AMMASCO RADIO NEWSROOM

Labarai

Harin hadin gwuiwar Amurka da Najeriya yayi sanadiyar kashe ýan ta'adda masu tarin yawa

Sanarwar haɗin gwuiwar tsakanin sojin Najeriya da kuma rundunar sojin Amurka dake Afirka ta ce, al-Minuki da aka kashe ne ke taimakawa wajen harkokin kafofin yaɗa labaran ƴan ta’addan da kuma kuɗaɗen da ake amfani da su wajen samar da makamai tare da jirage marasa matuƙa. Kwamandan rundunar Amurkar Janar Dagvin Anderson ya tabbatar da wannan nasarar lokacin da yake yiwa majalisar dokokin Amurka bayani dangane da aikin da suke yi na haɗin gwuiwa, inda ya kuma bayyana irin taimakon da suke samu daga sojojin Najeriya wajen gabatar musu da bayanan asiri da kuma taimaka musu wajen aikin. Shugaban N

Arsenal Ta Lashe Gasar Premier League Bayan Manchester City Ta Yi Canjaras Da Bournemouth

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta tabbata zakaran gasar Premier League ta kasar Ingila na bana, bayan da babban kalubalanta, Manchester City, ta tashi kunnen doki 1-1 a karawarta da kungiyar Bournemouth a daren Talata. Sakamakon wasan ya kawo karshen jiran shekaru 22 da magoya bayan Arsenal suka yi na sake ganin kungiyarsu ta dauki babban kofin kasar Ingila, tun bayan rabon da su lashe shi tun a kakar wasa ta 2003/2004 karkashin tsohon koci Arsene Wenger. Manchester City, wacce ke da bukatar samun nasara lallai da lallai a wannan wasan domin ci gaba da fafatawa da Arsenal, ta sha mamaki baya

Pantami ya janye daga neman takarar gwamnan Gombe a jam'iyyar APC

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Tsohon ministan sadarwar Najeriya, Isa Ali Pantami ya fitar a shafinsa na Facebook yau Talata, gabanin gudanar da zaɓen fidda gwani a gwamnoni a ranar alhamis mai zuwa. Pantami ya ce ya janye ne saboda rashin bin ƙa'idar da ta dace wajen tuntuɓar ƴaƴan jam'iyyar a kan shawarwarin da ta yanke, da kuma rashin samun tabbacin gudanar da sahihin zaɓe.

Pep Guardiola ne kocin mafi fice a wannan tsaran – In ji Wayne Rooney

Tsohon kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta kasar Ingila, Wayne Rooney, ya bayyana kocin Manchester City, Pep Guardiola, a matsayin "Sir Alex Ferguson na wannan zamanin," inda ya jinjina masa kan irin mamayar da ya yi a fagen kwallon kafa na Ingila. Da yake jawabi a shirin "Wayne Rooney Show" na kafar yada labarai ta BBC a ranar Talata, Rooney ya kwatanta nasarorin da Guardiola ya samu a City da irin wadanda tsohon kocinsa, Alex Ferguson, ya samu a Manchester United, wanda Rooney ya buga wa wasa a karkashinsa tsakanin shekarar 2004 zuwa 2013. "Na ga ana yawan kwatanta shi da Alex Ferguson," in

Mutane huɗu sun mutu a zanga-zangar tsadar man fetur a Kenya

Aƙalla mutane huɗu ne suka rasa rayukansu sakamakon zanga-zangar adawa da tsadar man fetur da hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar Kenya. Rahotanni sun bayyana cewa dubban mutane ne suka fito kan tituna a manyan biranen ƙasar domin nuna rashin jin daɗinsu kan matsin rayuwa da kuma ƙarin kuɗin man fetur. An kuma samu rikici tsakanin masu zanga-zangar da jami’an tsaro, inda aka yi amfani da barkonon tsohuwa da harsasai wajen tarwatsa masu zanga-zangar a wasu yankuna. Masu zanga-zangar na zargin gwamnatin shugaban ƙasar, William Ruto da gaza magance matsalolin tattalin arziƙi da hauhawar farashin

Jam'iyar ADC zata fadi zaben 2027 idan har Atiku ya samu tikitin takarar Shugaban kasa

Tsohon gwamnan jihar Rivers Rotimi Amaechi ya bayyana haka ne a daidai lokacin da jam'iyyar ke shirin fidda ɗan takarar da zai tsayawa ADC a matsayin mai neman kujerar shugabancin Najeriya a zaɓe mai zuwa. Bisa tsarin karɓa karɓa da ake, shugabancin Najeriyar zai tsaya ne a kudu har zuwa shekarar 2031. Amaechi na daga cikin masu sha'awar takarar shugabancin jam'iyyar la'akari da cewar ya sayi fom tare da Atiku Abubakar da Mohammed Hayatuddeen.

Hukumar EFCC ta cafke tsohon ministan Buhari, Sale Mamman

Hukumar EFCC ta cafke tsohon ministan Buhari, Sale Mamman da aka yanke wa hukuncin shekaru 75 a gidan yari bisa samun sa da laifin cin hanci Rohotanni sun nuna cewa an kama tsohon ministan na wutar lantarki ne a yankin Rigasa da ke jihar Kaduna, ana kuma zargin an cafke shi ne yayin da yake kokarin arcewa

Tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Janar Abdulrahman Dambazau mai ritaya, ya bayyana cewa kafa ‘yan sandan jihohi

Tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Janar Abdulrahman Dambazau mai ritaya, ya bayyana cewa kafa ‘yan sandan jihohi zai yi tasiri ne kawai idan an gina tsarin su bisa ƙwarewa da bin ƙa’ida. Dambazau ya bayyana haka yayin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN), inda ya ce bai kamata gwamnoni su mallaki ikon sarrafa ‘yan sandan jihohi ba, yana mai cewa hakan na iya sanyawa a yi amfani da su wajen danniya ko yaƙar abokan hamayyar siyasa. Ya kuma jaddada muhimmancin tantance jami’ai yadda ya kamata, horas da su tare da samar musu da kayan aiki da walwala domin tabbatar da

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya caccaki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya caccaki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan yadda matsalar tsaro ke ƙara muni a ƙasar nan, yana mai cewa yawaitar kashe-kashe da garkuwa da mutane alama ce ta gazawar shugabanci. A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya nuna damuwa matuƙa kan sace ɗalibai da malamai a Ogbomoso da kuma kashe wasu mutane a Jihar Katsina, ciki har da wata mata mai juna biyu. Ya ce abin takaici ne yadda gwamnati ke ci gaba da mayar da martani da fitar da sanarwar ta’aziyya bayan aukuwar hare-hare, maimako

Hukumar EFCC ta kama tsohon Ministan Lantarki Mamman wanda aka riga aka yanke wa hukunci

Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) ta kama tsohon Ministan Lantarki, Saleh Mamman, wanda kwanan nan Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa hukuncin daurin gidan yari saboda samun sa da laifin almubazzaranci da dukiyar kasa. Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, yayin da yake jawabi a taron manema labarai a babban sakatariyar hukumar da ke Abuja ranar Talata, ya tabbatar da cewa an kama Mamman ne da sanyin safiyar ranar Talata. A makon da ya gabata ne Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa Mamman hukuncin daurin shekaru 75 a gidan yari yana nan ba ya nan (i

Ronaldo ya kafa sabon tarihin gasar cin kofin duniya yayin da Portugal ta sanar da 'yan wasanta

Kungiyar kwallon kafa ta kasar Portugal ta tabbatar da jerin sunayen 'yan wasanta da zasu fafata a gasar cin kofin duniya ta FIFA na shekarar 2026 mai zuwa, inda Cristiano Ronaldo ke shirin kafa tarihin fitowa karo na shida a gasar. Dan wasan gaba mai shekaru 41 yana ci gaba da nuna juriya da bajinta a matakin kasa da kasa, inda yake jagorantar tawagar da ke cike da kwararrun 'yan wasa masu fasaha da gogewa. Dama can ana fakar idon ganin sunansa a jeri, amma duk da haka wannan ya zama wani lokaci na tarihi a duniyar kwallon kafa, domin babu wani namiji da taba buga gasar cin kofin duniya har s

Jami'an 'yan sanda sun kama wani mutum da kulli 339 na abin da ake zargi wiwi ne a Kogi

Rundunar 'yan sandan jihar Kogi ta bayyana cewa ta kama wani mutum mai shekaru 52 da kulli 339 na haramtattun kwayoyi da ake zargi wiwi ce (ganyen taba wiwi) a garin Kabba, da ke karkashin Karamar Hukumar Kabba/Bunu a jihar. Kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Naziru Kankarofi, ya shaida wa manema labarai a wani taron manema labarai da aka gudanar a babban sakatariyar rundunar da ke Lokoja ranar Talata cewa, an yi kamun ne a ranar 9 ga watan Mayu, 2026, da misalin karfe biyu na rana (1400hrs) ta hanyar yin amfani da bayanan sirri, dabarun tsayar da motoci don bincike, da kuma matakan riga-kafin

Gwamnatin ƙasar Togo ta sanar da cire buƙatar biza ga dukkan ‘yan ƙasashen Afirka da ke shiga ƙasar domin zama na wani ɗan lokaci.

Gwamnatin ƙasar Togo ta sanar da cire buƙatar biza ga dukkan ‘yan ƙasashen Afirka da ke shiga ƙasar domin zama na wani ɗan lokaci. Cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Tsaro ta Togo ta fitar a shafinta na X yau Talata, gwamnati tace duk wani ɗan Afirka mai riƙe da ingantaccen fasfo na ƙasarsa zai iya shiga Togo ba tare da neman biza ba domin zama har na tsawon kwanaki 30. Gwamnatin Togo ta ce wannan mataki wani ɓangare ne na ƙoƙarin ƙara ƙarfafa haɗin kan ƙasashen Afirka tare da sauƙaƙa zirga-zirga tsakanin al’ummar nahiyar. Sanarwar ta bayyana cewa shugaban majalisar ƙasar ya sake jaddada aniyars

Hukumar Tara Haraji ta Najeriya (NRS) ta yi gargadin cewa ci gaba da samun gibin haraji

Hukumar Tara Haraji ta Najeriya (NRS) ta yi gargadin cewa ci gaba da samun gibin haraji, jinkirin tura kudaden haraji da kuma rashin bin ka’idoji daga wasu hukumomin gwamnati da jihohi na iya kawo cikas ga kudirin tara kusan naira tiriliyan 40 a shekarar 2026. Hukumar ta bayyana hakan ne yayin wani taron kasa kan karfafa bin sabbin dokokin haraji da aka gudanar a Abuja, inda jami’an gwamnatin tarayya, jihohi, ma’aikatu da hukumomin tara kudaden shiga suka tattauna hanyoyin bunkasa tattara haraji. Da take jawabi a wajen taron, Daraktar kula da manyan masu biyan haraji da bangaren gwamnati na hu

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da samar da rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana.

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da samar da rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana guda 166 domin rage matsalar karancin ruwa da fadada samar da tsaftataccen ruwa ga al’ummar jihar. Mukaddashin Kwamishinan Albarkatun Ruwa na jihar, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce shirin wani bangare ne na matakan gaggawa da gwamnatin jihar ke dauka domin magance matsalar ruwa a yankuna daban-daban. A cewarsa, ana sa ran rijiyoyin za su samar da kimanin lita miliyan 4.15 na ruwa a kullum tare da anfani ga mutane kusan 830,000 a yank

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya umarci jami'an tsaro da su murkushe ƴan daba dake addabar cikin birnin Kano

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya umarci jami'an tsaro da su murkushe ƴan daba dake addabar cikin birnin Kano tare da magance ƴan fashin daji dake shigowa jihar ta kan iyakokin Katsina. Kwamishinan ƴansandan Kano, CP Ibrahim Bakori ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai bayan taron gaggawa na majalisar tsaron jihar Kano. Kwamishinan ƴansandan ya ce al'ummar Kano za su fara ganin sauyi nan da kwanaki uku game da matsalar tsaron dake addabar jihar.

Ƴan Mali 30 sun kuɓuta daga hannun masu safarar mutane a Nasarawa

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta ce ta tarwatsa wata ƙungiyar masu safarar mutane da ake zargin tana gudanar da ayyukanta a Abuja da wasu yankuna maƙwabta. Jami’an tsaron sun kuma kuɓutar da mutum 30 ‘yan asalin Mali da ake zargin an tsare su a Nasarawa. A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Anthony Placid ya fitar, ya ce jami’ai sun gano ayyukan ƙungiyar ne a wasu gidaje da ke yankunan Mararraba da Karu, inda ake zargin an killace mutanen. ‘Yan sanda sun ce sun kama mutum 13 da ake zargi suna da hannu a safarar mutanen. A cewar rundunar, binciken ya fara ne bayan samun bayanan sirri kan ɓ

Zaɓen fidda gwani na sanatocin APC ya tayar da ƙura

Ana ci gaba da ce-ce-ku-ce da korafe-korafe kan sakamakon zaɓukan fidda gwani na All Progressives Congress da aka gudanar a faɗin Najeriya. Jam’iyyar mai mulki ta gudanar da zaɓen fidda gwani na kujerun sanatoci a jihohi daban-daban, inda a wasu wuraren aka zaɓi tsarin maslaha maimakon kaɗa ƙuri’a. Sai dai matakin ya haifar da rashin gamsuwa da zarge-zargen rashin adalci daga wasu ‘yan takara da magoya bayansu. Sanatoci da dama masu ci sun rasa tikitin komawa majalisar dattawa a ƙarƙashin jam’iyyar APC, yayin da wasu jihohi kamar Kano da Jigawa da Yobe da Katsina suka rungumi tsarin maslaha wa

Shin dakatar da jarumai zai gyara Kannywood?

Kannywood ta shafe shekaru tana fama da ƙalubale daga ciki da wajen masana’antar, matsalolin da a wasu lokuta kan janyo tsaiko ga harkokinta. Daga cikin manyan matsalolin da suka fi ɗaukar hankali akwai rikice-rikicen cikin gida, musamman tsakanin Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano da wasu jarumai da masu shirya fina-finai. An kafa hukumar ne a zamanin tsohon gwamnan Ibrahim Shekarau domin sanya ido kan yadda ake gudanar da harkokin fina-finai da bidiyo a jihar Kano. Tun daga lokacin, dokokin addini da al’ada sun kasance cikin abubuwan da ake ganin suna takaita ci gaban masana’antar. Yayin

Ebola ta kashe mutum 131 a Congo

Ɓarkewar cutar Ebola mai saurin yaɗuwa ta kashe aƙalla mutane 131 a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, kamar yadda jami’an ƙasar ta tsakiyar Afirka suka bayyana bayan sabunta adadin daga mutum 118 da aka sanar a baya. Likitoci na ci gaba da bibiyar sama da mutum 500 da ake zargin sun kamu da cutar. Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) za ta gudanar da zaman kwamitin gaggawa a ranar Talata domin tattauna yadda cutar ke ƙara yaɗuwa. “An shirya zaman kwamitin gaggawa nan gaba a yau,” in ji wani mai magana da yawun WHO ga AFP, kwanaki biyu bayan shugaban hukumar lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya ya ayyana