AMMASCO RADIO NEWSROOM

Labarai

Hukumar Hisbah ta kama wani mutum bisa zargin yi wa yarinya mai shekara 11 fyaɗe

Hisbah a ƙaramar hukumar Dutsinma da ke jihar Katsina ta kama wani mutum bisa zargin yi wa wata yarinya mai shekara 11 fyaɗe a unguwar Bakin Sabuwar Kasuwa. A cewar sanarwar da jami’in sashen fasahar sadarwa na Hisbah a Dutsinma, Malam BYAREEMA ya fitar, mazauna unguwar ne suka kama wanda ake zargin tare da tsare shi kafin jami’an Hisbah suka isa wurin domin karɓarsa da fara bincike. Sanarwar ta ƙara da cewa an samu wanda ake zargin cikin maye yana riƙe da wandonsa a hannu. Hukumar Hisbah ta yaba da haɗin kan al’umma wajen taimakawa jami’an tsaro, tare da kira ga iyaye su ƙara sanya ido kan ya

Amurka na barazanar ƙara ƙaƙaba wa Iran takunkumi

Amurka na ƙara matsa wa Iran lamba ta hanyar sabbin matakan takunkumin tattalin arziƙi, da nufin tilasta mata buɗe Mashigar Hormuz. Sakataren Kuɗin Amurka, Scott Bessent, ya bayyana cewa Amurka za ta hana jiragen sama mallakin kamfanonin Iran sauka a wasu filayen jiragen sama, a wani mataki da ake ganin zai ƙara matsin tattalin arziƙi kan ƙasar. Wannan sanarwa ta biyo bayan matakan da Ma’aikatar Kuɗin Amurka ta ɗauka kwana ɗaya kafin hakan, inda ta bayyana sabbin tsare-tsare da suka shafi wata hukuma da ke karɓar haraji kan jiragen ruwan da ke wucewa ta Mashigar Hormuz, wata muhimmiyar hanya t

Atiku ya ziyarci Amaechi bayan lashe tikitin takarar ADC

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, wanda ya lashe zaɓen fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a ranar Laraba, ya kai ziyara ga abokin karawarsa, tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, a Abuja. A yayin sanar da sakamakon zaɓen, shugaban jam’iyyar ADC na ƙasa, David Mark, ya bayyana cewa Atiku ne ya yi nasara da ƙuri’u 1,846,370, inda ya kayar da Amaechi da kuma Mohammed Hayatu-Deen wanda ya zo na uku. Bayan sanar da sakamakon, an fara samun raɗe-raɗi kan yiwuwar rikici, ganin cewa tun kafin kammala kirga ƙuri’u wasu ‘yan takara sun nuna rashin gamsuwa da tsarin zaɓe

Sabon rahoton Amurka kan Fulani a Najeriya: Me ya ce?

Wani rahoto da ake danganta shi da Amurka ya yi zargin cewa wasu Fulani masu ɗauke da makamai na ci gaba da mamaye gonakin Kiristoci tare da kai hare-hare kan wuraren ibada na Kiristoci da Musulmai a Najeriya. Rahoton ya bayyana cewa a ‘yan shekarun nan, wasu masu ɗauke da makamai da ake dangantawa da Fulani sun kai hare-hare a kan al’ummomi daban-daban, ba wai Kiristoci kaɗai ba, a sassa daban-daban na ƙasar. Haka kuma ya yi iƙirarin cewa wasu daga cikin waɗannan ƙungiyoyi na Fulani ‘yan bindiga suna kai hare-hare kai tsaye, yayin da wasu lokuta kuma suke haɗa kai da ‘yan fashin daji da kuma

NLC ta soki gwamnati kan matsalar tsaro da taɓarɓarewar tattalin arziki

Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya (NLC) ta bayyana damuwarta kan ci gaba da tabarbarewar matsalar tsaro da kuma ƙalubalen tattalin arziki da ake fuskanta a ƙasar. A cikin saƙon barka da Sallah da Shugaban NLC, Joe Ajaero ya fitar, ƙungiyar ta ce ma’aikatan Najeriya da talakawa na cikin matsanancin ƙunci sakamakon wasu manufofi da ake aiwatarwa. Ya ce miliyoyin ‘yan ƙasa na fuskantar tsadar rayuwa da ke ƙara jefa su cikin talauci, tare da yin kira ga ‘yan siyasa da su sake duba tasirin matakan tattalin arzikinsu. NLC ta kuma bukaci gwamnati da ta ɗauki matakan gaggawa wajen shawo kan matsalar tsaro

Isra’ila ta kai hare-hare kan birnin Beirut na ƙasar Lebanon

Isra’ila ta kai hari a birnin Beirut, babban birnin Lebanon, karo na biyu tun bayan fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta a watan da ya gabata. Dakarun Isra’ila (IDF) sun ce an shirya harin ne kan wani takamaiman buri, sai dai ba su bayar da cikakken bayani ba. Kafofin yaɗa labarai na Isra’ila sun ambato wasu majiyoyi da ba a bayyana sunayensu ba suna cewa wanda aka nufa da harin wani jagoran ƙungiyar masu ɗauke da makamai masu samun goyon bayan Iran ne. Rahotanni sun ce Isra’ila ta sassauta harin kan Beirut ne bisa roƙon Shugaban Amurka, Donald Trump, yayin da hare-haren suka biyo bayan jer

Ghana ta dawo da ƴan ƙasarta 300 daga Afirka ta Kudu sakamakon zanga-zangar adawa da baƙin haure.

Jirgin farko da ke ɗauke da ‘yan Ghana da aka kwashe daga Afirka ta Kudu saboda tashin hankalin da ya shafi adawa da baƙin haure ya isa birnin Accra ranar Laraba, kamar yadda Ma’aikatar Harkokin Wajen Ghana ta bayyana. Ana sa ran kusan ‘yan Ghana 800 ne za su bar Afirka ta Kudu, bayan gwamnatin Ghana ta shirya jiragen dawo da su sakamakon zanga-zangar ƙin jinin baƙi da ta ɓarke a wasu sassan ƙasar. Wani mai ɗaukar hoto na AFP ya ga daruruwan ‘yan Ghana suna tsaye a layi a Filin Jiragen Sama na O.R. Tambo da ke wajen Johannesburg da safiyar Laraba domin komawa gida. Shafin FlightAware da ke bib

Sandy Onor ne Dan takarar shugaban kasa na PDP tsagin Wike

Jam’iyyar PDP tsagin ministan Abuja, Nyesom Wike, ta tabbatar da tsohon ɗan majalisar tarayya, Sandy Onor, a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027. Shugaban kwamitin zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na jam’iyyar, Samuel Ortom, ne ya sanar da hakan a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja. Ortom, wanda tsohon gwamnan jihar Benue ne, ya ce Onor ya zama ɗan takarar jam’iyyar ne ta hanyar yarjejeniya bayan tattaunawa da wakilan jihohi 36 da kuma Abuja. Shi ma shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Abdullahi Mohammed, ya bayyana cewa jam’iyyar na da ɗan takara guda ɗaya kacal, yana mai

Sama da yan Najeriya 1600 ne suka rasa ransu kan siyasa cikin shekaru 24

Majalisar dattawan Najeriya ta ce aƙalla mutane dubu 1,639 ne suka mutu sanadiyyar rikicin zaɓe daga shekarar 1999 zuwa 2023 a faɗin ƙasar. Dan majalisar Opeyemi Bamidele daga jihar Ekiti ne ya sanar da alƙaluman a matsayin wata babbar matsala ga ƙasa, wadda ya kamata a taka mata birki. Yana mai cewa bai kamata ƴan Najeriya su riƙa rasa rayukansu ba sanadiyyar muradunsu na siyasa. Sanatan na jihar Ekiti, ya yi wannan kira ne cikin saƙonsa na babbar sallah a jiya Laraba. Bamidele ya ce binciken cibiyar da ke bibiyar rikice rikice, shi ne ya gano yadda aka rasa rayukan ɗimbin mutane daga 1999 zu

Akalla mutane 16 ne suka mutu da 58 suka ji rauni a wani harin Isra'ila a Lebanon

Akalla mutane 16 ne suka mutu yayin da wasu 58 suka jikkata sakamakon hare-haren Isra’ila a kudancin Lebanon, kamar yadda hukumomin lafiya na Lebanon suka bayyana, yayin da Isra’ila ke kara tsananta hare-harenta tare da bayar da umarnin kwashe jama’a da dama daga yankin. Kamfanin dillancin labarai na gwamnatin Lebanon, wato National News Agency, ya rawaito a ranar Alhamis cewa mutum shida daga cikin wadanda suka mutu ‘yan gida daya ne. Rahoton ya ce sun mutu ne sakamakon harin jirgin yaki maras matuki na Isra’ila yayin da suke kokarin tserewa da asubahin kan babbar hanyar Adloun, wata muhimmi

Masu amfani da layukan sadarwa a Najeriya sun sake samun damar cin gajiyar ayyukan aron katin waya na gaggawa

Masu amfani da layukan sadarwa a Najeriya sun sake samun damar cin gajiyar ayyukan aron katin waya na gaggawa bayan Hukumar Kare Gasa da Kare Haƙƙin Mabukata ta Tarayya (FCCPC) ta dakatar da aiwatar da dokokinta na bayar da rancen kuɗi ta yanar gizo da hanyoyin zamani, wato ‘Digital, Electronic, Online or Non-Traditional Consumer Lending (DEON) Regulations 2025’. Matakin ya biyo-bayan umarnin da Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta bayar, inda ta umurci hukumar da ta dakatar da aiwatar da sabbin dokokin har sai an kammala shari’ar da ke ƙalubalantar ikon FCCPC na sa-ido kan tsarin aron katin wa

Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya ba al'ummar jihar damar yin layya su raba nama ga mutanen da basu samu damar yin layyar ba

Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya buƙaci al'ummar jihar da suka samu damar yin layya su raba nama ga mutanen da basu samu damar yin layyar ba kamar yadda Musulunci ya tanada. Gwamnan ya yi wannan bayani ne a saƙonsa na ranar Idi a jiya Laraba. A cewarsa, yin hakan zai kawo “sauƙi ga mutane masu rauni, baya ga samun lada daga Allah”. Ya ƙara da cewa Musulunci ya riga yayi bayani kan yadda ake raba naman layya, saboda haka ya kamata al'umma su bi ƙa'idar. A cewarsa, gwamnatin jihar na kashe maƙudan kuɗaɗe a kowace shekara wajen tallafa wa malaman addini da mabuƙata da ƴan-gudun hijira waɗanda

Atiku Abubakar ya Zama Dan takarar shugaban kasa a Jam'iyar hamayya ta ADC

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC domin babban zaɓen shekarar 2027. An sanar da sakamakon zaben ne a daren Laraba cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin X na jam’iyyar, inda aka bayyana cewa Atiku ya doke tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi da kuma tsohon ma’aikacin banki, Mohammed Hayatu-Deen a takarar. Atiku ya kayar da Amaechi da Hayatudeen domin samun tikitin takarar shugaban ƙasa na ADC. Sakamakon ƙarshe ya nuna cewa, Atiku Abubakar ya sami kuri’u 1,855,787 inda Amaechi ya samu kuri’u 509,397 sai kuma Hayatudeen

Tinubu ya bayar da wannan umarni ne cikin saƙonsa na bikin Ranar Yara ta shekarar 2026 wato yau Laraba

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci hukumomin tsaro da ma’aikatun da abin ya shafa da su ƙara ƙaimi wajen kare makarantu da ke yankunan da ake fuskantar barazanar tsaro a faɗin ƙasar nan. Tinubu ya bayar da wannan umarni ne cikin saƙonsa na bikin Ranar Yara ta shekarar 2026 wato yau Laraba, kamar yadda jaridar PUNCH Online ta ruwaito. Shugaba Tinubu ya ce gwamnati za ta ƙara ƙaimi wajen Samar da wani tsari na musamman na ceto yara da sauran al’umma masu rauni da aka yi garkuwa da su, musamman waɗanda aka sace a jihohin Oyo da Borno kwanan nan. “A yayin da muke bikin wannan rana ta musamman, wa

Rahoton Amurka ta ce masu tayar da ƙayar baya 30,000 ne ke haddasa tabarbarewar tsaro a Najeriya

Wani rahoto daga Hukumar Kula da ‘Yancin Addini ta Amurka (USCIRF) ya yi zargin cewa akwai kusan masu ɗauke da makamai 30,000 da ke gudanar da hare-hare a sassan Najeriya, lamarin da ke ƙara rura wutar rashin tsaro musamman a yankin Middle Belt da kudancin ƙasar. Rahoton na watan Mayun 2026 mai taken “Masu Take ‘Yancin Addini da Ba na Gwamnati ba a Nijeriya: Mayaƙan Fulani” ya bayyana cewa mayaƙan na aiki ne cikin ƙananan ƙungiyoyi masu mutum tsakanin 10 zuwa 1,000. A cewar rahoton, hare-haren da suke kaiwa sun yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane, da tarwatsa al’ummomi daga muhallansu, tare da

Kashim Shettima ya roki Yan Najeriya da su cigaba da hakuri da gwamnatin Shugaba Tinubu

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ya sake jaddada kudirin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na rage wa ‘yan Najeriya radadin matsin tattalin arzikin da suke fuskanta. Shettima ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Laraba yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan gudanar da sallar Eid-el-Kabir a filin Idi na Ramat Square da ke Maidugurin Jihar Brono Mataimakin Shugaban Kasar, wanda ya bayyana cewa tsadar rayuwa ta karu a duniya baki daya, ya roki ‘yan Najeriya da su ci gaba da hakuri da gwamnati.

Zamu yi duk mai yuwa wajen dawo da malamai da Dalibai da aka sace a Oyo - seyi Makinde

Gwamnan Jihar Oyo Seyi Makinde, ya tabbatarwa iyaye da al'ummar juharsa cewa Gwamnatinsa za ta yi duk mai yuwa wajen ganin ta kubutar da dukkan yara da malamai da aka yi garkuwa da su a ranar 16 ga watan Mayu a Karamar Hukumar Oriire, kuma za a dawo da su gida lafiya ga iyalansu. Makinde ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a gidansa da ke Ikolaba yayin da yake karbar bakuncin mataimakinsa Bayo Lawal, da sauran masu mukaman gwamnati Musulmai a Jihar Oyo cikin shagulgulan salah

Shugaban Tunisia shugaba Kais Saied ya yi afuwa ga ɗan majalisar dokokin ƙasar da aka yankewa hukuncin ɗaurin watanni takwas Sabida Yana sukarsa

Afuwar da shugaba Kais Saied ya yi masa na cikin shagulgulan sallar layya da ake gudanarwa a ƙasar a yau Laraba. A watan Faburairu dai aka yankewa Saidani hukuncin zaman gidan yari na watanni 8, bayan da ya wallafa wani rubutu da yayi kan shugaban ƙasar a lokacin da ya ziyarci wani yankin da aka samu ambaliyan ruwa, inda ya bayyana shi a matsayin babban kwamandan duba gari. Shi dai Saidani ya kasance ya kasance mai goyon bayan yadda gwamnatin Saied musamman yadda ta ke kulle ƴan adawa, sai dai a baya-bayan nan anga yadda shima ya ke sukar gwamnatin.

EFCC ta mika sale Mamman gidan gyaran Hali na kuje dake Abuja

Hukumar EFFC Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa a Nijeriya ta mika tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, zuwa Gidan Gyaran Hali na Kuje da ke Abuja domin fara zaman hukuncin daurin shekaru 75 da kotu ta yanke masa. Hakan ya biyo bayan umarnin da Mai Shari’a James Omotosho na Babbar Kotun Tarayya da ke Maitama, Abuja, ya bayar a ranar Talata, bayan gabatar da Mamman a gaban kotun da EFCC ta yi. DCL Hausa ta ruwaito cewa kotun ta kuma saurari bukatar EFCC na kwace wasu karin kadarori guda biyar da ake zargin suna da alaka da Mamman, ciki har da gidaje da otel-otel da ke Abuja da Kaduna.

Tinubu ya gana da wasu gwamnoni a Legas bayan nasarar da ya yi a zaɓen fidda gwani

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya karɓi baƙuncin tsohon shugaban majalisar dattawa, Pius Anyim, a gidansa da ke Ikoyi a jihar Legas bayan nasarar da ya samu a zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na jam’iyyar APC. Jaridar Punch ta rawaito cewa Anyim, wanda shi ne shugaban kwamitin zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, ya kai ziyarar ne kwanaki biyu bayan bayyana Tinubu a matsayin ɗan takarar jam’iyyar a zaɓen shekarar 2027. Kazalika Tinubu ya kuma gana da gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, da kuma gwamnan jihar Cross River, Bassey Otu.