AMMASCO RADIO NEWSROOM

Labarai

NDC ta ɗauki matakin sulhu bayan ɓarkewar rikici a jam’iyyar

Jam’iyyar NDC ta sanar da ɗaukar wasu muhimman matakai da nufin ƙarfafa dimokuraɗiyya, ladabtarwa da haɗin kai a cikin jam’iyyar, yayin da take shirin tunkarar zaɓuɓɓuka masu zuwa. An cimma matsayar ne a taro na biyu na Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar, kamar yadda ke ƙunshe cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa, Osa Director, ya fitar a ranar Asabar. A cewar sanarwar, jam’iyyar ta amince da kafa kwamitin sulhu domin magance duk wata rashin jituwa da ka iya tasowa a tsakanin mambobinta tare da ƙarfafa haɗin kai a cikin gida. Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa dukkan gwam

Masu neman sulhu sun faɗa hannun 'yan bindiga a Zamfara

Wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da dattijan wani ƙauye a Ƙaramar Hukumar Maradun da ke Jihar Zamfara bayan sun amsa gayyatar yin sulhu da su domin kawo ƙarshen hare-haren da suka addabi yankin. Lamarin ya faru ne a ƙauyen Magamin Diddi, wanda ke kusa da wani daji da ake zargin 'yan bindigar ke amfani da shi a matsayin mafaka. Da yake zantawa da BBC, Shugaban Ƙaramar Hukumar Maradun, Sunusi Ahmed Dosara, ya ce tun watanni uku da suka gabata mazauna ƙauyen ke fama da hare-haren 'yan bindiga da suka hana su gudanar da harkokinsu cikin walwala. Ya bayyana cewa 'yan bindigar sun aika saƙon gayyata

Masana MDD kan ’yancin addini sun fara ziyarar aiki a Najeriya

Manyan jami’an Majalisar Ɗinkin Duniya masu kula da harkokin ’yancin addini sun fara wata ziyarar aiki ta makwanni biyu a Najeriya domin nazarin halin da ake ciki game da ’yancin addini da zamantakewar al’umma a ƙasar. Ziyarar na zuwa ne bayan ce-ce-ku-ce da suka taso a shekarar da ta gabata kan zarge-zargen tauye ’yancin addini, musamman bayan wasu rahotanni da suka yi ikirarin cewa ana fuskantar ƙalubale wajen kare haƙƙin mabiya addinai daban-daban a Najeriya. Masana da masu bincike kan harkokin tsaro sun ce matsalolin da Najeriya ke fuskanta sun fi alaƙa da matsalar ta’addanci da hare-haren

An saki sama da mutum 400 da Boko Haram ta yi garkuwa da su a Borno

Satar mutane ta zama ɗaya daga cikin manyan dabarun da mayaƙan Boko Haram ke amfani da su a hare-haren da suke kaiwa a Najeriya tsawon sama da shekaru 17, musamman a yankin arewa maso gabas. Ƙungiyar Boko Haram ta saki fiye da mutum 400 da ta sace a farkon wannan shekara daga wani ƙauye da ke Jihar Borno, kamar yadda wani sanata da kuma wani shugaban ƙungiyar matasa suka tabbatar a ranar Lahadi. Samaila Kaigama, shugaban ƙungiyar Borno South Youth Alliance (BOSYA), ya bayyana cewa ƙungiyarsu ta tabbatar da sakin mata da yara 416 da aka sace daga ƙauyen Ngoshe. Ya ce an saki mutanen ne a ranar

Rikicin Iran da Isra’ila ya tayar da farashin man fetur a kasuwannin duniya

Farashin danyen mai ya fara tashi a kasuwannin duniya sakamakon rahotannin musayar hare-hare tsakanin Iran da Isra’ila, lamarin da ya ƙara tayar da fargaba kan yiwuwar tsanantar rikici a yankin Gabas ta Tsakiya. Masana tattalin arziki sun bayyana cewa damuwar yiwuwar faɗaɗa rikicin na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa tashin farashin mai a kasuwannin duniya, musamman ganin yankin na taka muhimmiyar rawa wajen samar da makamashi. Rahotanni sun nuna cewa farashin man Brent ya ƙaru da kashi 4.5 cikin ɗari, inda ya kai kusan dala 97.30 kan kowace ganga. Haka kuma, man West Texas Intermediat

Hezbollah ta harba makamai masu linzami kan sojojin Isra’ila a kudancin Lebanon

Ƙungiyar Hezbollah ta bayyana cewa ta harba jerin makamai masu linzami kan tarin motocin sojin Isra’ila tare da dakarunsu da ke kudancin Lebanon da safiyar yau. A cikin wani saƙo da ta wallafa a manhajar Telegram, ƙungiyar ta ce ta kai farmakin ne kan wani taron sojojin Isra’ila a wajen garin Beit Yahoun da ke kudancin ƙasar. Hezbollah ta bayyana harin a matsayin martani ga abin da ta kira karya yarjejeniyar tsagaita wuta, tare da ci gaba da hare-haren da Isra’ila ke kai wa kan ƙauyukan kudancin Lebanon. Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar sojin Isra’ila ba ta fitar da wani bayani ba

Atiku ya yabawa sojojin Najeriya kan ceto mutum 360 daga hannun Boko Haram a Borno

Atiku ya yabawa sojojin Najeriya kan ceto mutum 360 daga hannun Boko Haram a Borno Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yaba wa dakarun sojin Najeriya bisa nasarar da suka samu wajen kuɓutar da mutum 360 da aka sace a ƙauyen Ngoshe da ke Jihar Borno. Rahotanni sun ce an gudanar da aikin ceton ne a yankin Dutsen Mandara, inda mayaƙan Boko Haram suka tsare mutanen bayan wani hari da suka kai kan sansanin soji da ke Ngoshe. A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Litinin, Atiku ya bayyana farin cikinsa kan nasarar aik

Gwamnatin Tarayya ta rage kuɗaɗen gudanarwa na ministoci zuwa N700,000

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sanar da sabbin matakan da nufinsu shi ne ƙarfafa bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗen gwamnati da kuma inganta gaskiya da riƙon amana a ma’aikatun gwamnati. A ƙarƙashin sabbin ƙa’idojin, an rage adadin kuɗaɗen gudanarwa da ake warewa ministoci domin ayyukan gaggawa da sauran buƙatun ofis zuwa Naira 700,000. Matakin na daga cikin sauye-sauyen da gwamnati ke aiwatarwa domin tabbatar da an bi dokokin kuɗi yadda ya kamata tare da rage almubazzaranci a amfani da dukiyar jama’a. Sabuwar ƙa’idar ta fito ne cikin wata takarda da ta tanadi iyakar kuɗaɗen da jami’an gwamnati za su

Kwankwaso ya yi barazanar ficewa daga jam'iyar NDC

Hakan yabiyo bayan da jam’iyyar NDC ta cire wasu daga cikin ’yan takarar da tsagin Kwankwasiyya ya gabatar a Kano, tana mai cewa an karya yarjejeniyar da aka yi kan rabon mukamai da tikitin takara. Shugaban NDC na Kano, Hussaini Isah Mairiga, ya bayyana cewa an yi sauyin ne domin a bi yarjejeniyar da aka cimma tsakanin jam’iyyar da Kwankwasiyya. A cewar jam’iyyar, an amince cewa Kwankwasiyya za ta samu kashi 60% na mukamai da tikitin takara, yayin da tsofaffin ’yan jam’iyyar za su samu kashi 40%. Sauye-sauyen sun shafi wasu ’yan takarar Majalisar Wakilai da kuma na Majalisar Dokokin Jihar Kano

Atiku ya yabawa jami'an tsaron kasarnan Kan ceto mutane daga hannun boko haram

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a zaɓen 2027, Atiku Abubakar, ya yabawa jami’an tsaro bisa nasarar ceto mutane 360 da ‘yan ta’addan Boko Haram suka yi garkuwa da su a garin Ngoshe da ke jihar Borno . Atiku ya bayyana farin cikinsa da wannan nasara, yana mai cewa hakan ya kawo ƙarshen wahalar da waɗanda aka sace da iyalansu suka shafe watanni suna fuskanta tun bayan sace su a watan Maris. Ya kuma yabawa rundunar soji, musamman dakarun Operation HADIN KAI, da sauran hukumomin tsaro da suka taka rawa wajen gudanar da aikin ceton. Tsohon mataimakin s

KNARDA ta yi gargaɗi ga manoma da al’ummar jihar kan wasu mutane da ke amfani da sunanta wajen karɓar kuɗi da sunan samar da tallafin noma.

Hukumar Bunƙasa Noma da Raya Karkara ta Jihar Kano (KNARDA) ta yi gargaɗi ga manoma da al’ummar jihar kan wasu mutane da ke amfani da sunanta wajen karɓar kuɗi da sunan samar da tallafin noma. Shugaban hukumar, Dakta Farouk Ahmad Kurawa, ya bayyana cewa an gano wasu na karɓar kuɗi daga manoma, musamman a karkara, suna alƙawarin samar musu da taki, iri da sauran kayan aikin gona. Hukumar ta bayyana cewa ba ta karɓar kuɗi daga manoma domin samun tallafin gwamnati ko wani taimako, tare da cewa duk masu yin hakan ƴan damfara ne. KNARDA ta buƙaci al’umma su yi hattara da irin waɗannan mutane, sanna

Shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid, Florentino Pérez, ya sake lashe zaɓen shugabancin ƙungiyar ba tare da hamayya ba

Shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid, Florentino Pérez, ya sake lashe zaɓen shugabancin ƙungiyar ba tare da hamayya ba, wanda hakan ya ba shi damar ci gaba da jagorantar kulob ɗin a karo na shida. Pérez, mai shekaru 79, zai ci gaba da zama shugaban Real Madrid har zuwa shekarar 2030, bayan da babu wani ɗan takara da ya cika sharuddan tsayawa takara a zaɓen. Tun bayan komawarsa shugabancin ƙungiyar a shekarar 2009, Pérez ya taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarori masu yawa, ciki har da lashe kofunan gasar zakarun nahiyar turai da dama da kuma bunƙasa tattalin arzikin kungiyar. Magoya

Gwamnatin Tarayya ta sauya ranar fara jigilar rukunin farko na ‘yan Najeriya da ke son dawowa daga ƙasar Afirka ta Kudu, biyo bayan hare-haren kin jinin baki

Gwamnatin Tarayya ta sauya ranar fara jigilar rukunin farko na ‘yan Najeriya da ke son dawowa daga ƙasar Afirka ta Kudu, biyo bayan hare-haren kin jinin baki (xenophobia). Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Ebienfa, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin. A cewar Ebienfa, an sauya ranar jigilar rukunin farko na waɗanda ke son dawowa daga Afirka ta Kudu, wanda tun farko aka tsara yi a ranar Litinin (yau), zuwa ranar Laraba saboda wasu matsalolin shirye-shirye da ba a yi hasashensu ba. Ta ce Shugaba Bola Tinubu ya amince da jiragen kwashe mutane g

Rundunar Hisbah ta Kano ta sanar da cewa za ta fara gudanar da gwajin lafiya ga mutanen da za su amfana da shirin auren gata

Rundunar Hisbah ta Kano ta sanar da cewa za ta fara gudanar da gwajin lafiya ga mutanen da za su amfana da shirin auren gata da gwamnatin jihar ke shiryawa, wanda zai haɗa ma'aurata 3,000. Mataimakin Babban Kwamandan rundunar, Dr. Mujahideen Aminuddeen, ya bayyana cewa daga ranar Litinin 8 ga watan Yunin 2026 za a fara aikin tantancewar, inda ake buƙatar duk masu neman shiga shirin daga ƙananan hukumomi 24 su jr ofisoshin Hisbah da ke yankunan su. Ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Rogo, Wudil, Tudun Wada, Warawa, Kibiya, Dawakin Tofa, Garun Malam, Kura, Dambatta, Karaye, Tsanyawa,

Ministan harkokin cikin gida na Pakistan, Mohsen Naqvi, ya gana da ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, a birnin Tehran.

Ministan harkokin cikin gida na Pakistan, Mohsen Naqvi, ya gana da ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, a birnin Tehran. Kafin ganawar tasu a daren jiya Asabar, Naqvi ya kuma gana da takwaransa na Iran, Eskandar Momeni. Rahotannin kafafen yaɗa labaran Iran sun ce bayan ganawar, Naqvi ya bayyana cewa ya kai ziyara Tehran ne domin isar da wata “wasika ta musamman” da kuma wani “muhimmin sako” daga babban kwamandan rundunar sojin Pakistan da kuma firaministan ƙasar zuwa ga Mojtaba Khamenei. Sai dai rahotannin ba su bayyana cikakken abin da sakon ko wasikar suka ƙunsa ba.

Kasar mali ta Samar da shingayen tsaro a cikim dazuka na tsahon kilomita 40-40 tsakaninsu da cikin gari

A wani ɓangare na yaƙi da ta’addanci, ƙasar Mali ta samar da wasu shingayen jami’an tsaro a cikin dazuka, kilomita 40-40 tsakanin su da cikin gari, waɗanda aka haramtawa fararen hula kusantar gurin. Bayanai sun ce za’a samar da waɗannan shingaye ne a cikin dazukan ƙasar sama da 40, inda aka fi tsammanin ƴan ta’adda na samun mafaka. Da yake bayani kan sabon tsarin yaƙi da ta’addancin, ministan tsaron ƙasar, ya ce duk wanda aka samu a kusa da wannan shinge, za’a ɗauke shi a matsayin ɗan ta’adda. Wannan sabuwar dabara zata rage hare-haren kwanton bauna da ƴan ta’adda ke kaiwa sojoji ta hanyar saj

Miyetti Allah ta yabawa Gwamna Abba Kankwato filayen kiwo 371 a fadin jihar.

Shugabannin kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah da kungiyar ci gaban Fulani ta Najeriya sun yabawa gwamnatin Jihar Kano kan kokarin da take yi na kwato filayen kiwo 371, Burtalai da sauran guraren makiyaya da aka mamaye a fadin jihar. Shugabannin kungiyoyin biyu sun bayyana hakan ne a tattaunawa daban-daban da Kamfanin Dillancin Labarai na kasa (NAN), inda suka ce matakin zai taimaka wajen rage rikice-rikicen da ke faruwa tsakanin makiyaya da manoma. Shugaban kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah na Jihar Kano, Kyaftin Abdullahi Bakoji mai ritaya, ya ce mamaye filayen kiwo da hanyoyin dabbobi na d

Gwamnatin Jihar na ci gaba da daukar matakan magance matsalar zaizayar kasa a Jihar

Gwamnatin Jihar Kano ta ce tana ci gaba da daukar matakan magance matsalar zaizayar kasa da ta dade tana addabar al’ummar Bulbula da Gayawa, lamarin da ya janyo asarar rayuka da dukiyoyi tare da kawo cikas ga harkokin yau da kullum na mazauna yankunan. Kwamishinan Ma’aikatar Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi ta Jihar Kano, Dakta Dahir Muhammad Hashim, ya bayyana cewa gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta kuduri aniyar samar da mafita mai dorewa ga matsalar, duk da cewa mutane da dama sun yi imanin cewa magance ta abu ne mai matukar wahala.

Dakarun rundunar Operation Hadin Kai tare da dakaru na musamman sun ceto mutane 360

Dakarun rundunar Operation Hadin Kai tare da dakaru na musamman sun ceto mutane 360, galibinsu mata da kananan yara, da ’yan ta’adda suka sace daga garin Ngoshe da ke karamar hukumar Gwoza a jihar Borno. Kwamandan rundunar, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, ya ce an gudanar da samamen ne a yankin tsaunukan Mandara a ranar 6 ga Yuni, inda aka samu nasarar kubutar da wadanda aka sace tun bayan harin da aka kai wa al’ummar Ngoshe a watan Maris. Sai dai ya ce jarirai biyu sun rasu yayin aikin ceton sakamakon wahalar hanya. An kuma kai wadanda aka ceto asibiti domin kula da lafiyarsu kafin a hada su

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yi gargaɗi ga duk wanda ke taimaka wa ’yan bindiga ta hanyar ba su bayanai

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yi gargaɗi ga duk wanda ke taimaka wa ’yan bindiga ta hanyar ba su bayanai, yana mai cewa gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wanda aka samu da hannu a irin waɗannan ayyuka. ‎ ‎Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wani taron gaggawa na tsaro da aka gudanar a Fadar Gwamnati da ke Birnin Kebbi, bayan sake barkewar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar. ‎ ‎Ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da yin aiki kafada da kafada da jami’an tsaro domin dakile ayyukan masu tayar da ƙayar baya. ‎