AMMASCO RADIO NEWSROOM

Labarai

Pantami ya janye daga zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC na gwamna a jihar Gombe, sakamakon zargin take dokokin zaɓe.

Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani na Nijeriya, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya janye takararsa daga zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC domin neman kujerar gwamnan Jihar Gombe. Ya bayyana hakan a wata sanarwa da lauyansa, Barista Ibrahim M. Attahir, ya fitar ranar Talata. Pantami ya ce ya ɗauki matakin ne bayan tuntubar masu ruwa da tsaki da kuma nazarin abubuwan da suka faru game da zaɓen. Ya danganta janyewar da zargin take Dokar Zaɓe ta 2026 da rashin gaskiya a tsarin zaɓen cikin gida na jam’iyyar. Ya kara da cewa duk da ya bi dukkan ka’idojin APC kuma ya amsa kiran mata

Tsohon minista Sa'idu Ahmed Alkali ya janye daga takarar fidda gwani a jihar Gombe

Tsohon ministan sufuri kuma ɗan takarar gwamnan jihar Gombe a jam’iyyar APC, Sa'idu Ahmed Alkali, ya sanar da janye kansa daga shiga zaɓen fidda gwani na gwamna da jam’iyyar za ta gudanar ranar 21 ga watan Mayun 2026. A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Umar Alkali Jibrin ya fitar, Sanata Alƙali ya ce ya ɗauki matakin ne saboda abin da ya kira rashin gaskiya da karya dokokin zaɓe a jihar. Sanarwar ta bayyana cewa Alƙali ya cika dukkan sharuɗɗan shiga takarar gwamna, ciki har da sayen fom ɗin nuna sha’awa da na tsayawa takara tare da wuce tantancewar da jam’iyyar

FAAN ta ɗauki tsauraran matakan kariya a dukkan filayen jiragen saman ƙasa da ƙasa domin dakile yaduwar cutar Ebola bayan bullarta a wasu sassan Afirka ta Tsakiya

Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Najeriya, FAAN ta ɗauki tsauraran matakan kariya a dukkan filayen jiragen saman ƙasa da ƙasa domin dakile yaduwar cutar Ebola bayan bullarta a wasu sassan Afirka ta Tsakiya. A wata sanarwa da Daraktan Hulɗa da Jama’a da Kare Haƙƙin Fasinjoji na hukumar, Henry Agbebire, ya fitar, FAAN ta ce tana aiki tare da cibiyar dakile yaduwar cututtuka, Hukumar Kula da Lafiyar Tashoshin Jiragen Ruwa da Sama, da sauran hukumomi domin ƙarfafa sa ido kan fasinjojin da ke shigowa Najeriya, musamman daga yankunan da ake fuskantar haɗarin cutar. Hukumar ta bayyana cewa ana

Dele Momodu na jam’iyyar ADC ya bayyana cewa, dole su haɗa kai maimakon rarrabuwa a kan kayar da Tinubu a zaɓen 2027

Jigo a jam'iyyar ADC Dele Momodu ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels. Inda ya ce, muddin ‘yan adawa na son kayar da Tinubu a 2027, dole su haɗa kai maimakon rarrabuwa a doron yanki-yanki. Dele Momodu ya shawarci ‘yan takarar Kudu irin su Goodluck Jonathan, Peter Obi da Seyi Makinde da su zauna su cimma matsaya kan ɗan takara guda domin gujewa raba ƙuri’un Kudu. Momodu ya jaddada cewa tsarin maslaha (consensus) shi ne mafi dacewa idan har ‘yan adawa suna son kafa hamayya mai ƙarfin da za ta kayar da Tinubu a zaɓen 2027

Tsohon ministan tsaro, Theophilus Danjuma, ya bayar da gudunmawar Naira biliyan 3 yayin ƙaddamar da littafin tarihin tsohon shugaban ƙasa

Tsohon ministan tsaro, Theophilus Danjuma, ya bayar da gudunmawar Naira biliyan 3 yayin ƙaddamar da littafin tarihin tsohon shugaban ƙasa, Yakubu Gowon mai suna “My Life of Duty and Allegiance” da aka gudanar a Abuja ranar Talata. Haka kuma shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya sayi kwafi 25 na littafin kan Naira miliyan 500 ta hannun wakilinsa, Mansur Ahmed. Shugaban BUA Group, Abdul Samad Rabiu, shi ma ya sayi kwafi na littafin da kudinsu ya kai naira miliyan 25. Rahotanni sun bayyana cewa Danjuma ya kuma umarci a saya tare da rabawa dakunan karatu na jami’o’i 20 da suka bai

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya jinjinawa shugaban Amurka Donald Trump dangane da goyan bayan da ya ke bai wa ƙasar,

Sanarwar haɗin gwuiwar tsakanin sojin Najeriya da kuma rundunar sojin Amurka dake Afirka ta ce, al-Minuki da aka kashe ne ke taimakawa wajen harkokin kafofin yaɗa labaran ƴan ta’addan da kuma kuɗaɗen da ake amfani da su wajen samar da makamai tare da jirage marasa matuƙa. Kwamandan rundunar Amurkar Janar Dagvin Anderson ya tabbatar da wannan nasarar lokacin da yake yiwa majalisar dokokin Amurka bayani dangane da aikin da suke yi na haɗin gwuiwa, inda ya kuma bayyana irin taimakon da suke samu daga sojojin Najeriya wajen gabatar musu da bayanan asiri da kuma taimaka musu wajen aikin. Shugaban N

China Da Rasha Sun Haɗa Baki Wajen Sukan Manufofin Amurka A Duniya

Bayan wata gagarumar tattaunawa da ta gudana tsakanin Shugaba Xi Jinping da takwaransa Vladimir Putin, kasashen China da Rasha sun fito fili sun kalubalanci dabarun siyasa da na soja da Amurka ke amfani da su, musamman a kasashe irin su Iran da Venezuela. Abubuwan Da Kasashen Biyu Suka Soki Katsalandan Cikin Gida: Shugabannin biyu sun nuna adawa da yunkurin kifar da gwamnatoci ko rura wutar fitina a cikin kasashen da ke cin gashin kansu. Keta Dokokin Duniya: Sun bayyana cewa matakan barazanar soja ko farmakin ba-zata da Amurka ke yi, suna gurbata tsarin da Majalisar Dinkin Duniya ta shimfida t

Masu Sayen Motocin Lantarki Sun Ƙaru Da Kashi 28% Sanadiyyar Rikicin Iran

Hukumar kula da makamashi ta duniya ta ce yaƙin Iran ya janyo ƙaruwar sayen motoci masu amfani da lantarki a duniya da kusan kashi 28 cikin 100. Hukumar ta danganta wannan ƙaruwa da hauhawar farashin mai da ya biyo bayan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila. Rahoton ya ce tsadar mai ya sa mutane da dama sun koma amfani da motocin lantarki domin rage kashe kuɗin sufuri. A cewar hukumar, kusan ƙasashe 30 sun samu ƙarin masu sayen motocin da ke amfani da lantarki a watan Maris, ciki har da ƙasashen Latin Amurka inda aka samu ƙaruwa da kashi 75 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

An Buɗe Sabon Sashen Bin Doka Domin Bunƙasa Tattara Haraji

Hukumar Tara Haraji ta Jihar Kano, ta ƙaddamar da sabon ginin ofisoshin sashen bin doka da tabbatar da biyan haraji domin inganta aikin ma’aikata da Ƙarfafa tsarin tattara haraji a fadin jihar. Sshugaban hukumar, Dakta Zaid Abubakar, ne ya bayyana hakan yayin bikin Ƙaddamar da ginin da aka gudanar jiya Talata. Ya ce samar da sabbin ofisoshin na daga cikin ƙoƙarin hukumar na samar da ingantaccen wajen aiki ga ma’aikata domin ƙara musu ƙwarin gwiwa wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. Shugaban hukumar ya ƙara da cewa sabon ginin zai taimaka wajen inganta tsarin bin diddigi da tabbatar da

Ma'aikatar Ilimi Ta Kano Ta Fitarda Tsarin Hutun Babbar Sallah Ga Makarantu

Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano ta sanar da hutun Babbar Sallah ga dukkan makarantun firamare da sakandire na gwamnati da masu zaman kansu a fadin jihar. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kai na ma’aikatar, Musbahu Aminu Yakasai, ya sanya hannu yau Laraba. Sanarwar ta bayyana cewa daliban makarantun kwana za su fara hutu daga ranar Asabar 23 ga watan Mayun da muke ciki , sannan su koma makaranta ranar Lahadi 31 ga watan Mayun. Daliban jeka ka dawo kuwa, za su fara hutun ne daga ranar Juma’a 22 ga watan Mayun, tare da komawa makaranta ranar Litinin 1 ga watan Yuni mai zu

An Dakatar da Wani Waje Da Ake Zargin Ana Sarrafa Gurbataccen Man Gyada a Bompai.

Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, tare da haɗin gwiwar jami’an lafiya da tsaftar muhalli, sun fara bincike kan wasu mutane da ake zargi da sarrafa gurbataccen man gyada a titin Mai Malari Bompai kusa da Ramin Ranji a Birnin Kano. Shugaban hukumar, Comrade Sa’idu Yahaya, ya ce jami’an hukumar sun kai samame wurin tare da dakatar da ci gaba da sarrafa man har sai an kammala bincike domin kare lafiyar al’ummar Jihar Kano. Shugaban hukumar ya ce bayan samun sahihan bayanan sirri, jami’an sun kai sumame wurin tare da kama kayayyakin da ake amfani da su, yay

Dakarun Soji Sun Tarwatsa Shirin Mayakan Ta'addanci a Arewa Maso Gabas

Yayin da suke tsaka da gudanar da ayyukan tabbatar da tsaro, dakarun hadin gwiwa na "Operation Hadin Kai" sun yi nasarar fatattakar wasu 'yan bindiga da suka yi yunkurin kaddamar da gagarumin hari a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan. Baya ga dakile harin, sojojin sun kuma kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su, tare da damke wasu mutane da ake zargi da bai wa 'yan ta'addan bayanai da kayan aiki. Yadda Aka Fafata a Sansanin Gajibo Shirin Makirci: Rahotanni sun nuna cewa dakarun da ke sansanin FOB Gajibo ne suka fuskanci barazanar, inda ake zargin mayakan Boko Haram da ISWAP ne suka taho

Dan Sanda Ya Rasa Ransa Gab da Ritaya a Kano Sakamakon Fadan Daba.

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta fuskanci babban rashi na wani gogaggen jami'inta mai suna Sani S.O, wanda ya rasa ransa sakamakon rikicin daban da ya ɓarke a yankin Hotoro. Abin bakin ciki shi ne, jami'in ya rayu ne da sauran 'yan makonni kalilan ya ije aikin sarki domin ya tafi ritaya. Yadda Lamarin Ya Faru Kiran Gaggawa: An tura marigayin ne tare da tawagarsa domin su kwantar da tarzoma tare da raba wani fada da ya barke tsakanin gungun matasan banza. Harbin Bindiga: Yayin kokarin dawo da doka da oda, wani daga cikin 'yan daban ya harbe shi da makami. Rasa Rai: Ko da aka garzaya da shi ba

Gwamnatin jihar Kwara ta buƙaci masu ruwa da tsaki a ɓangaren lafiya da su haɗa kai wajen samar da ingantaccen kiwon lafiya a faɗin jihar.

Gwamnatin jihar Kwara ta buƙaci masu ruwa da tsaki a ɓangaren lafiya da su haɗa kai wajen samar da ingantaccen tsarin aiwatar da kiwon lafiya na zamani domin inganta ayyukan lafiya a faɗin jihar. Kiran ya fito ne yayin buɗe wani taron kwana uku da aka gudanar a birnin Ilorin kan samar da tsarin aiwatar da shirin lafiya na zamani da ya dace da bukatun jihar Kwara. Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiya ta jihar, Dakta Taoheed Abdullahi, wanda ya wakilci Kwamishiniyar Lafiya, Amina El-Imam, ya ce taron na da nufin mayar da manufofin lafiya na ƙasa zuwa ayyuka na zahiri da za su dace da halin da ake

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya lashe takarar Sanatan Gombe ta Arewa a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC

Jam’iyyar APC ta bayyana gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, a matsayin dan takarar Sanatan Gombe ta Arewa bayan samun kuri’u masu rinjaye a zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka gudanar a jihar. ‎Shugaban kwamitin zaben fidda gwani na APC a jihar, Mallam Labiru Musa Kafur, ya ce an gudanar da zaben cikin lumana da gaskiya a dukkan kananan hukumomi 11 na jihar. ‎Haka kuma, tsohon mataimakin kwamishinan ’yan sanda, Mohammed Ahmed, ya zama dan takarar APC na Sanatan Gombe ta Tsakiya. ‎Kwamitin ya tabbatar da cewa duk wadanda suka yi nasara sun cika sharuddan kundin tsarin mulki da na ja

Rundunar ’Yan Sandan ƙasar nan ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da haɗa baki wajen sace wani dattijo a Jihar Kaduna domin neman kuɗin fansa, tare da ƙwato bindiga ƙirar AK-47.

Rundunar ’Yan Sandan ƙasar nan ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da haɗa baki wajen sace wani dattijo a Jihar Kaduna domin neman kuɗin fansa, tare da ƙwato bindiga ƙirar AK-47. Wannan na cikin sanarwar da Jami’in Yaɗa Labaran Rundunar, DCP Anthony Okon, ya fitar jiya Talata. Sanarwar ta ce bincike ya nuna cewa Yusuf Rabo, ya haɗa kai da Musa Adamu da Ali Haruna, wanda shi ne jikan dattijon, domin sace mahaifinsa bisa zargin cewa yana da dukiya da dabbobi masu yawa. Binciken ya kuma gano cewa an sace dattijon har sau biyu, inda aka karɓi kuɗin fansa naira miliyan biyu a karon farko da kuma

Hukumar Kwashe Shara ta Jihar Kano, REMASAB, ta hukunta wani mai aikin gini, Alhaji Garzali Sani, kan zuba yashi a kan hanya, da lalata magudanan ruwa

Hukumar Kwashe Shara ta Jihar Kano, REMASAB, ta hukunta wani mai aikin gini, Alhaji Garzali Sani, kan zuba yashi a kan hanya, lamarin da ya toshe kwalbati tare da lalata magudanan ruwa. Wannan na cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Malam Abubakar Ahmad, ya fitar yau Laraba. Sanarwar ta ce kotun tafi-da-gidanka ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Halima A.B. Wali ta ɗauki matakin ne a ci gaba da aikin sa ido da hukumar ke yi domin tabbatar da bin dokokin tsaftar muhalli a faɗin jihar. Haka kuma kotun ta gurfanar da gidan man TotalEnergies da ke titin Ahmadu Bello Way, tare da huk

Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, PCACC, ta bayyana cewa ta gayyaci tsohon Shugaban Ma’aikatan Jihar Abdullahi Musa kan zargin cire kuɗi daga albashin ma’aikata.

Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, PCACC, ta bayyana cewa ta gayyaci tsohon Shugaban Ma’aikatan Jihar Abdullahi Musa kan zargin cire kuɗi daga albashin ma’aikata. Shugaban Hukumar, Sa’idu Yahaya ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa ta musamman da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, a Kano ranar Talata.

Rigimar takarar Shugaban kasa daga jam'iyun adawa sharar fage ne ga nasarar shugaban kasa Tinubu - cewar jigo a jamíyar ADC,Dele Momodu

Jigo a jam'iyyar ADC Dele Momodu ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels. Inda ya ce, muddin ‘yan adawa na son kayar da Tinubu a 2027, dole su haɗa kai maimakon rarrabuwa a doron yanki-yanki. Dele Momodu ya shawarci ‘yan takarar Kudu irin su Goodluck Jonathan, Peter Obi da Seyi Makinde da su zauna su cimma matsaya kan ɗan takara guda domin gujewa raba ƙuri’un Kudu. Momodu ya jaddada cewa tsarin maslaha (consensus) shi ne mafi dacewa idan har ‘yan adawa suna son kafa hamayya mai ƙarfin da za ta kayar da Tinubu a zaɓen 2027.

Rundunar ’yan sandan jihar Yobe ta kama wasu mutane da ake zargi da aikata laifuka daban-daban

Rundunar ’yan sandan jihar Yobe ta kama wasu mutane da ake zargi da aikata laifuka daban-daban tare da kwato babur da saniyar sata a wasu samame da ta gudanar a Garin Alkali da ke karamar hukumar Bursari. ‎A wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Dungus Abdulkarim, ya fitar, ya ce jami’an rundunar sun kama wani mutum mai suna Abubakar Haruna mai shekaru 30 daga Lafiya Lamurde a jihar Adamawa, wanda ake zargi da kwarewa wajen satar babura a kasuwanni da wuraren taruwar jama’a. ‎ ‎ ‎Bayan faruwar lamarin, wasu mutane sun bi sawunsa domin kama shi, inda a yayin gudun tsira ya buge wani dattijo mai