AMMASCO RADIO NEWSROOM

Labarai

Majalisar Dattawa Najeriya ta ci alwashin gaggauta Samar da matsaya Kan batun Yan sandan jihohi

Majalisar dattijan Najeriya ta yi alƙawarin gaggauta ɗaukar mataki da kuma samun matsaya kan batun ƴan sandan jihohi, a dai-dai lokacin da matsalolin ta’addanci ke ƙaruwa a sassan ƙasar. Shugaban kwamitin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na Majalisar Yemi Adaramodu ne ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai. A cewar sa lokaci yayi da ya kamata a kawo ƙarshen jan ƙafar da ake yi game da batun samar da ƴan sandan jihohi wanda zai taimaka wajen kawo ƙarshen wannan matsala, da kuma baiwa manoma damar ci gaba da harkokin su na noma. Kwanaki uku da suka gabata, Majalisar ta sanar da komaw

Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta haramta sare bishiyoyi ba bisa ka'ida ba a harabar ARTV dake kano

Gwamnatin Jihar Kano ta ba da umarnin dakatar da sare bishiyoyi ba tare da ka’ida ba a harabar gidan talabijin na jihar, Abubakar Rimi Television (ARTV), bayan wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta yana nuna yadda ake sare bishiyoyin. Kwamishinan yaɗaabarai da harkokin cikin gida na jihar, Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayar da umarnin yayin wata ziyara ta bazata da ya kai tashar a ranar Asabar. Ya ce sare bishiyoyin ya saɓa wa manufofin gwamnatin jihar na kare muhalli da yaƙi da sauyin yanayi, tare da gargadin cewa daga yanzu ba za a sare kowace bishiya a tashar ba sai an samu amince

Yan bindiga da suka yi garkuwa da Janar Abubakar rabe mai ritaya, sun bukaci a sako mutanensu uku Kafin sakinsa da matarsa

Manjo Janar Abubakar Rabe (mai ritaya) da matarsa, sun ruko Gwamnati ta kawo musu dauki daga hannun masu garkuwa da mutane. Koken nasu na cikin wani faifan bidiyo mai tsawon mintuna huɗu da daƙiƙa biyu da ya bazu a kafafen sada zumunta, inda aka ga tsohon janar din da matarsa tsaye suna isar da buƙatun masu garkuwa da Mutanen da suka yi garkuwa da su. Da take magana a cikin bidiyon, matar tsohon hafsan sojin ta bayyana cewa masu garkuwar sun buƙaci a saki mutum uku daga cikin membobinsu da suka bayyana sunayensu a matsayin Sani da Aminu da Nasiru. Masu garkuwar sun kuma buƙaci a mayar musu da

Iran ta zargi Amurka da hana tawagar ƙwallon ƙafarta halartar gasar cin kofin duniya ta 2026,

Iran ta zargi Amurka da hana wasu manyan jami’an tawagar ƙwallon ƙafarta shiga ƙasar, duk da amincewa da bai wa ‘yan wasa da wasu ma’aikatan tawagar bizar halartar Gasar Kofin Duniya ta 2026. Mahukuntan Iran sun ce an ƙi bai wa wasu jami’an gudanarwa da masu ba da shawara biza, lamarin da suka bayyana a matsayin katsalandan a harkokin wasanni saboda dalilai na siyasa. Sai dai gwamnatin Amurka ta ce ta bayar da biza ga ‘yan wasa da sauran ma’aikatan da ake buƙata domin halartar gasar, tana mai jaddada cewa ba za ta amince a yi amfani da tsarin gasar wajen shigar da mutanen da ake zargi da alaƙa

Iran Ta Yi Gargaɗin Rufe Mashigar Hormuz Gaba Ɗaya

Rundunar Juyin Juya Halin Iran (IRGC) ta yi barazanar rufe Mashigar Hormuz gaba ɗaya ga zirga-zirgar jiragen da ke jigilar mai da iskar gas, yayin da rikici tsakanin Iran da Amurka ke ci gaba da ƙamari a yankin Tekun Fasha. Hukumar ta ce za ta iya ɗaukar wannan mataki a matsayin martani idan Amurka ta ci gaba da abin da ta bayyana a matsayin ayyukan tsokana da kuma cin zarafin ikon ƙasar Iran. Barazanar ta zo ne bayan Amurka ta sanar da cewa dakarunta sun kai hare-hare kan wasu na’urorin sa ido da ke yankunan gaɓar teku na Goruk da Qeshm a Iran. A nata ɓangaren, rundunar IRGC ta ce ta harba ma

ICPC Ta Yi Watsi Da Buƙatar El-Rufai Ta Samun Kulawar Asibiti

Mai bai wa tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya zargi Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa Mai Zaman Kanta (ICPC) da hana El-Rufai samun kulawar lafiya yayin da yake tsare a hannunta. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Adekeye ya ce El-Rufai ya koka kan matsalar ƙaiƙayi da kumburi a idanunsa, lamarin da ya sa ya nemi a kai shi asibiti domin a duba lafiyarsa. Sai dai, a cewarsa, jami’an ICPC ba su amince da wannan buƙata ba. Adekeye ya bayyana cewa an kai El-Rufai wani asibitin ido a ranar 4 ga watan Yuni, amma daga bisani matsalar ida

Dangote Ya Ƙara Yawan Man Fetur Da Matatarsa Ke Tacewa A Rana

Matatar man fetur ta Dangote ta ƙara yawan ɗanyen man da take tacewa zuwa ganga 700,000 a rana, bayan wani gwajin da hukumomin da ke kula da harkokin matatun mai suka gudanar. Sabon adadin ya nuna cewa matatar ta ƙara ƙarfin aikinta daga ganga 650,000 zuwa 700,000 a kowace rana, lamarin da ke ƙara kusantar da ita ga burinta na zama ɗaya daga cikin manyan matatun mai a duniya. Mataimakin shugaban sashen mai da iskar gas na kamfanin Dangote, Devakumar Edwin, ya ce wannan ci gaban na cikin shirye-shiryen faɗaɗa ayyukan matatar domin ninka yawan ɗanyen man da take tacewa zuwa ganga miliyan 1.4 a r

Najeriya Ta Shirya Kwaso Ƴan Ƙasarta 1,000 Daga Afirka Ta Kudu Sakamakon Zargin Nuna Wariya

Gwamnatin Najeriya ta fara shirye-shiryen kwaso sama da ƴan ƙasarta 1,000 daga Afirka ta Kudu sakamakon ƙara yawaitar tashin-tashina da zargin nuna adawa ga baƙi a ƙasar. Matakin ya biyo bayan yadda Ghana ta fara dawo da wasu daga cikin ƴan ƙasarta bayan barazanar da zanga-zangar adawa da baƙi ta haifar. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, Kimiebi Ebienfa, ya ce an fara tantance ƴan Najeriya da suka nuna sha’awar komawa gida tun ranar Alhamis. “Muna sa ran fara kwashe kusan mutum 1,000, duk da cewa har yanzu ba mu da tabbataccen adadin waɗanda za a dawo da su,” in ji Ebienfa. Ya kuma c

Haryanzu ana cigaba tafka muhara kan matsalar tsaro a nakeriya musamman a yankin arewa maso gabashi da kuma arewa ta tsakiya sai kuma wasu jihohi dake yankin Kudu maso yammaci

Haryanzu ana cigaba tafka muhara kan matsalar tsaro a nakeriya musamman a yankin arewa maso gabashi da kuma arewa ta tsakiya sai kuma wasu jihohi dake yankin Kudu maso yammaci, musamman ma kan batun sace daliban karanta a Jihar Borno d akuma jihar oyo. Wani rahota da BBC hausa ta wallaf a shafinta a ranar 5 ga watan Yunin 2026, ya fito karara da sanda aka fara sace a dalibai a najeiya. Rahohon na BBC yace, ‘yan Najeriya sun fara samun labarin garkuwa ko kashewa dalibai ne a ranar 14 ga watan Afrilun 2014 sanda mayaƙan Boko Haram suka kai wani hari makarantar sakandaren mata da ke Chibok a jiha

MDD ta yi kira da a saki ɗalibai da malaman da aka sace a Oyo da Borno

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kira da a saki ɗalibai da malaman da aka sace a Oyo da Borno a hare-haren da suka faru a jihohin. Mai kula da ayyukan Majalisar Ɗinkin Duniya da na jin ƙai a kasar nan Mohamed Malick Fall, ne ya bayyana hakan a ganawarsa da tawagar Cibiyar Kula da Tsaron Makarantu ta Ƙasa a birnin tarraya Abuja, ƙarƙashin jagorancin Dakta Samuel Umanah. A cewarsa, bai kamata a ci gaba da zuba ido ana ganin matsalar tsaro na ci gaba da yiwa makarantu barazana a faɗin ƙasar nan, yana mai cewa irin waɗannan hare-hare na kawo cikas ga ilimi da kariyar yara. Ya ce makarantu ya kamata s

Yan bindiga sun sace sarkin Fulani da mata biyu masu goyo a jihar kwara

Wasu 'yan bindiga sun kai samame rugar sarkin Fulani da ke gefen garin Lafiyagi, shalkwatar karamar hukumar Edun ta jihar Kwara, inda suka sace dan sarkin Fulanin da matansa biyu masu dauke da goyon jarirai, ciki har da jaririn da bai kai wata guda da haihuwa ba. Rahotan da bbc ta wallafa a shafinta ya ce, maharan Sun kuma kashe wani mutumin garin, suka tafi da dansa shi ma. Maharan suna neman a ba su naira miliyan dari a matsayin kudin fansa, kafin su sako mutanen da suka sace. Al'amarin da ke kara nuna matsalar hare-haren 'yan bindiga dai ba ta bar hatta Fulani makiyaya da ke daji ba. A cewa

NAHCON ta yi kira ga alhazan Najeriya da su cike takardun bayanan Lafiyarsu kafin komowa gida

Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta bukaci dukkan alhazan kasar da ke shirin komawa gida bayan kammala aikin Hajjin bana da su tabbatar sun cike takardar bayanan lafiyarsu (Health Declaration Form) kafin tashinsu daga Saudiyya. Kamar yadda wata sanarwa ta bayyana, tuni aka raba takardar ga tawagogin likitocin jihohi tun daga tashin jirgin farko na alhazan bana. Hukumar ta ce ana bukatar tawagogin likitocin jihohi su taimaka wa alhazan da ba su iya karatu ko rubutu wajen cike takardar domin kauce wa jinkirin da ka iya tasowa a filayen jiragen sama da zarar sun isa Najeriya. Sanarwar ta ce a

An samu gagarumim cigaba wajen kafa Yan sandan jihohi a Najeriya, cewar fadar Shugaban kasa

Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa an samu gagarumin ci gaba wajen kafa rundunar ’yan sandan jihohi, inda ake sa ran za a gabatar da gyaran kundin tsarin mulki nan ba da jimawa ba domin ba da damar aiwatar da shirin. Talbijin na channels ya rawaito cewa, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila, ne ya bayyana hakan bayan wani taron tuntuba da aka gudanar a Abuja tsakanin bangaren zartarwa, Majalisar Dokoki ta Kasa da hukumomin tsaro. Ya ce tattaunawar kafa ’yan sandan jihohi ta fara ne bisa umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kuma yanzu an kai matakin duba gyaran kundin tsari

Kungiyar lauyoyi ta NBA ta nuna damuwa Kan tsananta sharudan beli da alkalai ke yi a Najeriya

Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) ta nuna damuwa kan yadda kotuna da jami’an tsaro ke sanya tsauraran sharuɗɗan beli da ke hana mutane da dama samun ‘yancinsu duk da an amince musu da beli. Shugaban NBA, Afam Osigwe, ya bayyana cewa yawan buƙatar masu tsaya wa wanda ake tuhuma su kasance manyan ma’aikatan gwamnati ko kuma mallakar kadarori masu tsada ya mayar da beli tamkar wata hanyar tsare mutum kafin a yanke masa hukunci. Ya ce hakan na tauye haƙƙin ‘yanci da kundin tsarin mulki ya tanada tare da karya ka’idar cewa wanda ake tuhuma ba shi da laifi har sai an same shi da laifi a kotu. Osigwe

Bankunan Nijeriya sun tara N209bn daga ladan kula da asusu cikin watanni ukun farkon shekarar 2026

Bankunan Nijeriya sun tara N209bn daga ladan kula da asusu cikin watanni ukun farkon shekarar 2026 Wasu sabbin bayanai da jaridar Punch ta tattaro sun nuna cewa bankunan Nijeriya sun tara Naira biliayan 209 daga kudaden da suke cira na kula da asusu (Account maintenance fees) cikin watanni uku na farkon shekarar 2026. Hakan na nuna cewa an samu kari kan Naira biliyan 183 da suka samu a watanni ukun farkon shekarar 2025.

Ƴanbindiga sun sace ɗalibai shida na Federal Polytechnic Kaura-Namoda a Zamfara

Wasu da ake zargin ƴanbindiga ne sun yi garkuwa da ɗalibai shida na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya (Federal Polytechnic) da ke Ƙauran-Namoda a jihar Zamfara, bayan sun kai hari gidan da ɗaliban ke zaune a wajen harabar makarantar. An ruwaito cewa lamarin ya faru ne a wani gida da ke gefen unguwar Low-Cost a garin Ƙauran-Namoda, inda maharan suka kutsa cikin gidan tare da yin awon gaba da daliban. Shugaban ƙaramar hukumar, Mannir Haidara Ƙaura, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa jami’an tsaro sun fara gudanar da ayyukan ceto domin tabbatar da kuɓutar da ɗaliban cikin ƙoshin la

Hukumar kula da wutar lantarki ta Nijeriya, ta fara aiwatar da sabbin dokokin da za su bai wa masu amfani da solar damar sayar da wutar lantarki

Hukumar kula da wutar lantarki ta Nijeriya, ta fara aiwatar da sabbin dokokin da za su bai wa masu amfani da solar damar sayar da wutar lantarkin da ta yi musu yawa ga kamfanonin rarraba lantarki. Jaridar punch ta bayyana cewa sabon tsarin zai ƙarfafa amfani da makamashi musamman na hasken rana, tare da bai wa masu zuba jari a fannin samar da wuta damar samun ƙarin riba. A ƙarƙashin sabon tsarin, masu amfani da solar za su fara amfani da wutar da suka samar domin bukatunsu, idan kuma an samu wutar fiye da abin da suke buƙata, za su iya tura wa ga kamfanin rarraba lantarki domin sayarwa.

Yan sanda a jihar kwara sun kama babban mai garkuwa da mutane

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kwara ta kama wani kasurgumin mai garkuwa da mutane tare da kwato makamai a Karamar Hukumar Baruten, Jami’ar Yaɗa Labaran Rundunar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi ne ya fitar da sanarwar Sanarwar ta ce ’yan sanda sun kama wasu mutane da ake zargi yayin wani samame da suka kai a yankin Tabida da ke Okuta, kafin daga bisani bincike ya kai ga gano Umar Abubakar wanda aka fi sani da Manti a matsayin wanda ake zargin yana jagorantar masu garkuwa da mutane a wasu yankuna. Rundunar ta ce bincike ya nuna wanda ake zargin na da hannu a hare-haren garkuwa da mutane a wasu sassan Kwa

Sunday Igboho ya yi barazanar bayyana sunayen ‘yan siyasar da ke da hannu a sace ɗalibai a Ƙaramar Hukumar Oriire ta Jihar Oyo.

Ɗan gwagwarmayar kafa ƙasar Yarabawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya yi barazanar bayyana sunayen ‘yan siyasar da ke da hannu a sace ɗalibai a Ƙaramar Hukumar Oriire ta Jihar Oyo. Igboho ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da sabbin shugabannin ƙungiyar ɗaliban Najeriya ta ƙasa (NANS) ƙarƙashin jagorancin Akinteye Bàbàtunde a gidansa da ke yankin Soka a Ibadan ranar Laraba. A cikin wani bidiyo da aka yada a kafafen sada zumunta, wanda Wisdom TV ta ɗauka, Igboho ya ce ya bayar da kansa domin korar ‘yan bindigar da suka aikata satar, amma gwamnatin jihar ta nuna rash

Kwamared Aminu Abduslamu Gwarzo ya yabawa Yan media na kwankwasiya Kan jajircewarsu

Gwarzo ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da wakilan kungiyar sama da 132 a Kano, inda ya ce gudummawar da suke bayarwa ta taka muhimmiyar rawa wajen yada ayyuka, nasarori da manufofin tafiyar Kwankwasiyya a kafafen zamani. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ibrahim Garba Shuaibu, ya fitar, Gwarzo ya ce yana matukar girmama mambobin kungiyar saboda jajircewarsu da kwarewarsu wajen gudanar da ayyukansu. Ya ce, “Muna da matukar girmamawa ga kungiyar masu yada manufofin Kwankwasiyya a kafafen sada zumunta, kuma suna sanya mu alfahari.” Dan takarar ya kuma bayyana cewa jagoran tafiy