Malema ya zargi gwamnati da goyon bayan hare-haren ƙiyayya ga baƙi a Afirka ta Kudu
Ɗan siyasa kuma ɗan majalisar dokokin Afirka ta Kudu, Julius Malema , ya bayyana hare-haren ƙiyayya ga baƙi da aka kai kwanan nan a ƙasar a matsayin waɗanda "gwamnati ta ɗauki nauyinsu". Malema ya zargi ƴansanda da sauran hukumomin gwamnati da gaza ɗaukar matakan da suka dace domin dakatar da ayyukan tsoratarwa, cin zarafi da kuma hare-haren da ake kai wa baƙi a sassa daban-daban na ƙasar. Ya ce rashin ɗaukar mataki cikin gaggawa daga hukumomi ya ba wasu damar ci gaba da kai hare-hare ba tare da fargabar hukunci ba. Kalaman na Malema na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa ka
