Sojoji Sun Ceto Matar Marigayi Janar Rabe Daga Hannun ’Yan Bindiga
Rundunar sojin Najeriya ta sanar da ceto matar marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar daga hannun ’yan bindiga bayan wani samame da dakarun haɗin gwiwa suka kai a jihar Katsina. A wata sanarwa da Daraktan Sashen Yaɗa Labarai na rundunar, Sama’ila Uba, ya fitar, ya ce dakarun Operation Fansan Yamma ne suka gudanar da farmakin a Ƙaramar Hukumar Matazu. Sanarwar ta ce jami’an tsaro sun yi arangama da ’yan bindigar a ƙauyen Tunga, lamarin da ya tilasta musu tserewa sakamakon matsin lambar da dakarun suka yi musu. Sai dai kafin su gudu, ’yan bindigar sun harbi matar marigayin. Duk da haka, sojojin sun
