AMMASCO RADIO NEWSROOM

Labarai

Magoya bayan Senegal sun samu ‘yanci bayan tsarewa a Maroko

Sarkin Maroko Mohammed na shida ya yi afuwa ga wasu magoya bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Senegal da aka daure bayan samun su da hannu a tayar da tarzoma a wasan ƙarshe na gasar cin kofin Afrika da aka gudanar a birnin Rabat a watan Janairun 2026. An saki magoya bayan ne a wani mataki na jin ƙai da kuma ƙarfafa dangantaka tsakanin Maroko da Senegal, musamman yayin da ake shirin gudanar da Babbar Sallah. Shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya bayyana a shafinsa na X cewa nan ba da jimawa ba magoya bayan za su koma wajen iyalansu. “Ina miƙa godiyata ga mai martaba saboda wannan mataki na ta

Gwamnatin Ghana ta amince da aikin haƙar zinare na dala biliyan ɗaya

Gwamnatin Ghana ta zaɓi wani kamfanin cikin gida mai suna Engineers & Planners Ltd domin ya karɓi ragamar gudanar da aikin haƙar zinare na Damang daga kamfanin Gold Fields, kamar yadda ministan harkokin ma’adinai na ƙasar ya bayyana a ranar Talata. Matakin na daga cikin ƙoƙarin da Ghana ke yi na ƙarfafa kamfanonin cikin gida a fannin haƙar ma’adinai, musamman a masana’antar zinare da ƙasar ta shahara da ita. A bara ne gwamnatin Ghana ta ƙi sabunta lasisin kamfanin Gold Fields mai hedkwata a Johannesburg, inda ta karɓe ikon gudanar da aikin haƙar ma’adinan na Damang, lamarin da ya kawo ƙarshen

China za ta daina karɓar haraji kan kayayyakin ƙasashen Afirka 53

A ranar Juma’a ne China ta sanar da faɗaɗa cire haraji kan kayayyakin da ake shigar mata daga dukkan ƙasashen Afirka da ke da alaƙar diflomasiyya da ita, a wani mataki da ke da nufin ƙarfafa kasuwanci da bunƙasa masana’antu a nahiyar, kamar yadda kafafen yaɗa labaran gwamnati suka ruwaito. A ƙarƙashin sabon tsarin, ƙasashen Afirka 53 ne za su amfana da cire harajin shigo da kaya, ciki har da Nijeriya da Kenya da Masar, a cewar kamfanin dillancin labarai na Xinhua. Sabuwar manufar ta ƙara faɗaɗa tsarin da China ta riga ta aiwatar, wanda ya bai wa ƙasashe 33 mafi ƙarancin ci gaba a Afirka damar

NNPC ta zargi matatar Dangote da neman mamaye kasuwar man Nijeriya

Kamfanin mai na Nijeriya, NNPC, ya zargi matatar mai ta Dangote da yunƙurin mamaye kasuwar man fetur ta ƙasar ta hanyar ƙalubalantar lasisin shigo da mai da aka bai wa wasu kamfanonin da ke gogayya da ita, kamar yadda takardun kotu da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gani suka nuna. A cikin bayanan kariya da ya gabatar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Legas, NNPC ya ce idan har aka amince da buƙatar Dangote na soke ko rage yawan lasisin shigo da mai, hakan na iya haddasa matsala wajen samar da mai, da rashin daidaiton farashi, tare da barazana ga tsaron makamashin Nijeriya. Hukumar K

Shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye, ya kori Firaminista Ousmane Sonko

Shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya kori Firaminista Ousmane Sonko daga muƙaminsa a wani mataki da ya jawo cece-kuce a fagen siyasar ƙasar. Rahotanni sun bayyana cewa matakin korar ya biyo bayan zazzafar muhawara da aka yi a majalisar dokokin Senegal, inda Firaminista Sonko ya fito fili ya soki salon mulkin shugaban ƙasar. Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ƙarin rikice-rikicen siyasa a ƙasar, inda masu sa ido ke ganin cewa zai iya ƙara haifar da saɓani a tsakanin manyan jami’an gwamnatin Senegal

Ambasada Yusuf Maitama Tuggar bai samu tikitin takarar gwamnan jihar Bauchi ba.

Yusuf Tuggar bai samu tikitin takarar gwamnan jihar Bauchi ba. Ambasada Yusuf Maitama Tuggar bai samu tikitin takarar gwamnan jihar Bauchi ba, a jam’iyyar APC. Hakan ya biyo bayan kai ruwa rana tsakanin masu ruwa da tsaki na jihar, kafin daga ƙarshe su tabbatar da tsohon gwamnan Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar a matsayin ɗan takarar gwamnan Bauchi na Jam'iyyar APC, a zaɓen 2027.

Farfesa Usman Yusuf ya shigar da kara gaban DSS kan Kwankwaso bisa zaegin yi masa barazana

A cikin takardar ƙorafin mai ɗauke da kwanan watan 22 ga Mayu, 2026, Farfesa Usman Yusuf ya ce kalaman sun biyo bayan sharhin da ya yi kan haɗakar siyasa da kuma batutuwan siyasar yankuna. Ya bayyana cewa ko da yake Sanata Kwankwaso bai ambaci sunansa kai tsaye ba, amma bayanin da ya yi ya isa ya sa masu sauraro gane wanda ake nufi. Farfesa Yusuf ya kuma yi zargin cewa Sanatan ya bukaci magoya bayan Kwankwasiyya da wasu ƙungiyoyin matasa su “tarwatsa” wanda ake magana a kansa da kalmar Hausa ta “fata-fata,” lamarin da ya ce na iya jawo tsoratarwa ko tashin hankali.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Filato ta cafke wasu mutane shida bisa zargin satar shanu

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Filato ta cafke wasu mutane shida bisa zargin satar shanu, hada baki wajen aikata laifi da kuma mallakar bindigu ba bisa ka’ida ba. Arewa Updates ta rawaito cewa, Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Bassey Ewah ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da sashen yaki da manyan laifuka na VCRU a Jos. Ya ce an cafke daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Yahuza Sale bayan wani bidiyo da ya wallafa a Facebook wanda ake zargin yana tayar da hankalin jama’a. Sanarwar ta ce Yahuza ya amsa cewa yana hada baki da wani Victor Danladi wanda aka fi sani da Boka wajen satar shanu ta am

Osimhen ya kai ziyara tsohuwar makarantar firamare da ya yi karatu

Osimhen ya kai ziyara tsohuwar makarantar firamare da ya yi karatu, ya kuma bai wa mai gadi kyautar Naira miliyan 20. “Shi ne mai gadin makarantar lokacin da nake karatu a nan. Yakan siya min biskit da ice cream lokacin muna yara ƙanana. Wasu lokutan nakan zo makaranta ban ci komai ba, sai ya ɗauki abincinsa ya ba ni. Ga sauran ɗalibai shi mai gadi ne kawai, amma a wurina tamkar uba yake gare ni. Ba zan taɓa mantawa da shi ba.”

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke wasu sassan jadawalin zaben 2027 da Hukumar INEC ta fitar

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke wasu sassan jadawalin zaben 2027 da Hukumar INEC ta fitar, bayan wata kara da jam'iyyar YP ta shigar. Mai shari'a Mohammed Umar ya ce wasu wa'adin da INEC ta kayyade wa jam'iyyun siyasa sun saba wa Dokar Zabe ta 2026, musamman batun lokacin gudanar da zaben fidda gwani, gabatar da sunayen 'yan takara, janye takara da maye gurbin 'yan takara. Kotun ta bayyana cewa INEC ba ta da ikon rage ko sauya wa'adin da doka ta tanada, tare da cewa ba za ta iya kayyade karshen yakin neman zabe ko fitar da jerin 'yan takara ta hanyar da ta saba wa doka ba

Nico Páz ba zai koma Inter ko wata ƙungiya ba a wannan bazarar, kamar yadda Cesc Fabregas ya bayyana!

Nico Páz ba zai koma Inter ko wata ƙungiya ba a wannan bazarar, kamar yadda Cesc Fabregas ya bayyana! “Zan iya tabbatar muku cewa Nico Páz zai buga wa 𝐑𝐄𝐀𝐋 𝐌𝐀𝐃𝐑𝐈𝐃 ko kuma 𝐂𝐎𝐌𝐎 kawai, babu wata ƙungiya daban,” in ji Fabregas. Real Madrid na da damar dawo da shi kan €9m a wannan bazarar, sannan kuma akwai damar €10m a shekarar 2027. Real Madrid tare da sabon koci José Mourinho ne za su yanke hukunci nan ba da jimawa ba.

NBS: Kudin abinci mai lafiya ya kai N1,513 a kowace rana a watan Fabrairu

Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana cewa matsakaicin kudin cin abinci mai lafiya ga mutum guda a Najeriya ya kai N1,513 a kowace rana a watan Fabrairu. Hukumar ta bayyana hakan ne cikin rahotonta na “Cost of a Healthy Diet (CoHD)” na watan Fabrairu 2026 da aka fitar a Abuja. A cewar NBS, wannan adadi ya karu da kashi 3.76 idan aka kwatanta da N1,458 da aka samu a watan Janairu 2026. Hukumar ta bayyana cewa CoHD shi ne mafi arha hadin abinci daga cikin kayan abinci na gida da ake samu, wanda ke cika ka’idojin abinci mai gina jiki da aka amince da su a duniya. Ta ce ana amfani da wannan m

ICPC ta bayyana dalilin hana shugabannin ADC ganin El-Rufai

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka masu Alaƙa (ICPC) ta kare matakin da ta dauka na hana shugabannin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ganin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, tana mai cewa matakin ya yi daidai da umarnin kotu da ke kan lamarin. Kakakin hukumar, John Odey, ne ya bayyana haka ga PUNCH Online a ranar Asabar, yayin da yake mayar da martani kan zargin da ADC ta yi na cewa an hana shugabanninta shiga kuma an nuna musu rashin mutunci yayin ziyarar da suka kai ranar Juma’a. Odey ya ce ICPC ta riga ta mayar da martani ga wasikar da ADC ta aike t

Bauchi: Aikin gwamnati ba na sayarwa ba — gwamnati ta gargadi jama’a kan tayin aiki na bogi

Gwamnatin Jihar Bauchi, ta hannun Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnati ta Jiha (Civil Service Commission), ta gargadi jama’a da su guji karɓar tayin aikin bogi, tana mai jaddada cewa ayyukan gwamnati a jihar ba na sayarwa ba ne. Wannan gargadi ya biyo bayan cafke wani mutum mai suna Saleem Alhassan, wanda aka fi sani da “Jagaban Ningi,” da rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta yi bisa zargin forgery da wasu laifuka masu alaƙa. Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai a ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnati na jihar Bauchi, Awwal Waziri, ya fitar a ranar Asabar. A cewar sanar

Kwara ta farfado da cibiyoyin kiwon lafiya 100, ta dauki ma’aikatan lafiya 1,000

Gwamnatin Jihar Kwara ta kara kaimi wajen inganta harkar kiwon lafiya matakin farko ta hanyar farfado da cibiyoyin Primary Health Care (PHC) 100 tare da daukar fiye da ma’aikatan lafiya 1,000 a fadin jihar. Babbar Sakatariyar Hukumar Kula da Cibiyoyin Kiwon Lafiya na Matakin Farko ta jihar Kwara, Nusirat Elelu, ta bayyana hakan a wani taron tattaunawa da al’umma da aka gudanar a Ilorin, inda aka samu halartar masu ruwa da tsaki daga kananan hukumomi 16 na jihar. A cewar wata sanarwa da aka fitar ranar Asabar daga Kakakin hukumar, Bukola Abdulganiyu, an shirya taron ne domin karfafa hadin kai t

Fiye da mahajjata miliyan 1.5 sun isa Saudiyya domin aikin Hajji

Fiye da mahajjata miliyan 1.5 daga kasashe daban-daban sun isa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin bana, lamarin da ya zarce adadin bakin hajjin da suka halarci aikin hajji daga kasashen waje a shekarar 2025. Wani jami’in Saudiyya ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai, inda ya ce duk da rikice-rikicen da suka faru a yankin Gabas ta Tsakiya, mahajjata sun ci gaba da tururuwa zuwa kasar domin sauke farali. Rahotanni sun nuna cewa rikicin da ya biyo bayan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran a watan Fabrairu ya haddasa matsaloli a harkar zirga-zirgar jiragen sama

Babbar Kotun Tarayya ta yi jimamin rasuwar alkalin Kano

Babbar Kotun Tarayya ta Najeriya ta sanar da rasuwar daya daga cikin alkalanta masu zaman kansu, Mai shari’a Mohammed Yunusa na bangaren shari’a na Kano. Daraktar yada labarai ta kotun, Catherine-Oby Christopher, ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da aka fitar a Abuja ranar Asabar. Sanarwar ta ce Mai shari’a Yunusa ya rasu ne ranar Alhamis bayan gajeriyar rashin lafiya a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Jihar Kano. An kuma bayyana cewa an riga an yi masa jana’iza bisa koyarwar addinin Musulunci. Kotun ta bayyana marigayin a matsayin fitaccen masani a harkar shari’a wanda ya yi aiki da kwarewa, gaskiya

Majalisar Dinkin Duniya: ‘Yan Najeriya miliyan 35 na fuskantar barazanar matsananciyar yunwa a watanni masu zuwa

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa kusan mutane miliyan 35 a Najeriya na cikin hadarin fama da matsananciyar yunwa daga watan Yuni zuwa Agusta na wannan shekara. Kungiyar kula da harkokin jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana hakan a birnin New York na kasar Amurka, inda ta ce Najeriya na fuskantar karin matsalar karancin abinci yayin da lokacin fari da wahalar samun abinci ke kara matsowa. A cewar rahoton, kusan mutum daya cikin mutane bakwai a Najeriya na iya fuskantar matsananciyar rashin wadataccen abinci a watanni masu zuwa. Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa Najeriya ya

Sace Dalibai a Oyo: Wadanda ake zargi da ta’addanci sun fara tattaunawa, sun gindaya sharadi

Mutanen da ake zargi da kai harin sace dalibai da malamai a makarantu uku da ke garuruwan Esinele, Yamota da Alawusa a karamar hukumar Oriire ta jihar Oyo sun bude hanyar tattaunawa da gwamnatin jihar. Majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa masu garkuwar sun ki yin magana da iyalan wadanda aka sace, inda suka ce suna son tattaunawa kai tsaye da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, kuma wannan ne sharadin da suka bayar. Wata majiya ta ce har yanzu ba a bayyana cikakken bayanin tattaunawar ko bukatun masu garkuwar ba domin kare rayukan wadanda ke hannunsu. Har yanzu ba a tabbatar ko gwamnan ne da kans

Pep Guardiola zai bar Manchester City a ƙarshen kakar wasa

Pep Guardiola ya tabbatar da cewa zai bar Manchester City a ƙarshen kakar wasa, inda hakan zai kawo ƙarshen shekaru goma masu cike da nasarori da kofuna. Ku gano irin tasirin da Guardiola ya yi a Manchester City.