AMMASCO RADIO NEWSROOM

Labarai

Obasanjo ya bukaci ’yan Najeriya su rika yin gwaje-gwajen lafiya akai-akai domin gano cututtuka tun da wuri don daukar mataki

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya bukaci ’yan Najeriya su rika yin gwaje-gwajen lafiya akai-akai domin gano cututtuka tun da wuri tare da samun damar kula da su yadda ya kamata. Ya ce hakan na da matukar muhimmanci musamman wajen yaki da cututtuka kamar su kansa da ciwon sukari. Obasanjo ya bayyana hakan ne a birnin Abeokuta yayin kaddamar da wani shiri da aka shirya domin wayar da kan jama’a game da cutar kansar mafitsara. Da yake bayar da misali daga rayuwarsa, Obasanjo ya bayyana cewa ya shafe sama da shekaru 40 yana fama da ciwon sukari amma yana sarrafa shi ta hanyar motsa jiki

Gwamnatin Jihar Legas ta ƙara tsaurara matakan kariya domin hana shigowar cutar Ebola Najeriya, bayan sake ɓarkewar cutar a wasu ƙasashen Gabashin Afirka.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Farfesa Akin Abayomi, ya jagoranci wata tawaga ta musamman domin duba shirye-shiryen kariya a Filin Jirgin Sama na Murtala Mohammed da ke Legas. Matakin ya biyo bayan rahotannin sake ɓarkewar cutar Ebola a ƙasashen Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo da Uganda. Yayin ziyarar, tawagar ta tantance tsarin kula da fasinjoji, hanyoyin dakile yaduwar cututtuka, shirye-shiryen gaggawa da kuma matakan haɗin gwiwa tsakanin hukumomin lafiya da na filayen jiragen sama. Farfesa Abayomi ya bayyana cewa Filin Jirgin Sama na Murtala Mohammed shi ne mafi muhimmancin ƙofar shiga Naje

Amurka ta ware dala miliyan 3.5 domin sa ido kan tashe-tashen hankula masu alaka da addini a Najeriya

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar da ware dala miliyan 3.5 (kimanin Naira biliyan 5 ) domin tallafawa shirye-shiryen tattara bayanai da rahotanni kan take hakkin ‘yancin addini da tashe-tashen hankula masu alaka da addini a Najeriya. Shirin, wanda Ofishin Kula da ‘Yancin Addini na Kasa da Kasa (IRF) ya sanar a ranar 22 ga Mayu, 2026, na da nufin karfafa ayyukan kungiyoyi da cibiyoyi da ke sa ido tare da rubuta bayanai kan hare-haren da suka shafi addini da akida a fadin Najeriya. A cewar sanarwar, za a gudanar da aikin na tsawon watanni 24 zuwa 48 , kuma za a bai wa wata kungiya ko huk

NLC ta yi watsi da tayin mafi karancin albashi na N100,000, ta bukaci Naira miliyan 1

Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta yi watsi da shawarar biyan mafi karancin albashi na N100,000 , inda ta bayyana cewa adadin bai dace da halin matsin tattalin arzikin da ma’aikata ke ciki ba. Mai magana da yawun NLC, Benson Upah , ya bayyana haka a wata hira da aka yi da shi ranar Lahadi, bayan shugaban Kungiyar Gwamnonin Jihohi (NGF) kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq , ya bayyana cewa gwamnoni na nazarin yiwuwar karin mafi karancin albashi zuwa N100,000. AbdulRazaq ya ce gwamnoni na tattaunawa da gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago domin samar da tsarin albashi da zai k

Faransa ta tare jirgin dakon mai da ake zargin yana da alaka da Rasha

Gwamnatin Faransa ta sanar a ranar Litinin cewa ta tare wani jirgin dakon mai da ake zargin yana da alaka da Rasha a Tekun Atlantika, a wani sabon mataki na yaki da jiragen da ake zargin suna taimakawa Moscow wajen kauce wa takunkuman kasashen yamma. Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya bayyana cewa an kama jirgin mai suna Tagor a safiyar Lahadi a ruwan kasa da kasa tare da hadin gwiwar Birtaniya da wasu abokan hulda. Mahukuntan Faransa sun ce jirgin ya taso ne daga birnin Murmansk da ke arewa maso yammacin Rasha, kuma yana kan hanyarsa ta zuwa garin Limbe da ke kasar Kamaru lokacin da aka ta

Sace Dalibai a Oyo: NUT ta fara yajin aiki, Tinubu ya amince da daukar masu gadin dazuka 1,000

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da daukar masu gadin dazuka 1,000 a jihar Oyo domin karfafa tsaro da yaki da masu garkuwa da mutane. Haka kuma, shugaban kasar ya bayar da umarnin tura rundunar tsaro ta musamman mai kwarewa wajen gudanar da ayyukan ceto domin kara kaimi wajen kubutar da dalibai da malamai da aka sace daga makarantu uku a karamar hukumar Oriire. Wannan na zuwa ne yayin da Kungiyar Malaman Najeriya (NUT) ta ayyana yajin aiki na sai baba-ta-gani ga dukkan malamai a makarantun firamare da sakandare na jihar Oyo, tare da sanar da shirinta na gudanar da gangamin nuna goyon

Tinubu ya yi jimamin malamin da aka kashe a Oyo, ya yi alkawarin ceto dalibai da malamai da aka sace

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhininsa ga iyalan dalibai da malamai da aka sace a karamar hukumar Oriire ta jihar Oyo, yana mai cewa babu wani yaro da ya kamata a dauke shi daga cikin aminci da kariyar da makaranta ke bayarwa. A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin, shugaban kasar ya ce yana tare da iyalan wadanda abin ya shafa cikin wannan lokaci na damuwa da tashin hankali bayan harin da aka kai garuruwan Esiele da Yawota. Tinubu ya ce babu wani yaro da ya kamata a sace shi daga aji, kuma babu wani uba ko uwa da ya kamata ya shiga irin wannan azaba da damuwa. Shugaban

Babu kanshin gaskiya kan cewar zan koma PDP don zama mataimakin Jonathan- Kauran Bauchi

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya musanta rahotannin da ke cewa zai fice daga jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM) domin zama mataimakin tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, a zaɓen 2027 ƙarƙashin wani ɓangaren PDP. Mohammed ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce hankalinsa yana kan neman kujerar Sanatan Bauchi ta Kudu a ƙarƙashin jam’iyyar APM a zaɓen 2027. Ya buƙaci jama’a da su yi watsi da duk wasu rahotannin da ke nuna yana da wata manufa ta siyasa daban, yana mai cewa irin waɗannan rahotanni hasashe ne marasa tushe. Rahotannin sun biyo bayan

Gwamnatin Tinubu zata tura jami'an tsaro Dubu Daya 1,000 daji don ceto daliban Oyo

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya amince tare da bada umarnin baza jami'an tsaron gandun daji guda 1,000 domin ceto dalibai da malamai da aka yi garkuwa da su a jihar Oyo Wannan na cikin wata sanarwa da mai bai wa Shugaban Shawara kan yaɗa labarai Bayo Onanuga ya fitar. Onanuga yace wata babbar tawaga ta gwamnatin tarayya ta isar da umarnin Shugaban ga shugabannin al’umma da ‘yan majalisu yayin wata ziyara da ta kai ƙauyukan Esiele da Yawota da ke ƙaramar hukumar Oriire a ranar 31 ga Mayu, 2026.

Iran: Ba za mu amince da yarjejeniya da Amurka ba sai an kare hakkin al’ummarmu

Babban mai jagorantar tattaunawar Iran, Mohammad Ghalibaf, ya bayyana cewa kasarsa ba za ta amince da wata yarjejeniya da Amurka ba matukar ba ta tabbatar da kare hakkin al’ummar Iran ba. A wani jawabi da aka watsa a gidan talabijin na gwamnatin Iran ranar Lahadi, Ghalibaf ya ce gwamnati ba za ta sanya hannu kan wata yarjejeniya ba har sai ta gamsu cewa an mutunta da kuma kare muradun ‘yan Iran. Ya kara da cewa masu tattaunawar Iran ba sa yarda da kalamai ko alkawurran bangaren da suke tattaunawa da shi, yana mai jaddada cewa za su tsaya tsayin daka wajen kare bukatun kasarsu. Kalaman nasa na

Gwamnatin Iran ta yi alƙawarin kammala gyaran gidajen da yaƙi ya lalata zuwa Yuli

Mai magana da yawun Gwamnatin Birnin Tehran, Abdul Motahar Mohammadkhani, ya bayyana cewa ana sa ran kammala dukkan ayyukan da suka shafi sake gina da gyaran gidajen da yaƙin baya-bayan nan ya lalata kafin ƙarshen watan Yuli. Ya ce an samu ci gaba da ya kai kusan kashi 40 cikin 100 a aikin sake gina gidajen da lalacewarsu ta yi muni har ta kai ga buƙatar rushe su gaba ɗaya tare da sake ginawa. A cewarsa, gidaje kusan 51,000 ne suka samu matsaloli daban-daban sakamakon yaƙin, lamarin da ya sa gwamnatin birnin ta ɗauki matakan gaggawa domin magance matsalar. Mohammadkhani ya ƙara da cewa aikin g

ASBON ta ce matsakaitan sana’o’i miliyan biyu ne suka rufe harkokinsu cikin shekaru uku na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Kungiyar Masu Kananan sana’oi ta Najeriya (ASBON) ta bayyana cewa kimanin kananan da matsakaitan sana’o’i miliyan biyu ne suka rufe harkokinsu cikin shekaru uku na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, duk da alkawarin tallafin naira biliyan 200 da gwamnatin tarayya ta yi domin rage radadin sauye-sauyen tattalin arziki. ‎ ‎Kungiyar ta danganta rugujewar kasuwancin da cire tallafin man fetur, sauye-sauyen tsarin canjin kudaden kasashen waje, tashin farashin kayayyaki, karuwar kudin gudanar da kasuwanci da kuma raguwar karfin sayen jama’a. ‎ ‎A watan Yulin 2023, Shugaba Tinubu ya sanar da wani sh

Abba ya ce gwamnatinsa ta cika kashi 90 cikin 100 na alƙawuran da ta ɗauka

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta aiwatar da kusan kashi 90 cikin 100 na alƙawuran da ta ɗauka wa al’ummar jihar tun bayan hawanta mulki. Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi bakuncin Sarkin Rano, Ambasada Muhammad Isa Umaru, wanda ya kai masa ziyarar Sallah a Fadar Gwamnatin Kano ranar Asabar. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Gwamna Yusuf ya ce gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen aiwatar da shirye-shiryen ci gaba da manufofin da suka shafi rayuwar jama'a kai tsaye. Ya ce an samu gagarumin ci gaba

Gwamnatin Kano za ta matarsa Dutsen Dala da Goron cibiyoyin bincike na tarih

Gwamnatin Jihar Kano ta fara shirin mayar da dutsen Dala da Goron Dutse cibiyoyin binciken tarihi da yawon bude ido domin bunkasa harkokin tarihi da al’adun gargajiya a jihar. Shugaban Hukumar Tarihi da Al’adu ta Jihar Kano, Arc. Ahmad Abba Yusuf ne ya bayyana hakan a sakonsa na cikar Gwamna Abba Kabir Yusuf shekaru uku a mulki. Ya bayyana cewa shirin na daga cikin matakan da hukumar ke dauka na alkintawa da bunkasa wuraren tarihi masu muhimmanci a Kano tare da kara haɓaka harkokin yawon bude ido. Shugaban hukumar ya kuma bayyana cewa an gyara wuraren tarihi yayin da ake ci gaba da aikin sake

NDC ta tsayar da Peter Obi da Kwankwaso takara a zaɓen 2027

Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ƙarƙashin jagorancin Sanata Seriake Dickson ta ayyana tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027. An sanar da Obi a matsayin ɗan takarar jam’iyyar ne a yayin babban taron NDC da aka gudanar a Abuja ranar Asabar. Bayan karɓar tutar jam’iyyar, Obi ya bayyana tsohon gwamnan Jihar Kano, Musa Kwankwaso, a matsayin abokin takararsa. Fitowar Obi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC ya sake ƙara zafi a fafatawar siyasar 2027 tsakanin manyan 'yan takara daga manyan jam’iyyun ƙasar. Matakin n

PDP ta bayyana dalilin tsayar da Jonathan takarar shugaban ƙasa a 2027

Wani ɓangare na jam’iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Tanimu Turaki ya bayyana dalilan da suka sa ya ayyana tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, a matsayin ɗan takararsa na shugaban ƙasa a zaɓen 2027. Jam’iyyar ta ce Jonathan ne ya fi cancanta ya jagoranci Najeriya a wannan lokaci, tana mai nuni da nasarorin da aka samu a lokacin mulkinsa, da jajircewarsa wajen kare dimokuraɗiyya da kuma yadda ya gudanar da mulki cikin kwanciyar hankali. Da yake jawabi bayan wani taron masu ruwa da tsaki, shugabannin ɓangaren sun bayyana cewa mulkin Jonathan ya kasance lokaci na ci gaban tattalin arziki, haɗi

Gen Christopher Musa mai ritaya, ya ce Gwamnati zata cigaba da yin duk mai yuwa wajen ganin an ceto mutanen da a akayi garkuwa da su a Najeriya

Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro za su ci gaba da yin duk mai yiwuwa domin ganin an ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a sassan kasar nan. ‎Musa ya bayyana hakan ne jiya Asabar bayan da aka karrama shi da lambar yabo ta Southern Kaduna Grand Commander a wajen bikin al'adun Kudancin Kaduna na shekarar 2026. ‎Ya amince cewa har yanzu akwai wasu mutane da ke hannun masu garkuwa da mutane, yana mai jaddada cewa jami'an tsaro ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da an kubutar da su. ‎Ministan ya ce hadi

AMNESTY ta horas da matasa 30 Kan Yadda zasu gano tare da bayar da rohoton take hakkin Dan Adam

‎Kungiyar kare hakkin dan adama ta Amnesty International, ta horas da matasa 30 a jihar Cross River kan hanyoyin kare hakkokin dan Adam da kuma yadda za su gano tare da bayar da rahoton take hakki a cikin al'ummar su. ‎ ‎An gudanar da horaswar ne na tsawon kwanaki biyu karkashin wani shiri wanda Asusun Ofishin Jakadancin Jamus ya dauki nauyin tallafawa. ‎ ‎Shirin na da nufin samar da sabbin masu fafutukar kare hakkokin dan adama da za su iya tattara bayanai kan take hakki, neman tabbatar da adalci ga wadanda aka zalunta tare da hada kai da hukumomi domin magance matsalolin da ke addabar al'umm

Kasar china zata fara hukunta mutanen dake bayyana dukiyarsu a kafafen sada zumunta

Matakin ya biyo bayan yawaitar masu daukaka ko shuhura wato influencers dake bayyan dukuyar da suka mallaka a kafafen sada zumunta. Ƙasar na sa ido kan accounts da ke baje kolin motocin alfarma da manyan gidaje da tufafin masu tsada da kayan ado na zinariya da lu’ulu’u da jiragen sama masu zaman kansu, da kuma rayuwar da ta ta’allaka kan bautar kuɗi. Daga cikin shahararrun influencers da wannan mataki ya shafa ita ce Wang Hongquanxing, wadda aka fi sani a intanet da suna “Kim Kardashian ta China.” Tana da miliyoyin mabiya, kuma ta shahara ne saboda nuna tufafin alfarma da kayan ado masu tsada

Abin takaici ne yadda ake rasa rayuka a Kano — Gwarzo

Dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar NDC kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya soki Gwamna Abba Kabir Yusuf, inda ya zarge shi da yin sakaci wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar. A wata hira da ya yi da BBC Hausa, Kwamared Aminu Abdussalam ya bayyana cewa yanayin tsaro a Kano ya taɓarɓare fiye da kowane lokaci a tarihin baya-bayan nan. Ya ce a wasu ƙananan hukumomi irin su Tsanyawa, Shanono da Gwarzo, an samu hare-hare da suka yi sanadin kisan mutane da kuma kwashe dukiyoyi. Ya kuma yi zargin cewa har yanzu akwai wasu da ke tsare sama da watanni shida sakam