AMMASCO RADIO NEWSROOM

Labarai

Gwamnatin Kano ta bada kyautar Riyal 200 ga kowane maniyyaci.

Gwamnatin Kano ta bada kyautar Riyal 200 ga kowane maniyyaci da ya fito daga jihar, da nufin tallafa musu ta yadda zasu ji dadin gudanar da aikin hajjin su na bana a kasar Saudiyya cikin nutsuwa. Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan, lokacin da yake jawabi a wajen horaswa ta musamman a aikace ga maniyyatan Kano yadda ake gudanar da ibadun aikin hajji gabanin tafiyar su kasa mai tsarki. Gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Murtala Sule Garo, ya bukaci maniyyatan da su mutunta dokokin kasar Saudiyya yayin gudanar da ibadar ta su, inda ya ce gwamnati ta dauki matakai masu kyau domin

Barista Nuhu Hamza Dantani ya gana da IGP kan zargin tauye haƙƙin jama’a

Fitaccen lauya mai kare haƙƙin bil’adama Nuhu Hamza Dantani ya bayyana cewa ya gana da Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya Olayunji Disu domin tattauna batutuwan da suka shafi zargin take haƙƙin jama’a da ake yi wa wasu jami’an ‘yan sanda. Dantani ya wallafa bayanin ganawar a shafinsa na Facebook ranar Juma’a, inda ya ce a yayin tattaunawar ya yi zargin cewa wasu jami’an ‘yan sanda na tsare mutane ba bisa ƙa’ida ba, tare da cin zarafi ta hanyar duka da kuma barazana. Haka kuma an tattauna batun yadda za a daƙile matsalar faɗan daba a Jihar Kano, tare da neman hanyoyin gudanar da bincike kan k

An kori lauya a Ma’aikatar Shari’a ta Kano saboda amfani da sa hannun manyan jami’ai ba tare da izini ba

Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano ta sallami wani lauya na gwamnati, Mustapha Nura Muhammad, bayan an same shi da laifin bayar da bayanan ƙarya tare da amfani da sunaye da sa hannun manyan lauyoyin ma’aikatar ba tare da izini ba. Wata sanarwa daga Mataimakin Kwamishinan Shari’a kan Yada Labarai, Dr. Abubakar Tijjani Ibrahim, ta bayyana cewa Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnatin Kano ta amince da hukuncin ne bayan nazarin rahoton kwamitin ladabtarwa a zamanta na 1 ga Afrilu, 2026. Bincike ya nuna cewa lauyan ya fitar da shawarwarin shari’a ta hanyar amfani da sa hannun manyan jami’ai, lamarin da

Ukraine da Russia sun amince da yin musayar wasu fursunonin yaƙi.

Ukraine da Russia sun amince su yi musayar fursunonin yaƙi guda dubu ɗaya daga kowanne ɓangare, a wani ɓangare na yarjejeniyar da ta kuma ƙunshi tsagaita buɗe wuta na kwanaki uku tsakanin ƙasashen biyu. Russia ce ta buƙaci tsagaita wutar na wucin gadi domin bikin tunawa da cika shekaru da kawo ƙarshen World War II. Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce ya umarci dakarun ƙasarsa da kada su kai hari a Red Square inda za a gudanar da bikin. Shi ma shugaban United States, Donald Trump ya ce an cimma yarjejeniyar ne bisa buƙatarsa, yayin tattaunawar da ake yi domin kawo ƙarshen rikicin.

Neymar ya yi arangama da ɗan Robinho a karon farko da suka haɗu a filin atisayen Santos FC

Neymar ya samu saɓani da Robinho Junior yayin wani atisaye da Santos FC ta gudanar, kamar yadda rahotanni daga Brazil suka bayyana. Rahotannin sun ce Neymar mai shekaru 34 ya yi sa-in-sa da matashin ɗanwasan mai shekaru 18 bayan da ya zarge shi da yi masa yanka na raini a filin wasa. An ce lamarin ya kai har Neymar ya mari Robinho Junior, abin da ya jawo tunkuɗe-tunkuɗe tsakaninsu kafin daga bisani aka shiga tsakani. Daga baya Neymar ya huce tare da bai wa matashin ɗanwasan haƙuri, sai dai wasu rahotanni na cewa Robinho Junior bai gamsu ba, inda mashawartansa ke son ƙungiyar ta fitar da sanarw

Kungiyoyin Premier League sun yi asarar sama da dala biliyan ɗaya na kuɗin shiga

Duk da kasancewar Premier League na daga cikin gasannin ƙwallon ƙafa mafi samun kuɗaɗen shiga a duniya, wani sabon rahoto ya nuna cewa ƙungiyoyin gasar sun yi asarar kusan dala biliyan ɗaya a kakar 2024/25. Rahoton ya bayyana cewa duk da tara fam biliyan 6.8 na kuɗaɗen shiga, yawan kashe kuɗi kan sayen ’yan wasa, albashi da kuɗaɗen dillalai ya sa kuɗaɗen fita suka zarce abin da ake samu. Chelsea FC ta kafa tarihin asarar kuɗi mafi muni a tarihin gasar, bayan ta yi asarar fam miliyan 262 kafin haraji a shekarar kuɗin da ta ƙare ranar 30 ga Yunin 2025. Salon ƙungiyar na sayen matasan ’yan wasa d

Hukumomi a Chad sun ayyana dokar ta ɓaci na tsawon kwanaki 20 a yankin Lake Chad sakamakon matsalolin tsaro da hare-haren da ake samu a yankin.

Chad ta ayyana dokar ta ɓaci a yankin Lake Chad kwanaki kaɗan bayan da mayakan Boko Haram suka kashe jami’an soji aƙalla 24 a wani sansanin soji da ke Barka Tolorom. Dokar ta ɓacin za ta fara aiki daga daren 7 zuwa daren 27 ga watan Mayun 2026. Hukumomi sun bayyana cewa za a rufe iyakokin yankin tare da sanya dokar hana zirga-zirga domin ƙarfafa matakan tsaro. A wata sanarwa da ya gabatar ta gidan talabijin na ƙasar, mai magana da yawun gwamnatin Chadi, Gassim Cherif, ya ce ɗaukar matakin zai taimaka wajen kamo waɗanda ake zargi da kai harin, tare da dakile zirga-zirgar mutane, motoci da mashi

Ba za mu tsaya muna kallon yadda ake cin zarafi da wulakanta ’yan ƙasarmu ba, in ji Bianca Odumegwu Ojukwu.

Ministar harkokin wajen Najeriya ta bayyana cewa ƙasar ba za ta amince da ci gaba da cin zarafi da wulakanta ’yan Najeriya a South Africa ba. Ta bayyana hakan ne yayin tattaunawa kan dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu da kuma ƙalubalen da wasu ’yan Najeriya ke fuskanta a ƙasar. Ojukwu ta jaddada cewa gwamnatin Najeriya za ta ci gaba da kare mutunci da haƙƙin ’yan ƙasarta a duk inda suke a duniya, tare da kira da a mutunta su kamar sauran al’ummomi. Kalaman nata na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun koke-koke kan hare-hare, cin zarafi da sauran matsalolin da wasu ’yan Najeri

Oyo State ta sanar da hana sayar da raguna a manyan tituna da gefen hanya yayin da ake shirin bikin babbar Sallah.

Oyo State ta gargadi mazauna jihar da masu sayar da dabbobi da su guji sayar da shanu da raguna a manyan tituna yayin bikin Eid al-Adha mai zuwa. Bayanin hakan ya fito ne yayin taron masu ruwa da tsaki kan aiwatar da dokar hana kiwo a fili ta shekarar 2019 da aka gudanar a Ibadan, kamar yadda Jaridar PUNCH ta rawaito. Gwamnatin ta bayyana cewa dokar ba ta nufin nuna wariya ga wata ƙabila, tana mai cewa an tanadi kasuwannin sayar da dabbobi a dukkan ƙananan hukumomin jihar domin gudanar da kasuwanci cikin tsari. Shugabar Hukumar Tabbatar da Bin Doka ta jihar, Aderonke Aderemi, ta ce duk wanda a

Donald Trump ya dakatar da wani shiri da aka gabatar domin taimaka wa jiragen ruwa su rika wucewa cikin kariya ta mashigar Strait of Hormuz,

Rahotanni sun nuna cewa an dakatar da shirin ne bayan tattaunawa da jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki kan yiwuwar tasirin sa ga harkokin siyasa da tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya. Mashigar Hormuz na da muhimmanci matuƙa ga kasuwancin man fetur na duniya, kuma duk wata matsala a yankin kan haifar da tashin farashin mai da fargaba a kasuwannin duniya. Matakin na Trump ya zo ne a lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan tsaro da zaman lafiya a yankin Gulf, musamman dangane da hulɗar Amurka da Iran

Attatijin ya sanar da shirin samar da wutar lantarki da ta kai megawat 20,000.

Aliko Dangote ya bayyana wani gagarumin shiri na samar da wutar lantarki mai ƙarfin megawat 20,000 domin taimakawa wajen magance matsalar ƙarancin lantarki a Nijeriya. Sanarwar na zuwa ne a lokacin da Nijeriya, ƙasar da ta fi yawan jama’a a Afirka, ke ci gaba da fama da matsanancin ƙarancin wuta wanda ke kawo cikas ga bunƙasar tattalin arziki da ci gaban masana’antu. Dangote ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da babban daraktan hukumar kula da ‘yan kasuwa a ƙasashe masu tasowa ta International Finance Corporation, Makhtar Diop. Ya ce rukunin kamfanoninsa zai shiga fannin samar da lantar

Afirka ta Kudu ta nuna damuwa kan shirin Najeriya na kwashe ƴan kasarta

Afirka ta kudu ta bayyana damuwarta kan shirin Najeriya na kwaso ƴan ƙasarta da ke son komawa gida. Ministan harkokin wajen ƙasar Ronald Lamola ya tattauna da takwararsa ta Najeriya domin lalubo hanyoyin da za a kawo ƙarshen zaman tankiyar da ke tsakanin ƙasashen biyu. '' Mun san cewa Najeriya ƙasa ce mai ƴancin ɗaukr irin wannan mataki na kwashe ƴan ƙasarta da ke son tafiya, amma muna ganin cewa yin hakan ba zai magance matsalar shigar baƙi ta hanyar da ba ta dace ba.'' a cewar Ronald Lamola. A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, ministar harkokin wajen Najeriya Bianca Odumegwu - Ojukwu

Iran ta bayyana cewa wajibi ne United States ta bai wa tawagar ƙwallon ƙafarta shiga gasar 2026 FIFA World Cup

Ma’aikatar Harkokin Waje ta Iran ta bayyana cewa Amurka, a matsayinta na ɗaya daga cikin ƙasashen da za su karɓi bakuncin Gasar Kofin Duniya ta FIFA, tana da alhakin bai wa tawagar ƙwallon ƙafar Iran bizar shiga ƙasar duk da saɓanin siyasa tsakanin ƙasashen biyu. Kakakin ma’aikatar, Esmaeil Baghaei, ya ce gwamnatin Iran na yin duk mai yiwuwa domin tabbatar da cewa babu wata matsala da za ta hana tawagar ƙasar halartar gasar da za a gudanar a Amurka. “’Yan wasanmu za su je Amurka ne kawai domin buga Gasar Kofin Duniya,” in ji Baghaei yayin wani taron manema labarai, kamar yadda kamfanin dillanc