AMMASCO RADIO NEWSROOM

Labarai

Trump ya yi barazanar hukunta Iran kan jinkirta tattaunawar sulhu

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce Iran za ta fuskanci sakamako kan abin da ya kira jan ƙafa wajen tattaunawar neman sulhu. A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Truth Social, Trump ya zargi Iran da jinkirta cimma yarjejeniya duk da cewa, a cewarsa, yarjejeniyar za ta kasance mai amfani ga ƙasar. Trump ya ce, “Iran ta ɗauki lokaci mai tsawo wajen tattaunawa kan yarjejeniya da za ta amfane ta, yanzu kuma za ta fuskanci sakamakon hakan.” Kalaman na Trump sun zo ne yayin da ake fuskantar sabon tashin hankali tsakanin Amurka da Iran, bayan rahotannin musayar hare-hare tsakanin ɓa

Qatar ta aike da tawaga Tehran don tattaunawa da Iran

Tawagar manyan jami’ai daga ƙasar Qatar ta isa birnin Tehran domin ganawa da jami’an gwamnatin Iran, a wani yunkuri na tattaunawa kan dangantakar ƙasashen biyu da kuma halin da ake ciki a yankin. Rahotanni daga kafafen yada labarai na Iran sun ce bangarorin za su yi musayar ra’ayoyi kan huldar da ke tsakaninsu, tare da duba sabbin ci gaban da suka shafi yankin Gabas ta Tsakiya. Jaridar gwamnatin Iran ta ce tattaunawar za ta kuma mayar da hankali kan ƙoƙarin diflomasiyya na warware rikicin da ke tsakanin Iran da Amurka, baya ga sauran batutuwan da suka shafi tsaro da zaman lafiyar yankin. Ziyar

Ƙudurin dokar ƙara yawan alƙalan kotu ya tsallake karatu na biyu a Majalisar Tarayya

Majalisar Dattawa ta tsallake karatu na biyu ga wasu ƙudurorin dokar da ke neman ƙara yawan alƙalan manyan kotunan ƙasar domin rage cunkoso a harkar shari’a da kuma hanzarta yanke hukunci. Ƙudurorin sun tanadi ƙara yawan alƙalan Babbar Kotun Tarayya daga 70 zuwa 90, yayin da za a ƙara yawan alƙalan Kotun Ɗaukaka Ƙara daga 70 zuwa 110. Shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Opeyemi Bamidele, wanda ya gabatar da ƙudurorin, ya ce matakin zai ƙara wa ɓangaren shari’a ƙarfi wajen tafiyar da yawan shari’o’in da ke ƙaruwa a faɗin ƙasar. Ya bayyana cewa dimokuraɗiyya ba za ta bunƙasa yadda ya kama

HADA-HADAR KUDADE

Yadda canjin kudaden kasashen ketare zuwa Naira ke gudana a kasuwannin chanji a yau 10-06-2026. • DOLLAR ₦1,390 • UAE DIRHAM ₦380 • CEFA ₦2,440 • RIYAL ₦350

Gwamnatin Kano ta Kudiri aniyar rage talauci ta hanyar amfani da sabbin hanyoyin tallafawa al'umma

Gwamnatin Jihar Kano ta sake tabbatar da aniyarta na rage talauci ta hanyar aiwatar da shirye-shirye da manufofin da za su inganta rayuwar al’umma. Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Murtala Sule Garo, ya bayyana hakan a wani taron tattaunawa na jihohin Arewa maso Yamma kan hanyoyin rage talauci, wanda UNICEF da Tarayyar Turai suka shirya. Ya ce talauci na ci gaba da zama babban ƙalubale a yankin, inda yake shafar miliyoyin mutane ta fannin ilimi, kiwon lafiya, abinci mai gina jiki da damar samun abin yi. Ya ƙara da cewa magance matsalar na buƙatar haɗin kai da jajircewar gwamnati da sauran

IMF ya bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar sun taimaka wajen inganta wasu sassan tattalin arzikin Najeriya

Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar sun taimaka wajen inganta wasu sassan tattalin arzikin Najeriya, amma ya nuna damuwa cewa fiye da kashi 63 cikin 100 na ’yan ƙasar har yanzu na rayuwa cikin talauci. A rahotonsa na shekara-shekara kan tattalin arzikin Najeriya, IMF ya ce duk da ci gaban da aka samu a wasu fannoni, miliyoyin ’yan Najeriya na ci gaba da fuskantar matsin rayuwa. Tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, Shugaba Tinubu ya cire tallafin man fetur tare da aiwatar da sauye-sauye a tsarin canjin

Gwamnonin Arewa maso Yamma sun kaddamar da shirin rage talauci

Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa maso Yamma ta gudanar da wani taron tattaunawa na musamman a Kano domin samar da hanyoyin rage talauci ta hanyar fadada shirye-shiryen tallafin jin kai da samar da sabbin hanyoyin samun kudade. A wajen taron, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda mataimakinsa Murtala Sule Garo ya wakilta, ya ce dole ne a dauki tsarin tallafin gudanar da rayuwa a matsayin jari na bunkasa tattalin arziki da ci gaban al’umma, ba kawai tallafi ba. Darakta Janar ta Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Yamma, Maryam Yahaya, ta bayyana cewa yankin na fuskantar matsaloli da suka hada da talau

Yansandan Kano Sun Kama ’Yandaba da Dilolin Ƙwaya 345 Cikin Kwana Uku

Rundunar 'Yansandan Jihar Kano ta sanar da kama mutane 345 da ake zargi da hannu a ayyukan daba, safarar miyagun ƙwayoyi da kuma mallakar makamai masu haɗari a wani samame na musamman da ta gudanar a faɗin jihar cikin kwanaki uku. Da yake jawabi ga manema labarai a Hedikwatar Rundunar da ke Bompai a ranar Litinin, Kwamishinan 'Yansandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce an gudanar da aikin ne bisa umarnin Babban Sufeton 'Yansandan Najeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu, tare da amfani da sahihan bayanan sirri da kuma rahotannin da aka samu daga al'umma. A cewarsa, samamen ya gudana ne tsa

Talauci Ya Ƙaru a Najeriya, Mutum Miliyan 60 Sun Kara Faɗawa Matsin Rayuwa – IMF

Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Najeriya ta aiwatar sun taimaka wajen ƙarfafa tattalin arzikin ƙasar, amma kuma sun zo da ƙalubale masu tsanani ga rayuwar al'umma, inda sama da 'yan Najeriya miliyan 60 suka ƙara faɗawa cikin talauci. A cikin wani rahoto da hukumar ta fitar, IMF ta ce matakan da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ɗauka cikin shekaru uku da suka gabata, ciki har da cire tallafin man fetur, sauya tsarin kasuwar canjin kuɗaɗen waje da kuma gyaran tsarin haraji, sun taimaka wajen daidaita wasu fannoni na tattalin ar

Najeriya Ta Yi Barazanar Daukar Mataki Kan Hare-Haren da Ake Kai wa 'Yan Ƙasarta a Afrika ta Kudu

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa tana nazarin matakan da za ta ɗauka kan abin da ta kira hare-hare da cin zarafin da ake yi wa 'yan ƙasarta a Afrika ta Kudu, yayin da take shirin fara kwashe wasu daga cikinsu daga ƙasar a ranar Laraba. Ministar Harkokin Wajen Najeriya, Bianca Ojukwu, ta ce gwamnati na duba yiwuwar mayar da martani kan abubuwan da ke faruwa, tare da ci gaba da tattaunawa domin cimma matsaya kan matakin da ya dace a ɗauka. Ta zargi hukumomin South Africa da rashin ɗaukar matakan da suka dace domin dakile hare-haren da ake kai wa 'yan Najeriya, duk da cewa yawancin waɗanda ke z

Babu wanda ya isa ya hana ni zuwa ko ina a Najeriya - Sheikh Gumi

Shahararren malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya magantu kan ziyarar da ya kai garin Ibadan a ƙarshen shekarar da ta gabata, bayan ce-ce-ku-ce da suka biyo baya cewa yana ƙoƙarin yaɗa manufofin addinin Musulunci a Jihar Oyo. Gumi ya jaddada cewa babu wanda zai hana shi ziyartar ko'ina a cikin ƙasar nan, yana mai cewa ba wata ƙungiyar Musulmi ko wani mutum daga yankin Kudu maso Yamma ne ya gayyace shi ba. A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Talata, ya ce ya je Ibadan ne a matsayin wakilin malaman addinin Musulunci na Arewacin Najeriya. Ya bayyana hakan ne kwana gu

Isra'ila Ta Kara Karfafa Hadin Gwiwa da Najeriya a fannin Noma da Kiwon Lafiya

Kasar Isra’ila ta ce tana ci gaba da karfafa hadin gwiwa da Najeriya a bangaren noma, inda manoman Najeriya ke amfana da iri da sabbin fasahohin noma na Isra’ila. A cewar jaridar Punch, Jakadan Isra’ila a Najeriya, Michael Freeman, ya bayyana cewa kasarsa ta tallafa wa Najeriya da motocin daukar marasa lafiya domin inganta ayyukan kiwon lafiya.

Amurka Ta Amince da Banbancin Matsaya Tsakaninta da Isra’ila

Mataimakin Shugaban Ƙasar Amurka, JD Vance, ya ce Amurka da Israel suna da muradu iri ɗaya a fannoni da dama, sai dai akwai lokutan da manufofinsu kan bambanta. Da yake magana da tashar Fox News a ranar Litinin, Vance ya bayyana cewa manufofin Washington kan Iran za su ci gaba da bin abin da shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ke ganin ya fi dacewa da muradun ƙasar. “Muna da muradu iri ɗaya da Isra’ila, amma akwai lokuta da muradunmu ke bambanta,” in ji Vance. Ya bayyana cewa babban burin Amurka shi ne tabbatar da cewa Iran ba ta mallaki makamin nukiliya ba. A cewarsa, gwamnatin Amurka ta sam

Sabbin Ministoci Biyu Sun Kama Aiki Bayan Tinubu Ya Rantsar da Su

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya rantsar da sabbin ministoci biyu, inda ya naɗa Joseph Tegbe a matsayin Ministan Lantarki, yayin da Sola Enikanolaiye ya zama Ƙaramin Ministan Harkokin Waje. An gudanar da bikin rantsarwar ne a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, tare da halartar iyalan sabbin ministocin da manyan jami’an gwamnati. Joseph Tegbe, ɗan asalin Ibadan da ke Jihar Oyo, ƙwararren masani ne a fannin sauye-sauyen tattalin arziki, harkokin kuɗi da tsarin hukumomi. Ya shafe sama da shekaru 35 yana aiki a gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu, inda ya taka muhimmiyar rawa a fannoni da

Mutum Uku Sun Mutu, Kimanin 40 Sun Jikkata a Hatsarin Jirgin Ƙasa a Delta

An tabbatar da mutuwar mutum uku tare da jikkatar kusan mutum 40 a wani hatsarin jirgin ƙasa da ya faru a Najeriya. Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin, inda fasinjoji da dama suka samu raunuka daban-daban. Rahotanni sun bayyana cewa jirgin ƙasar ya sauka daga kan layin dogo ne yayin da yake kan hanyarsa daga Warri zuwa Itakpe, a yankin Agbor na jihar Delta da ke kudancin Najeriya. A cikin wata sanarwa da NRC ta fitar, ta ce ta tura jami’an kai ɗaukin gaggawa tare da sauran hukumomin da abin ya shafa zuwa wurin da hatsar

Najeriya na bukatar shugabanni masu nagarta da kwarewa ba Yan shiyar kudu ko Arewa ba - Hakeem Baba

Shugaban Jam’iyyar PRP Hakeem Baba-Ahmed, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su daina duba yanki ko shiyya wajen zaɓen shugabanni, maimakon haka su zaɓi mutanen da ke da ƙwarewa, nagarta da hangen nesa. Baba-Ahmed ya yi wannan kira ne cikin shirin kamfanin dillancin Labarai na kasa NAN, mai taken Personality Interview Series a ranar Talata a Abuja. Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa shugaban na PRP ya yi wannan bayani ne a daidai lokacin da tsohon gwamnan Cross River State, Donald Duke, ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar domin zaɓen gama gari na shekarar 2027.

Gonakin Gwamnati ya kamata a kai matasa da aka kama a kano - Abba Hikima

Fitaccen lauya mai fafuktukar kare hakkin Dan adam Barista Abba Hikima, ya wallafa wannan sharawa ce a shafinsa na Facebook, kwana guda bayan da hukumar 'yan sanda ta jihar Kano tayi baje kolin wasu matasa masu dunbin yawa data kama Kan aikata laifuka daban daban a jihar. Hikima ya kara da cewa, idan har kotu ta tabbatar da laifin da ake zargin matasan da aikatawa, to mai makon a mika su gidan Gyaran hali, a Kai su wani fili ko gona su yi noma wasu kuma su share gari. Musamman ma waɗanda basu yi nisa a harkar ba. Inda ya cigaba da cewa yana yabawa jami’an yan sanda kan ƙoƙarinsu na kamo waɗann

HADA-HADAR KUDADE

Yadda canjin kudaden kasashen ketare zuwa Naira ke gudana a kasuwannin chanji a yau 09-06-2026. • DOLLAR ₦1,380 • UAE DIRHAM ₦360 • CEFA ₦2,440 • RIYAL ₦350

Harin Iran ya sa Isra’ila ta katse shigar agaji zuwa Gaza

Isra’ila ta sanar da sake rufe wuraren shiga da fita na Zirin Gaza bayan hare-haren da Iran ta kai a wasu sassan ƙasar, a wani mataki da mahukunta suka ce na da nasaba da tsaurara matakan tsaro. Matakin ya shafi rufe mashigar Rafah da ta Kerem Shalom, waɗanda ke daga cikin manyan hanyoyin da ake amfani da su wajen shigar da kayan agajin jin ƙai da sauran kayayyaki zuwa Zirin Gaza. Hukumar Cogat, mai kula da ayyukan gwamnatin Isra’ila a yankunan Falasdinawa kuma ƙarƙashin Ma’aikatar Tsaron ƙasar, ta ce an ɗauki matakin ne a matsayin wani ɓangare na matakan tsaro da suka zama wajibi sakamakon ha

Hukumar INEC ta fitar da jerin ƴan takarar zaben cike gurbi

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta wallafa jerin sunayen ƴan takarar da za su fafata a zaɓukan cike gurbi da aka shirya gudanarwa a ranar 20 ga Yunin 2026 a wasu kujerun Majalisar Dattawa, Majalisar Wakilai da Majalisun Dokokin Jihohi. A zaɓen Sanatan Ondo ta Kudu, ƴan takara huɗu ne za su fafata, waɗanda suka haɗa da Adesanya Olaoluwa na APP, Faduyile Francis Adedayo na APC, Akinwumi Adeolu Harrison na APM da kuma Nejo Funso Clement na BP. A mazaɓar Sanatan Nasarawa ta Arewa kuwa, Halilu Danladi Envwulu-Aza ne zai yi takara a ƙarƙashin jam’iyyar APC, yayin da Maku Labaran ke wakil