Malamai Sun Fito Zanga-Zanga a Najeriya Kan Sace Ɗalibai a Borno da Oyo
malamai a sassa daban-daban na Najeriya sun fito zanga-zanga a faɗin ƙasar, inda suke neman a gaggauta kuɓutar da ɗaliban da aka sace a jihohin Oyo da Borno. Zanga-zangar, wadda ƙungiyar malaman Najeriya (NUT) ta shirya, ta soma ne a ranar Litinin, inda jihohi da dama suka shiga ciki har da Borno, Kano, Legas, Akwa Ibom da Abuja, tare da bin sahun Oyo da Ogun da suka fara gudanar da ita tun farko. Ƙungiyar ta ce matakin nuna goyon baya ne ga takwarorinsu da kuma ɗaliban da ke hannun masu garkuwa, bayan jerin hare-hare kan makarantu da suka haifar da fargaba a tsakanin iyaye da malamai. A biran
