AMMASCO RADIO NEWSROOM

Labarai

Mafi ƙarancin albashi na iya haura N100,000 yayin da gwamnoni ke nazari

Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) kuma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bayyana cewa gwamnoni na duba yiwuwar ƙara mafi ƙarancin albashin ƙasa zuwa Naira 100,000. A cewar rahoton da jaridar Punch ta wallafa, AbdulRazaq ya bayyana hakan ne ta cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya danganta matakin da hauhawar farashi, tsadar rayuwa da kuma matsin tattalin arziƙin da ma’aikata ke fuskanta. Ya ce gwamnatocin jihohi na ci gaba da tattaunawa da gwamnatin tarayya da kuma ƙungiyoyin ƙwadago domin samar da matsaya kan sabon tsarin albashi wanda zai taimak

Cibiyar gas ta South Pars ta janyo wa Iran asarar dala biliyan huɗu

Wani ɗan majalisar dokokin Iran, Jafar Pourkabagani, ya bayyana cewa ƙasar ta yi asarar da ta kai kusan dala biliyan huɗu a filin gas na South Pars sakamakon hare-haren da suka afku yayin rikicin baya-bayan nan. A cewarsa, wannan ƙiyasin ya samo asali ne daga binciken haɗin gwiwa da ƙwararru da masana daga Jami’ar Kimiyya da Fasaha suka gudanar. Ya ƙara da cewa raguwar ayyukan da aka samu a filin na haifar da asarar kusan dala miliyan biyu a kowace rana. Rahotanni sun nuna cewa a lokacin rikicin, Amurka da Isra’ila sun kai hare-hare kan wasu wurare a filin South Pars, wanda ake ɗauka a matsayi

Tsohon kakakin sojoji ya faɗa hannun ƴanbindiga a Katsina

Ana zargin wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Sojin Najeriya, Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, tare da matarsa a Jihar Katsina. Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar a yankin Matazu lokacin da tsohon jami'in sojan da matarsa ke kan hanyarsu ta zuwa birnin Katsina. Maharan sun tare motar da suke ciki tare da yin awon gaba da su zuwa wani wuri da ba a bayyana ba. Wata majiya ta tsaro ta bayyana cewa direban motar ya samu raunukan harbin bindiga yayin harin, amma ya samu nasarar tserewa daga hannun maharan. Har zuwa lokacin haɗa wannan r

Gwamna Makinde ya nuna Bimbo Adekanmbi a matsayin wanda yake so ya gaje shi a Oyo

Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana Bimbo Adekanmbi a matsayin wanda yake fatan zai gaje shi a kujerar gwamnan jihar a zaben shekarar 2027. Makinde ya bayyana hakan ne yayin taron gangamin haɗin gwiwa na jam’iyyun PDP da APM da aka gudanar a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, inda aka kuma kaddamar da Adekanmbi a matsayin ɗan takarar gwamna na bai ɗaya na jam’iyyar APM. Gwamnan ya ce al’ummar jihar Oyo sun amfana da tsare-tsaren gwamnatinsa na “Omituntun 1.0” da “Omituntun 2.0”, yana mai bayyana cewa yanzu lokaci ya yi na aiwatar da “Omituntun 3.0”. Haka kuma, Makinde ya shawarci Adekanm

Dakta Dahir Hashim ya yaba wa Gwamna Abba kan nuna hikima a batun fitar da ƴan takarar APC

Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na Jihar Kano, Dakta Dahir M. Hashim, ya yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa abin da ya bayyana a matsayin nuna kwarewa, gogewa da hikima wajen tafiyar da batun fitar da ƴan takarar jam’iyyar APC a jihar. A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, Dakta Dahir Hashim ya taya gwamnan murnar nasarar gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar cikin lumana a fadin jihar Kano, yana mai cewa tsarin ya gudana cikin natsuwa da fahimtar juna tsakanin masu ruwa da tsaki. Ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna ƙwarewar siyasa ta hanyar haɗa k

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya zai kai ziyara gabashin Congo saboda Ebola

Ziyarar Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus na nuna muhimmancin da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ke bai wa yaƙi da cutar Ebola a yankunan da suka fi fuskantar barazanar barkewar annobar. Wannan ita ce karo na 17 da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo ke fuskantar barkewar cutar Ebola, lamarin da ke ci gaba da jefa fargaba a tsakanin al'umma da hukumomin lafiya. Alƙaluman baya-bayan nan sun nuna cewa an samu kusan mutum 1,000 da ake zargin sun kamu da cutar, yayin da sama da mutum 220 suka rasa rayukansu sakamakon annobar. Lardin Ituri, wanda ya kasance ɗaya daga cikin wuraren da cutar ta fi kamari,

PSG ko Arsenal, wa zai lashe kofin Turai?

Babu tabbataccen wanda zai lashe kofin Champions League har sai an buga wasan ƙarshe, amma PSG da Arsenal duka suna da dalilan da ke sa magoya bayansu ke fatan samun nasara. PSG na shiga wasan da ƙwarin gwiwa bayan ta nuna bajinta a duk matakan gasar, tare da samun fa'idar hutun ƴan wasa da kuma zurfin tawaga. Koci Luis Enrique ya samu damar hutar da wasu daga cikin manyan ƴan wasansa a wasannin Ligue 1, lamarin da zai iya taimaka wa ƙungiyar ta kasance cikin ƙoshin lafiya a wasan ƙarshe. A gefe guda kuma, Arsenal ta nuna ƙwazo da daidaito a kakar bana ƙarƙashin jagorancin Mikel Arteta. Ƙungiy

Dan wasan baya na Newcastle United, Kieran Trippier, na dab da komawa Wolverhampton Wanderers

Dan wasan baya na Newcastle United, Kieran Trippier, na dab da komawa Wolverhampton Wanderers bayan bangarorin biyu sun kai matakin karshe na tattaunawar cinikin. Rahotanni sun nuna cewa Wolverhampton na son kara karfin bangaren tsaronta da kwarewar Trippier, wanda ya taka muhimmiyar rawa a Newcastle tun bayan zuwansa daga Atletico Madrid a shekarar 2022. Ana sa ran za a kammala yarjejeniyar cikin kwanaki masu zuwa idan har aka cimma matsaya kan sharuddan karshe na kwantiragin dan wasan. Trippier, mai shekaru 35, ya taimaka wa Newcastle wajen samun gurbi a gasar zakarun Turai tare da kasancewa

Real Madrid ta sake naɗa Mourinho a matsayin koci kan yarjejeniyar shekaru uku

Jose Mourinho ya amince da kwantiragin shekara uku domin komawa matsayin kocin Real Madrid, sai dai ba za a gabatar da shi a hukumance ba har sai bayan zaɓen shugaban ƙungiyar da za a gudanar a ranar 7 ga watan Yuni. Rahotanni sun nuna cewa kwantiragin Mourinho zai fara aiki ne kawai idan shugaban ƙungiyar na yanzu, Florentino Perez, ya sake samun nasara a zaɓen. Perez ya sanar da gudanar da sabon zaɓen ne a wani taron manema labarai da aka yi a farkon watan nan, inda ya zargi wasu kafafen yaɗa labarai da kuma hukumar La Liga da gudanar da abin da ya kira “yaƙin tsari” a kansa. Perez mai sheka

Saudiyya ta sanar da kammala Hajjin 2026 cikin nasara, alhazai miliyan 1.7 sun sauke ibada

Yarima Saud bin Mishal bin Abdulaziz, mataimakin gwamnan yankin Makkah kuma mataimakin shugaban Kwamitin Dindindin na Hajj da Umrah, ya bayyana cewa kakar Hajjin 2026/1447 AH ta kasance mai nasara, sakamakon ingantaccen tsarin tsaro, tsari da ayyuka masu haɗaka da suka bai wa mahajjata damar gudanar da ibadarsu cikin natsuwa da aminci. Ya bayyana hakan ne a wata sanarwa ta talabijin a daren kammala aikin Hajjin bana, inda ya ce Saudiyya ta kammala kakar Hajji cikin nasara, tare da tabbatar da sauƙi da kwanciyar hankali ga mahajjata a duk matakan ibada. Yarima Saud ya ƙara da cewa wannan nasara

Gwamnati na nazarin kakaba takunkumin tafiye-tafiye saboda barazanar Ebola

Gwamnatin Tarayyar Najeriya na duba yiwuwar kakaba takunkumin tafiye-tafiye kan jiragen da ke fitowa daga ƙasashen da ke fama da cutar Ebola, a wani ɓangare na sabbin matakan kare ƙasar daga yaduwar cutar. Shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila ne ya bayyana hakan yayin wani taro na musamman da aka gudanar a Legas domin nazari kan shirin Najeriya na tunkarar Ebola. Ya ce ana kuma nazarin yiwuwar maye gurbin takunkumin tafiye-tafiye da tsarin keɓe fasinjojin da ke nuna alamun kamuwa da cutar. Taron ya samu halartar manyan jami’ai da suka haɗa da Darakta Janar na NCDC, Jide I

‘Aminu Abdussalam shi ne ɗan takararmu na gwamna a 2027’ — Kwankwaso

Jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo a matsayin ɗan takarar gwamnan jam’iyyar NDC a zaɓen shekarar 2027. Kwankwaso ya bayyana hakan ne cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya kuma sanar da cewa Dakta Nasiru Yusuf Gawuna zai nemi kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya. Ya ce an ɗauki matakin ne bisa la’akari da gaskiya, biyayya da ƙwarewa, waɗanda ya bayyana a matsayin ginshiƙan haɗin kai da ci gaban Kwankwasiyya. Sanarwar na zuwa ne bayan kwanaki ana gudanar da tattaunawa tsakanin mambobin Kwankwasiyya da wasu manyan ƴan siyasa kan shi

An cafke ɗalibai takwas kan zargin hannu a gobarar makaranta a Kenya

Hukumomi a Kenya sun kama ɗalibai takwas bisa zargin suna da hannu a mummunar gobarar da ta tashi a wata makarantar kwana ta ƴanmata da ke Gilgil, wadda ta yi sanadin mutuwar ɗalibai 16. Sashen binciken manyan laifuka na ƙasar ya tabbatar da kamen, yana mai cewa binciken farko-farko ya nuna akwai alamun cewa an tayar da gobarar da gangan. Gobarar ta tashi ne a ɗakin kwanan ɗalibai inda ta lalata wani sashe na ginin mai hawa biyu. Hukumomi sun ce ƙwararrun masu bincike na ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin tashin gobarar. Rahotanni sun bayyana cewa jami’an bincike sun riga sun

‘Mun kafa tubalin warware matsalolin Najeriya’ — Tinubu

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ce gwamnatinsa ta shimfiɗa tubalin magance matsalolin da suka daɗe suna addabar ƙasar, duk da cewa har yanzu ba a kai ga cimma dukkan manufofin da aka sa gaba ba. A jawabinsa na cikar shekara uku a mulki, Tinubu ya bayyana cewa ya fahimci irin ƙalubale da sadaukarwar da iyalai suka fuskanta a cikin shekarun baya-bayan nan, tare da nuna ƙwarin gwiwar cewa Najeriya na kan hanyar samun ci gaba. Shugaban ya jaddada cewa harkar tsaro na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta fi bai wa muhimmanci, yana mai cewa ana ci gaba da samun nasarori duk da ƙalub

WHO ta nemi ƙarin tallafi domin yaƙi da cutar Ebola a Congo

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya nemi ƙarin kuɗaɗe domin taimaka wa Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo wajen yaƙi da ɓarkewar cutar Ebola. Da yake jawabi a Kinshasa, Tedros ya bayyana cewa zuwa yanzu an samu kusan kashi ɗaya bisa uku ne kawai na tallafin da ake buƙata domin ci gaba da ayyukan daƙile cutar. A nasa ɓangaren, United States ta yi alƙawarin bayar da ƙarin dala miliyan 80 domin tallafa wa matakan yaƙi da cutar a Congo da kuma Uganda, inda aka tabbatar da kamuwar mutum bakwai da Ebola. Hukumar WHO ta kuma sanar da cewa an sallami mutum na farko da y

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta yaba wa al’umma, gwamnatin jihar da hukumomin tsaro bisa yadda aka gudanar da bukukuwan Eid El Kabir na shekarar 2026.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, rundunar ta miƙa godiyarta ga gwamnatin jihar Kano bisa goyon baya da haɗin kai da ta bayar ga jami’an tsaro a lokacin bukukuwan Sallah. Sanarwar ta kuma yaba wa sarakunan gargajiya a faɗin jihar bisa irin gudunmawar da suka bayar wajen tabbatar da zaman lafiya da bin doka da oda. Rundunar ta jinjinawa al’ummar jihar Kano saboda addu’o’i, goyon baya da kuma bin shawarwarin tsaro da aka bayar, tana mai cewa hakan ya nuna haɗin kai da jajircewar jama’ar jihar wajen tabbatar da zaman lafiya. Haka kuma, rundunar ta yab

Dalilin daya sa Hukumar Tarayyar Turai ba za ta taɓa zama mai shiga tsakani ko yin sulhu tsakanin Rasha da Ukraine ba

Babban jami'in manufofin kasashen waje na kungiyar, Kaja Kallas, shi ne ya bayyana haka bayan taron ministocin harkokin wajen ƙungiyar da aka yi a ƙasar Cyprus. Kallas ya ce ƙasashen Turai ba za su iya zama a tsaka-tsaki ba saboda sun riga sun zaɓi ɓangare guda, wato suna goyon bayan Ukraine ɗari bisa ɗari. EU ta bayyana cewa ƙoƙarinta ba zai maye gurbin rawar da Amurka ke takawa ba a shirin samar da zaman lafiya tsakanin ƙasashen biyu ba. Maimakon sulhu, EU na shirin ci gaba da amfani da ƙarfinta wajen sanya sabbin takunkumai don tilasta wa Rasha amincewa da ƙudurorin zaman lafiya. Wannan j

Ministan tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta samu maki 70 cikin 100 kan kokarin magance matsalar tsaro a kasar nan.

Ministan tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta samu maki 70 cikin 100 kan kokarin da take yi wajen magance matsalar tsaro a kasar nan. Christopher Musa ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na ARISE, domin nazarin shekaru uku da gwamnatin Tinubu ta yi tana mulki, kamar yadda jaridar Punch ta rawaito. A cewarsa, duk da cewa har yanzu ana fama da wasu matsalolin sace mutane da hare-haren 'yan bindiga, amma matakin ta'addanci a Nijeriya ya ragu sosai idan aka kwatanta da shekarun baya. Ministan ya ce babu wata k

Tinubu ya ɗora mana ɗan takara

Siyasar Jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Najeriya ana kallonta a matsayin siyasa mai cike da ƙalubale da ke yawan bai wa gwamnoni kunya, inda ake ganin tsarin “siyasar ubangida” na da tasiri wajen sauya akalar abubuwa ba tare da hasashe ba. A irin wannan yanayi, ana zargin cewa tsarin siyasar jihar ba ya barin ‘yan takara su tabbatar da makomarsu cikin sauƙi, lamarin da ya sa a wannan karo manyan ‘yan takarar gwamnan jihar suka kadu da sakamakon zaɓen fidda gwani da aka gudanar. Daga cikin masu neman tikitin takarar akwai Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar, Sanata mai

Gwamnati ta gargadi mazauna yankin Mokwa su fice saboda barazanar sake aukuwar ambaliya

Gwamnatin ƙaramar hukumar Mokwa a jihar Neja ta umarci mazauna yankunan da ambaliya ta shafa a bara da su fice daga wuraren saboda barazanar sake aukuwar ambaliya. A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran shugaban ƙaramar hukumar, Haruna Saidu Kinbokun ya fitar ranar Alhamis, ya bayyana cewa an samu taruwar ruwa a yankin sakamakon toshewar hanyar ruwa da ake zargin aikin sake gina layin dogo ya haddasa. Sanarwar ta ce binciken farko ya nuna cewa aikin da kamfanin CPN ke yi ya kawo cikas ga hanyar ruwa na ɗan lokaci, lamarin da ya janyo kwararar ruwa mai yawa da ka iya haifar da sabon amb