AMMASCO RADIO NEWSROOM

Labarai

Hezbollah da Isra’ila Sun Amince da Tsagaita Wuta Bayan Mummunan Artabu

Isra’ila da ƙungiyar Hezbollah sun amince da tsagaita wuta bayan kwana ɗaya na kazamin faɗa da ya haddasa asarar rayuka da jikkata mutane da dama a Lebanon. Wani babban jami’in gwamnatin Amurka ya tabbatar da cimma yarjejeniyar tsagaita wutar, yayin da kakakin rundunar sojin Isra’ila ya bayyana cewa sojojin ƙasar za su ci gaba da kasancewa cikin shiri idan har bukatar komawa fagen daga ta taso. Yarjejeniyar ta zo ne a daidai lokacin da ake nuna damuwa cewa ci gaba da rikicin a Lebanon na iya kawo cikas ga ƙoƙarin diflomasiyya da kuma yarjejeniyar zaman lafiya da ake ƙoƙarin tabbatarwa tsakanin

Rundunar Sojin Najeriya Za Ta Fara Ɗaukar Ƴan Jarida A Lokacin Ayyuka

Gwamnatin Tarayyar Najeriya na nazarin wani sabon tsari da zai bai wa ƴan jarida damar yin rakiya da dakarun sojin ƙasar a lokacin da za su ƙaddamar da wasu farmaki na musamman. Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya bayyana hakan a yayin wani taro da Ƙungiyar Ƴan Jarida ta Najeriya (NUJ) ta shirya a Abuja. Ministan ya ce matakin zai taimaka wajen inganta yadda ƴan jarida ke bayar da rahotanni kan haƙiƙanin abin da ke faruwa a yaƙin da ake yi da masu tayar da ƙayar baya da sauran matsalolin tsaron cikin gida. Ya ce hakan zai ƙara fahimtar da jama’a ayyukan da rundunar sojin ƙasar ke yi. Mai ba s

Majalisar Dokokin Zimbabwe Ta Amince da Tsawaita Wa'adin Shugaban Ƙasa Zuwa Shekara Bakwai

Majalisar dokokin Zimbabwe ta amince da ƙudirin doka na tsawaita wa'adin mulkin shugaban ƙasa daga shekara biyar zuwa bakwai. Wannan matakin zai bai wa Shugaba Emmerson Mnangagwa damar ci gaba da mulki har zuwa shekara ta 2030. Fiye da yan majalisa 200 ne suka kada ƙuri’a don amincewa da daftarin dokar a ranar Alhamis, abin da ya zarce kashi biyu bisa uku da ake buƙata domin yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin ƙasar. Ƙudirin ya kuma soke batun zaɓen shugaban ƙasa kai tsaye, inda daga yanzu ƴan majalisa za su kasance masu zaɓen shugabannin ƙasar. Mnangagwa, mai shekara 83, ya karɓi mulki ne

Gwamnatin Nijar Ta Zargi Faransa da Ɗaukar Nauyin Harin Filin Jirgin Sama na Niamey

Gwamnatin mulkin sojan Nijar ta zargi Faransa da ɗaukar nauyin harin da aka kai a filin jirgin saman Yamai da safiyar Alhamis. A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Tsaro ta ƙasar ta fitar kuma aka karanta a gidan talabijin na RTN a birnin Niamey, gwamnatin ta yi zargin cewa “masu ɗauke da makamai da Macron ke biya” ne suka kai wani mummunan hari da ya kashe aƙalla sojoji 11 da fararen hula biyu. Duk da haka, gwamnatin ƙasar ba ta bayar da wata shaidar da za ta tabbatar da wannan zargin ba, kuma Faransa ba ta ce uffan kan batun ba har yanzu. A cewar sanarwar, maharan waɗanda ake zargi suna sanye

Za a Gurfanar da Kyaftin ɗin Morocco Achraf Hakimi Kan Zargin Fyade

Kyaftin ɗin tawagar ƙwallon ƙafa ta Morocco, Achraf Hakimi, zai gurfana a gaban kotu a Faransa bayan masu gabatar da ƙara sun amince da ci gaba da shari’ar da ake yi masa kan zargin fyade. Wata mata mai shekara 24 ta zargi ɗan wasan bayan na Paris Saint-Germain da yi mata fyade a gidansa da ke birnin Paris a shekarar 2023. Ofishin mai gabatar da ƙara a Nanterre, da ke yammacin Paris, ya fara gudanar da bincike kan lamarin tun a watan Maris na shekarar 2023. A watan Fabrairun 2026, wani alƙali mai bincike ya bayar da umarnin a ci gaba da shari’ar, yayin da rahotanni daga kafofin yaɗa labarai na

Waɗanne Ƙungiyoyi Xabi Alonso Zai Fuskanta a Wasanni Biyar na Farko da Chelsea?

Sabuwar kakar Premier League ta zo da sabon salo ga Chelsea bayan naɗa Xabi Alonso a matsayin sabon kocinta kan kwantiragin shekara huɗu. Tsohon ɗan wasan tsakiyar fili na Liverpool da tawagar ƙasar Spain ya koma Stamford Bridge ne bayan rabuwa da Real Madrid, inda ya bar aikinsa kafin cika kwantiragin da ke tsakaninsu. Magoya bayan Chelsea na fatan Alonso zai kawo kwanciyar hankali da kuma dawo da ƙungiyar cikin sahun manyan masu fafatawa a Premier League. Wasanni Biyar na Farko na Chelsea Fulham (Waje) Brighton & Hove Albion (Gida) Arsenal (Waje) Hull City (Gida) Brentford (Waje) Daga cikin

Michael Carrick Zai Fara Aikinsa da Jadawali Mai Sauƙi

Binciken da kamfanin ƙididdiga na ƙwallon ƙafa, Opta, ya gudanar ya nuna cewa Manchester United ce za ta fara kakar Premier League ta 2026/27 da jadawalin wasanni mafi sauƙi idan aka kwatanta da sauran ƙungiyoyi. Rahoton ya nuna cewa United ce ke da mafi sauƙin wasanni biyar na farko a gasar, duk da cewa za ta kara da abokiyar hamayyarta ta birni, Manchester City, a cikin wannan lokaci. Sabuwar kakar za ta kuma kasance muhimmiyar dama ga Michael Carrick, wanda zai fara kakarsa ta farko a matsayin cikakken kocin Manchester United. Opta ta kuma bayyana cewa Liverpool da Newcastle United suna cik

Wanene Zai Maye Gurbin Kieran McKenna a Ipswich Town?

Ƙungiyar Ipswich Town na neman sabon koci bayan tsohon mai horar da ita, Kieran McKenna, ya yi murabus duk da nasarar da ya samu wajen dawo da ƙungiyar gasar Premier League bayan shekara guda a waje. A halin yanzu, tsohon kocin Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer, da kuma tsohon kocin Wolverhampton Wanderers, Gary O'Neil, na daga cikin waɗanda ake ganin suna kan gaba wajen karɓar aikin horar da ƙungiyar ta Portman Road. Duk da rashin koci a halin yanzu, magoya bayan Ipswich na ɗokin ganin yadda ƙungiyar za ta fara kakar wasanta a Premier League. Wasan farko na Ipswich zai kasance a gida da

Manchester City Za Ta Kara da United da Liverpool Tun Farkon Kaka

Ƙungiyar Manchester City na ci gaba da shirye-shiryen sabon kakar wasa yayin da ake rade-radin neman magajin kocinta, Pep Guardiola. Rahotanni na nuna cewa City na nazarin yiwuwar ɗaukar Enzo Maresca domin jagorantar ƙungiyar, kuma ana sa ran sabon kocin zai fara aiki kafin fara kakar wasa mai zuwa. Duk wanda zai karɓi ragamar horar da Manchester City, zai fuskanci gwaji mai tsauri tun daga farkon kakar wasa, domin ƙungiyar za ta kara da manyan abokan hamayyarta biyu cikin wasanni shida na farko. Jadawalin wasannin farko na Manchester City ya haɗa da: Bournemouth (Gida) Crystal Palace (Waje) C

Coventry Ta Koma Premier League Bayan Shekaru 25

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Coventry City za ta fara sabon babi a tarihinta yayin da ta koma gasar Premier League bayan shafe shekaru 25 ba ta buga gasar ba. A wasan buɗe kakar wasa, Coventry za ta karɓi baƙuncin Arsenal, wanda ke daga cikin manyan ƙungiyoyin gasar. Wasan zai haɗa ƙungiyar da ta lashe gasar Championship da kuma ɗaya daga cikin fitattun ƙungiyoyin Premier League. Bayan wannan wasan, Coventry za ta fuskanci ƙalubale masu tsauri, inda za ta yi wasa da Manchester City, kafin daga bisani ta ziyarci Hull City. Duk da wahalar wasannin farko da ke gabanta, komawar Coventry Premier League

Ƙungiyoyin Premier League da Suka Cancanci Gasar Turai a Kakar Wasa Mai Zuwa

An tabbatar da ƙungiyoyin Premier League da za su wakilci Ingila a manyan gasar ƙwallon ƙafa na Turai a kakar wasa mai zuwa. Ƙungiyoyi biyar sun samu tikitin shiga Gasar Zakarun Turai (UEFA Champions League), wato: Arsenal Manchester City Manchester United Aston Villa Liverpool A Gasar Europa League kuwa, ƙungiyoyi uku ne za su fafata, waɗanda suka haɗa da: Bournemouth Sunderland Crystal Palace Yayin da Brighton & Hove Albion za ta wakilci Ingila a Gasar UEFA Conference League. Hakan na nufin ƙungiyoyi tara daga Premier League ne za su shiga gasannin Turai daban-daban a kakar wasa mai zuwa, ab

Netanyahu Ya Ce Isra’ila Za Ta Ci Gaba da Zama a Kudancin Lebanon

Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya sake jaddada cewa gwamnatinsa ba ta da niyyar janye sojojin Isra’ila daga kudancin Lebanon da kuma yankunan da take kallon su a matsayin shingen kariyar tsaro. Netanyahu ya bayyana hakan ne yayin da wasu mambobin majalisarsa ke ci gaba da sukar yarjejeniyar da ake ƙoƙarin cimmawa tsakanin Amurka da Iran. Ya ce kamar yadda Isra’ila ta samu nasarar dawo da tsaro da zaman lafiya a yankunan da ke kan iyaka da Zirin Gaza, haka kuma tana da burin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a birane da ƙauyukan arewacin ƙasar. “Kiyaye tsaron al’ummomin da ke a

Tsoffin Janar-Janar Sun Bukaci Garambawul a Tsarin Tsaro Bayan Kisan Janar Rabe Abubakar

Tsoffin hafsoshin sojin Najeriya da abokan aikin marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar (mai ritaya) sun yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su sake duba tsarin tsaron ƙasar tare da ɗaukar matakan da suka dace domin magance matsalar rashin tsaro. Sun bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a Kaduna, bayan rasuwar tsohon Janar ɗin wanda aka ce wasu ƴan bindiga sun sace tare da kashe shi a Jihar Katsina. Birgediya Janar Isma’ila Abdullahi (mai ritaya), wanda ya yi magana a madadin abokan aiki da iyalan marigayin, ya ce lokaci ya yi da za a yi wa tsarin tsaron ƙasar garambaw

An Kashe Mutane 30 a Harin da aka Kai Filin Jirgin Sama na Niamey a Nijar

An kashe sojoji 11 a harin da aka kai filin jirgin sama na birnin Niamey a Jamhuriyar Nijar, inda aka ce an kashe mutane 30 gabaɗaya. Ma’aikatar Tsaro ta ƙasar ta ce daga cikin mutanen da aka kashe akwai sojoji 11 da fararen hula biyu, yayin da aka kashe mutum 22 daga cikin maharan. Da sanyin safiyar yau Alhamis ne aka fara jin ƙarar harbe-harbe da fashe-fashe a babban filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na birnin Niamey. Har yanzu ba a bayyana waɗanda suka kai harin ba. Hukumomin ƙasar sun ce an daƙile harin, kuma za a ci gaba da zirga-zirgar jiragen sama a filin. Nijar tare da maƙotanta Mali da

Firaministan Equatorial Guinea Ya Yi Murabus Tare da Gwamnatinsa Bayan Gaza Cika Alƙawura

Firaministan ƙasar Equatorial Guinea, Manuel Osa Nsue Nsua, ya yi murabus tare da dukkan mambobin gwamnatinsa bayan zargin cewa sun gaza cika alƙawuran da aka ɗora musu. Mataimakin Shugaban Ƙasar, Teodoro Nguema Obiang Mangue, wanda shi ne ɗa ga Shugaba Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, ya bayyana cewa gwamnatin ta kasa cimma har ma da kashi 10 cikin 100 na manufofin da aka ɗora mata tun lokacin da aka kafa ta. Ya ce firaministan ya miƙa takardar murabus ɗinsa tare da sauran ministoci da manyan jami’an gwamnati, bayan an yi nazari kan yadda suka gudanar da ayyukansu. Ko da yake ba a bayyana takam

JD Vance Ya Bukaci Isra'ila Ta Mutunta Yarjejeniyar Zaman Lafiya

Mataimakin Shugaban Amurka, J.D. Vance, ya bayyana cewa kowace ƙasa na da haƙƙin kare kanta, amma ya jaddada cewa Isra'ila dole ne ta mutunta yarjejeniyoyin zaman lafiya da ake ƙoƙarin cimma a yankin Gabas ta Tsakiya. Da yake amsa tambayoyin manema labarai kan sukar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi game da hare-haren da Isra'ila ta kai a Lebanon, Vance ya ce ba ya son tauye wa Isra'ila haƙƙinta na kare kanta daga barazanar tsaro. Duk da haka, ya bayyana damuwarsa game da wani hari da ya afku a wani yanki da jama'a ke zaune a birnin Beirut, yana mai cewa abin ya faru ne a daidai lokacin da

Taliban Ta Haramta Wa Ma’aikatan Gwamnati Zuwa Aiki da Manyan Wayoyi

Gwamnatin Taliban a Afghanistan ta haramta wa ma’aikatan gwamnati da na hukumomin tsaro zuwa wuraren aiki da manyan wayoyi, a wani sabon mataki da ta ce an ɗauka domin ƙara mayar da hankali kan ayyukan gwamnati. Ma’aikatan gwamnati da dama sun shaida wa BBC cewa an umarce su da kada su kawo wayoyin hannu na zamani zuwa ofisoshi da wuraren aiki, yayin da wasu suka ce an gargade su da su rage amfani da wayoyin har ma a gidajensu. Wani jami’in gwamnatin Taliban ya bayyana cewa manufar matakin ita ce tabbatar da cewa ma’aikata suna mayar da hankali kan ayyukan da aka ɗora musu maimakon ɓata lokaci

Tara Buhunan Ba-Haya a Ƙofar Gida Ya Jawo Wa Mutum Ɗauri da Tara

Wata kotu a birnin Kano ta yanke wa wani mutum hukuncin ɗauri da tarar kuɗi bayan an same shi da laifin tara buhunan ba-haya a ƙofar gidansa, lamarin da ya haddasa mummunan wari tare da barazana ga lafiyar maƙwabtansa. An gurfanar da Mohammed Sa’idu ne bayan mazauna unguwar sun kai ƙorafi kotu, suna zargin cewa buhunan ba-hayar da yake jibgawa a ƙofar gidansa sun jawo wari mai tsanani wanda ya hana su walwala da zama cikin kwanciyar hankali. Mai shari’a Halima Wali ta yanke hukuncin ɗaurin wata huɗu tare da tarar Naira 100,000, tana mai bayyana abin da ya aikata a matsayin barazana ga lafiyar

INEC Ta Fara Raba Kayan Zaɓe Gabanin Zaɓen Cike Gurbi na Sanatan Rivers South East

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa ta Independent (INEC) a Jihar Rivers ta fara rarraba kayan zaɓe don zaɓen ƙari na Majalisar Dattawa na Gundumar Kudu Gabas ta Jihar Rivers, da za a gudanar a ranar Asabar 20 ga watan Yuni. A yayin rarraba kayan a ofishin Babban Bankin Najeriya (CBN) da ke Port Harcourt, Kwamishinan Zaɓe na Jihar Rivers, Johnson Alalibo Senikien, ya tabbatar da cewa zaɓen zai kasance mai 'yanci, adalci da bayyananne.  Jam'iyyu huɗu na siyasa ne ke shiga zaɓen ƙarin da za a yi a cikin ƙananan hukumomi bakwai, inda aka samu jimillar masu rijista na jefa ƙuri'a 858,573 a wuraren zaɓe 1,629. Z

Najeriya Ta Sanya Hannu Kan Sabon Alƙawarin Goyon Bayan MDD

Gabanin zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA), Najeriya ta sanya hannu kan wata sabuwar takardar jaddada goyon baya ga Kundin Tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma ajandar gyaran tsarin MDD ta UN80. Jakadan Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya, Jimoh Ibrahim, ne ya sanya hannu a madadin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ya bayyana cewa Najeriya na ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa. Jakada Ibrahim, wanda kuma shi ne shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi, Kashe-Kashe da Gudanarwa na MDD, ya ce matakin ya nuna cikakken amincewar N