fara ranar 11 ga Yuni, inda ƙasashe 48 za su fafata domin lashe Kofin Duniya na FIFA 2026. Babbar tambayar da ke gaban masoya wasa ita ce ko ƙasashen Turai za su sake yin fice, ko kuma ƙasashen nahiyar Amurka za su ɗauke kambun. Ga taƙaitaccen bayanin wasu daga cikin manyan tawagogin da ake ganin suna da ƙarfi a bana: Sifaniya Tun bayan nasarar da ta samu a 2010, Sifaniya ba ta sake kaiwa matakin ƙarshe a manyan gasa ba, amma tana ci gaba da sake gina tawagarta. A wannan karon, tana da matasa masu hazaka kamar Lamine Yamal, Pedri da Rodri. Sifaniya

Dan wasan baya na Newcastle United, Kieran Trippier, na dab da komawa Wolverhampton Wanderers

Dan wasan baya na Newcastle United, Kieran Trippier, na dab da komawa Wolverhampton Wanderers bayan bangarorin biyu sun kai matakin karshe na tattaunawar cinikin. Rahotanni sun nuna cewa Wolverhampton na son kara karfin bangaren tsaronta da kwarewar Trippier, wanda ya taka muhimmiyar rawa a Newcastle tun bayan zuwansa daga Atletico Madrid a shekarar 2022. Ana sa ran za a kammala yarjejeniyar cikin kwanaki masu zuwa idan har aka cimma matsaya kan sharuddan karshe na kwantiragin dan wasan. Trippier, mai shekaru 35, ya taimaka wa Newcastle wajen samun gurbi a gasar zakarun Turai tare da kasancewa

Real Madrid ta sake naɗa Mourinho a matsayin koci kan yarjejeniyar shekaru uku

Jose Mourinho ya amince da kwantiragin shekara uku domin komawa matsayin kocin Real Madrid, sai dai ba za a gabatar da shi a hukumance ba har sai bayan zaɓen shugaban ƙungiyar da za a gudanar a ranar 7 ga watan Yuni. Rahotanni sun nuna cewa kwantiragin Mourinho zai fara aiki ne kawai idan shugaban ƙungiyar na yanzu, Florentino Perez, ya sake samun nasara a zaɓen. Perez ya sanar da gudanar da sabon zaɓen ne a wani taron manema labarai da aka yi a farkon watan nan, inda ya zargi wasu kafafen yaɗa labarai da kuma hukumar La Liga da gudanar da abin da ya kira “yaƙin tsari” a kansa. Perez mai sheka

Spain ta saka Yamal i a cikin tawagar gasar Kofin Duniya duk da rauni da yake fama dash

Tauraron matashin dan wasan Barcelona, Lamine Yamal, na cikin jerin ‘yan wasan da kocin Spain, Luis de la Fuente, ya bayyana domin gasar Kofin Duniya ta 2026 duk da cewa yana fama da rauni. Kocin ya kuma saka dan wasan Arsenal, Mikel Merino, bayan dawowarsa daga jinya sakamakon karayar ƙafa da ta hana shi taka leda tun watan Janairu. A karo na farko a tarihin Kofin Duniya, tawagar Spain ba ta kunshi ko dan wasa daya daga Real Madrid ba, bayan da aka cire Dean Huijsen da kuma Dani Carvajal wanda ya yi fama da raunuka a kakar wasa. De la Fuente ya kuma gayyaci Eric Garcia da Marc Pubill bayan ra

Pep Guardiola ne kocin mafi fice a wannan tsaran – In ji Wayne Rooney

Tsohon kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta kasar Ingila, Wayne Rooney, ya bayyana kocin Manchester City, Pep Guardiola, a matsayin "Sir Alex Ferguson na wannan zamanin," inda ya jinjina masa kan irin mamayar da ya yi a fagen kwallon kafa na Ingila. Da yake jawabi a shirin "Wayne Rooney Show" na kafar yada labarai ta BBC a ranar Talata, Rooney ya kwatanta nasarorin da Guardiola ya samu a City da irin wadanda tsohon kocinsa, Alex Ferguson, ya samu a Manchester United, wanda Rooney ya buga wa wasa a karkashinsa tsakanin shekarar 2004 zuwa 2013. "Na ga ana yawan kwatanta shi da Alex Ferguson," in

Ronaldo ya kafa sabon tarihin gasar cin kofin duniya yayin da Portugal ta sanar da 'yan wasanta

Kungiyar kwallon kafa ta kasar Portugal ta tabbatar da jerin sunayen 'yan wasanta da zasu fafata a gasar cin kofin duniya ta FIFA na shekarar 2026 mai zuwa, inda Cristiano Ronaldo ke shirin kafa tarihin fitowa karo na shida a gasar. Dan wasan gaba mai shekaru 41 yana ci gaba da nuna juriya da bajinta a matakin kasa da kasa, inda yake jagorantar tawagar da ke cike da kwararrun 'yan wasa masu fasaha da gogewa. Dama can ana fakar idon ganin sunansa a jeri, amma duk da haka wannan ya zama wani lokaci na tarihi a duniyar kwallon kafa, domin babu wani namiji da taba buga gasar cin kofin duniya har s

Neymar ya yi arangama da ɗan Robinho a karon farko da suka haɗu a filin atisayen Santos FC

Neymar ya samu saɓani da Robinho Junior yayin wani atisaye da Santos FC ta gudanar, kamar yadda rahotanni daga Brazil suka bayyana. Rahotannin sun ce Neymar mai shekaru 34 ya yi sa-in-sa da matashin ɗanwasan mai shekaru 18 bayan da ya zarge shi da yi masa yanka na raini a filin wasa. An ce lamarin ya kai har Neymar ya mari Robinho Junior, abin da ya jawo tunkuɗe-tunkuɗe tsakaninsu kafin daga bisani aka shiga tsakani. Daga baya Neymar ya huce tare da bai wa matashin ɗanwasan haƙuri, sai dai wasu rahotanni na cewa Robinho Junior bai gamsu ba, inda mashawartansa ke son ƙungiyar ta fitar da sanarw

Kungiyoyin Premier League sun yi asarar sama da dala biliyan ɗaya na kuɗin shiga

Duk da kasancewar Premier League na daga cikin gasannin ƙwallon ƙafa mafi samun kuɗaɗen shiga a duniya, wani sabon rahoto ya nuna cewa ƙungiyoyin gasar sun yi asarar kusan dala biliyan ɗaya a kakar 2024/25. Rahoton ya bayyana cewa duk da tara fam biliyan 6.8 na kuɗaɗen shiga, yawan kashe kuɗi kan sayen ’yan wasa, albashi da kuɗaɗen dillalai ya sa kuɗaɗen fita suka zarce abin da ake samu. Chelsea FC ta kafa tarihin asarar kuɗi mafi muni a tarihin gasar, bayan ta yi asarar fam miliyan 262 kafin haraji a shekarar kuɗin da ta ƙare ranar 30 ga Yunin 2025. Salon ƙungiyar na sayen matasan ’yan wasa d