AMMASCO RADIO NEWSROOM

Labarai

Mataimakin gwamnan jihar Lagos, Obafemi Hamzat, ya lashe zaɓen fidda gwani na APC

Mataimakin gwamnan jihar Lagos, Obafemi Hamzat, ya lashe zaɓen fidda gwani na APC domin takarar gwamna a 2027 bayan samun ƙuri’u 657,917 cikin 657,974 da aka kaɗa. Abokin takararsa Lanre Jim-Kamal ya samu ƙuri’a ɗaya kacal. Shugaban kwamitin zaɓen, Janar Jon Temlong mai ritaya, ya ce an gudanar da zaɓen cikin lumana a sakatariyar APC da ke Ikeja. Hamzat ya gode wa Shugaba Tinubu, Gwamna Sanwo-Olu da shugabannin APC bisa goyon baya, sannan ya gabatar da tsarinsa na “My Lagos Dream” wanda ya mayar da hankali kan ayyukan yi, ababen more rayuwa, ilimi, lafiya da tsaro.

Gwamnatin jihar Zamfara ta amince da fara biyan albashin watan Mayu ga dukkan ma'aikatan gwamnati kafin bikin Eid al-Kabir

Gwamnatin jihar Zamfara ta amince da fara biyan albashin watan Mayu ga dukkan ma'aikatan gwamnati kafin bikin Eid al-Kabir domin ba su damar yin shirye-shiryen Sallah cikin sauki. A cikin wata sanarwa da Ma'aikatar Yada Labarai da Al'adu ta jihar ta fitar, Kwamishinan Yada Labarai da Al'adu, Alhaji Mahmud Muhammad Dantawasa, ya ce matakin ya nuna kudirin gwamnatin Gwamna Dauda Lawal na kula da walwalar ma'aikata da iyalansu. Gwamnatin ta bayyana cewa biyan albashin da wuri zai taimaka wajen rage wa ma'aikata matsin tattalin arziki da ke tattare da lokutan bukukuwa, musamman a wannan lokaci da

Shugabannin jam’iyyar ADC na kasa sun koka kan yadda jami’an hukumar ICPC suka hana su ganin Nasir El Rufai

Shugabannin jam’iyyar ADC na kasa sun koka kan yadda jami’an hukumar ICPC suka hana su ganin Nasir El Rufai, yayin wa ziyar da suka kai inda ake tsare da shi. Tawagar ADC wadda ta kunshi sakataren jam’iyyar Rauf Aregbesola da Sakataren yada labaran jam’iyyar Bolaji Abdullahi da kuma Salihu Lukman, sun ziyarci El Rufai domin tattaunawa kan wasu batutuwa, amma basu samu damar ganin El Rufai ba. A martanin da ta fitar, hukumar ICPC ta ce kotu bata bawa ‘yan siyasa da abokan El Rufai damar ganinsa a inda yake tsare ba.

Shugaban kasar Kenya William Ruto ya ce gwamnatinsa za ta rage farashin man dizel a ƙasar

Shugaban kasar Kenya William Ruto ya ce gwamnatinsa za ta rage farashin man dizel a ƙasar domin tallafa wa masu amfani da shi, biyo bayan zanga-zangar da aka yi kan tsadar makamashi sakamakon rikicin Gabas Ta Tsakiya. A cikin makon nan, masu motocin sufurin haya a Kenya sun gudanar da yajin aikin kwanaki biyu, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu tare da jikkata wasu kusan 30. Wannan mataki ya faru ne saboda fushin jama’a kan tsadar man fetur da ta janyo tsadar rayuwa. A cikin jawabin nasa a talabijin, Ruto ya ce ya bayar da umarnin rage farashin dizel a tsarin farashi na watannin Yuni z

Masarautar Zazzau ta dakatar da shugaban ƙauyen Matarawa bisa zargin damfara da cin zarafin al’umma a harkokin rabon gado.

Masarautar Zazzau ta dakatar da shugaban ƙauyen Matarawa bisa zargin damfara da cin zarafin al’umma a harkokin rabon gado. A cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na masarautar, Abdullahi Aliyu Kwarbai, ya fitar, Sarkin Zazzau, Mallam Ahmed Nuhu Bamalli, ya gargaɗi hakimai da shugabannin ƙauyuka da su guji cutar da jama’a musamman a harkokin rabon gado. Sanarwar ta ce Sarkin ya umarci hakimai da su sanya ido sosai kan yadda shugabannin ƙauyuka ke gudanar da harkokinsu na yau da kullum da al’umma. Haka kuma sanarwar ta bayyana cewa bayan kammala dawo da kuɗaɗen da aka ka

Kungiyar Shugabannin ƙananan hukumomi ALGON reshen jihar Kaduna ta karyata rahoton jaridar Sahara Reporters da ya yi zargin gwamnatin jihar na wawure kuɗaɗen ƙananan hukumomi tare da hana su amfani da kudaden gudanar da ayyuka.

Shugaban ALGON na Jihar Kaduna Muhammad Jamilu Abubakar Albani ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu. Sanarwar ta ce babu gaskiya a rahoton da Sahara Reporters ta wallafa cewa shugabannin kananan hukumomi na karbar kasa da naira miliyan 25 duk wata duk da tarin kudaden da ake turo musu daga gwamnatin tarayya. Ya ce gwamnatin Kaduna ta samar da tsarin biyan albashi ta hanyar fasahar zamani na e-payment tare da tabbatar da biyan albashi, fansho da sauran hakkokin ma’aikata kai tsaye bisa hukuncin kotun koli na cin gashin kan kananan hukumomi. Kungiyar ta kuma bukaci Sahar

Gwamnan kano Abba Kabir yusuf ya kafa kwamitin mutum 13 domin shirya gagarumin bikin cikarsa shekara uku akan mulki

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanya wa hannu Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Umar Farouk Ibrahim ne zai jagoranci kwamitin a matsayin shugaba. Sauran mambobin kwamitin sun hada da: Engr. Marwan Ahmad – Kwamishinan Ayyuka Dr. Abubakar Labaran Yusuf – Kwamishinan Lafiya Dr. Dahir Muhammad Hashim – Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi Dr. Danjuma Mahmoud – Kwamishinan Noma da Albarkatun Kasa Dr. Gwani Ali Haruna Abubakar Makoda – Kwamishinan Ilimi Hon. Abduljabbar Umar Garko – Kwamishinan Kasa da Tsare-tsaren Hon. Abdulkadir

Gwamnatin Jihar Jigawa ta samar da kwale-kwalen gudu guda 20 domin ƙarfafa ayyukan kwashe mutane da bayar da agajin gaggawa

Gwamnatin Jihar Jigawa ta samar da kwale-kwalen gudu guda 20 domin ƙarfafa ayyukan kwashe mutane da bayar da agajin gaggawa a yankunan da ambaliya ke yawan shafa a jihar. Mai bai wa Gwamna Umar Namadi shawara na musamman kan muhalli, Hamza Muhammad, ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN a Dutse. Ya ce matakin zai tabbatar da saurin kwashe mutanen da ambaliya ta rutsa da su a al’ummomin da ke fama da ambaliya.

Ministan kiwon lafiya na Jamhuriyar demokkuradiyyar Congo,Samuel Kamba ya bayyana cewa cutar da ta bullu a ƙasar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 153

Ministan kiwon lafiya na Jamhuriyar demokkuradiyyar Congo,Samuel Kamba ya bayyana cewa cutar da ta bullu a ƙasar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 153,daga cikin mutane 626 da aka gano sun kamu da ita. Ministan ya bayyana yankunan Ituri dake karkashin ikon jihar Bunia da yankin Mongwalu ida lamarin ya fi kamari,duk da cewa akwai wasu yankuna da cutar ta bullu. Ya zuwa wannan lokaci,arewacin Kivu ne cutar ta bayyana inda aka gano mutum daya da ya kamu da ita a Goma,biyu a Butembo,wacce ba ta tsaya a nan ba,ta kuma bazu zuwa kudancin Kivu. Rahotanni daga yankunan da ke karkashin ikon ƴan tawayen M

Ministan Tsaro Janar Christopher Musa ya bayyana cewa ayyukan ta’addanci na daga cikin manyan barazanar da ke addabar ƙasar nan.

Ministan Tsaro Janar Christopher Musa ya bayyana cewa ayyukan ta’addanci na daga cikin manyan barazanar da ke addabar ƙasar nan. Da yake jawabi a Abuja yayin ƙaddamar da wani littafi mai taken ayyukan yaki da Ta’addanci da tada Ƙayar Baya a Arewa maso Gabas, Wanda tsohon Kwamandan Rundunar Haɗin Gwiwa ta MNJTF kuma tsohon Shugaban Kwalejin horas da sojoji Manjo Janar Ibrahim Yusuf mai ritaya ya rubuta. Christoper Musa ya jaddada cewa nasarar kawar da ta’addanci na buƙatar haɗin kai da jajircewar rundunar soji, hukumomin gwamnati da kuma al’umma baki ɗaya. Ya yi kira da a ƙara ƙarfafa haɗin gw

Mai bawa Gwamnan Jihar Oyo shawara ta musamman kan harkokin tsaro Abayomi Fagbenro ya musanta sako mutanen da sace a harin da aka kai makarantu uku a Karamar Hukumar Oriire a ranar Juma’ar da ta gabata

Mai bawa Gwamnan Jihar Oyo shawara ta musamman kan harkokin tsaro Abayomi Fagbenro ya bayyana cewa rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta dake cewa an sako mutanen da aka sace a harin da aka kai makarantu uku a Karamar Hukumar Oriire a ranar Juma’ar da ta gabata ba gaskiya ba ne. Harin da aka kai makarantun ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutum biyu tare da sace kusan malamai da ɗalibai 30. Tun daga daren ranar Laraba, rahotannin ke cewa an sako malamai da ɗaliban da aka sace a harin. Sai dai da yake zantawa da manema labarai game da tabbatar da sahihancin labarin, mai bawa gwamanan shawa

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya lashe tikitin takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen 2027

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya lashe tikitin takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen 2027 A wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar, ta ce ya zama ɗantakarar jam'iyyar ne bayan samun kuri’un amincewa daga wakilan jam'iyyar a yayin zaɓen fitar da gwani da aka gudanar a yau Alhamis. Ta ce an gudanar da zaɓen fitar da gwanin ne a gaban jami’an hukumar zaɓe ta INEC. Shugaban kwamitin gudanar da zaɓen Hon. Hafiz Ibrahim Kawu, ya ce an gudanar da zaɓen cikin lumana.

Rundunar ƴansandan jihar Kano, ta sanar da nasarar kama waɗanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban harsu 248 a cikin wata guda.

Rundunar ƴansandan jihar Kano, ta sanar da nasarar kama waɗanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban harsu 248 a cikin wata guda, waɗanda suka kunshi ƴan fashi da makami da masu garkuwa da mutane da masu safarar miyagun kwayoyi da ƴan daba da dai sauransu. Kwamishinan ƴansandan jihar CP Ibrahim Adamu Bakori ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke gabatar da waɗanda ake a shalkwatar rundunar dake Kano. Ya ce a lokacin wannan aiki da suka gudanar daga 20 ga watan Afrilu zuwa 20 ga Mayu, sun samu nasarar kama ƴan fashi da makani 18 da masu garkuwa da mutane 5 da masu safarar miyagun kwayoyi 32

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya musanta rahotannin da ke cewa yana shirin sauya sunan Najeriya tare da soke Shari’ar Musulunci a Arewacin kasar nan.

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya musanta rahotannin da ke cewa yana shirin sauya sunan Najeriya tare da soke Shari’ar Musulunci a Arewacin kasar nan. wannan na cikin sanarwar da Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai, Bayo Onanuga ya fitar. Sanarwar ta ce babu gaskiya a rahotannin da ke yawo cewa Tinubu na shirin gabatar da kudirin gyaran kundin tsarin mulki domin sauya sunan kasar nan zuwa United States of Nigeria. Ya ce wasu ‘yan siyasa ne ke yada rahotannin karya domin haddasa rikici da tayar da hankalin jama’a gabanin babban zaben 2027. Fadar shugaban kasa ta kuma bukaci ‘y

Gwamnatin Jihar Bauchi ta dage dakatarwar da ta sanya kan harkokin kasuwanci

Gwamnatin Jihar Bauchi ta dage dakatarwar da ta sanya kan harkokin kasuwanci a wasu kasuwannin shanu da ke jihar gabanin bikin babbar Sallah mai zuwa. A baya gwamnatin jihar ta dakatar da ayyukan kasuwanci a wasu kasuwannin shanu da ke kananan hukumomin Alkaleri, Bauchi, Kirfi da Tafawa Balewa saboda matsalolin tsaro. Sai dai cikin wata sanarwa da mai bai wa gwamna shawara kan harkokin yada labarai, Mukhtar Gidado, ya fitar, ya ce Gwamna Bala Mohammed ya amince da dage dakatarwar domin bai wa jama’a damar sayen dabbobin layya kafin sallah. Sanarwar ta ce matakin zai yi aiki na tsawon makonni b

NAHCON ta kammala jigilar Mahajjatan Nijeriya zuwa Saudiyya

NAHCON ta kammala jigilar Mahajjatan Nijeriya zuwa Saudiyya Hukumar Alhazai ta Nijeriya NAHCON ta sanar da kammala jigilar Mahajjatan 2026 zuwa ƙasar Saudiyya. Hukumar ta ce an kammala jigilar ne bayan jirgin ƙarshe na kamfanin Max Air da ya tashi daga filin jirgin saman Gusau ɗauke da Mahajjatan jihar Zamfara. Jaridar Daily Trust ta ruwaito NAHCON ta bayyana cewa an kammala tashin jiragi na 98 cikin kwanaki 18, inda Nijeriya ta samu guraben maniyyata 50,000 a Hajjin bana

Kungiyar malaman makarantun sakandare da firamare ta kasa (NUT) ‎, ta bayyana matukar damuwa kan yadda hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane ke kara kamari a makarantu

Kungiyar malaman makarantun sakandare da firamare ta kasa (NUT) ‎, ta bayyana matukar damuwa kan yadda hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane ke kara kamari a makarantu, tana mai gargadin cewa hakan na iya tilasta malamai janye ayyukansu idan gwamnati ba ta dauki matakin gaggawa ba. ‎A wata sanarwa da shugaban kungiyar na kasa, Audu Amba, tare da babban sakataren kungiyar suka sanyawa hannu, kungiyar ta ce makarantu sun daina zama wuraren koyarwa cikin kwanciyar hankali, inda suka koma filin hare-haren ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda. ‎Kungiyar ta bayyana hare-haren a matsayin abinda y

Shugaban ƙasar amurika Donald Trump ya sanar da cewa tattaunawar zaman lafiya da Iran ta kai matakin karshe

Shugaban ƙasar amurika Donald Trump ya sanar da cewa tattaunawar zaman lafiya da Iran ta kai matakin karshe, inda ya ba wa kasar wa’adin kwanaki biyu zuwa uku kacal domin ta amince da yarjejeniyar, ko kuma ta fuskanci mummunan harin soja. Wannan sanarwa ta zo ne bayan matakin da Trump ya ɗauka na dakatar da wani babban harin bam da Amurka ta shirya kai wa Iran. Shugaban ya bayyana cewa ya janye harin ne bayan buƙata da shawara daga shugabannin ƙasashen Larabawa na yankin Gulf, waɗanda ke ganin akwai alamun samun maslaha. Trump ya jaddada cewa lokaci yana ƙure wa Iran, yana mai barazanar cewa

Mayaƙan Boko Haram sun kashe matsunta da masu sarar itatuwa 33 a wasu hare-hare biyu da suka ƙaddamar a jihar Borno.

Wasu majiyoyi biyu ne suka tabbatar da afkuwar harin ga kamfanin dillancin labaran Faransa, a cewar wasu masu yaƙi da ayyukan mayaƙan da kuma jami’in ƙungiyar masunta da ke yankin sun ce tun a ranar litinin ɗin da ta gabata mayaƙan suka kai hari a yankin Mafa inda suka kashe masunta 27, sai kuma a yankin Dikwa da suka kashe masu sarar itatuwa shida. Shugaban ƙungiyar masu kamun kifin na Maidugurin Abdullahi Sani ya ce matsuntan na kan hanyar su ta dawowa daga aiki lokacin da maharan suka afka musu. Gabanin nan, mayaƙan Boko Haram sun harɓe masu sarar itatuwa shida lokacin da suke karɓar itace

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta lalata jabun kayayyaki, magungunan da wa’adin su ya ƙare

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta lalata jabun kayayyaki, magungunan da wa’adin su ya ƙare da kuma marasa inganci da darajarsu ta haura naira biliyan 1.8 a birnin tarayya Abuja. An gudanar da aikin lalata kayayyakin ne a ƙaramar hukumar Kuje, inda aka ƙone magunguna, kayan abinci, kayan kwalliya, sinadarai, na’urorin lafiya da barasa da hukumar ta kwace daga hannun masu sayarwa da masu safararsu. Babbar Daraktar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta bayyana yaɗuwar jabun kayayyaki a matsayin barazana ga tsaron ƙasa. NAFDAC ta bayyana cewa masu jabun kaya sun ƙara a