AMMASCO RADIO NEWSROOM

Labarai

DPO ne ya cire wa matata hijabi, ya tura ta kan titi

Aliyu Muhammad ya bayyana alhininsa bayan da wasu fusatattun mutane suka kashe tare da ƙona matarsa, Ummulkhairi, a jihar Kaduna bisa zargin satar yara. Ya ce tun kwanaki biyu kafin faruwar lamarin yana jin gabansa na faɗuwa, amma bai gaya mata ba domin kada ta damu. A ranar da lamarin ya faru, sun yi sallama da safe yayin da matar ta tafi wani wa’azi, shi kuma ya tafi aiki. Daga baya aka sanar da shi cewa an kama matarsa da zargin satar yara kuma an kai ta gidan mai unguwa. Sai dai kafin a gudanar da bincike ko tabbatar da zargin, mutane sun taru a gidan suna neman a miƙa musu ita domin su hu

Ma'aikatar kula da lafiya a matakin farko ta jijar kano, ta dakatar da dukan sugabannin masu aikin Rigakafi da aka tura Hotoron Arewa

Ma’aikatar Kula da Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Kano (KSPHCMB) ta amince da wasu muhimman matakai domin ƙarfafa ingancin ayyukan rigakafi, tabbatar da sahihancin bayanai da kuma inganta yadda ake gudanar da gangamin rigakafin BCU/IBRA na watan Yunin 2026. An cimma waɗannan matsayai ne a taron kwanaki biyu na masu ruwa da tsaki da aka gudanar ƙarƙashin jagorancin Darakta Janar na ma’aikatar, Farfesa Salisu Ahmad Ibrahim, kamar yadda ke kunshe cikin wata sanarwar manema labarai da Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta KSPHCMB, Sa’adatu Sulaiman ANIPR, ta sanya wa hannu a ranar 21 ga Yunin 2026. Bayan naz

Dole shugaban Tinubu ya ayyana dokar ta baci Kan matsalar tsaro kafin ya gagari kundila - makarfi

Tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma tsohon sanata, Ahmed Mohammed Makarfi, ya yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya ayyana dokar ta-baci kan matsalar rashin tsaro a Najeriya. Makarfi ya bayyana cewa halin da ƙasar ke ciki na rashin tsaro ya kai matakin da ke bukatar daukar matakin gaggawa domin dakile yawaitar hare-haren ‘yan bindiga, garkuwa da mutane da kuma kashe-kashen jama’a. Akwai bukatar gwamnati ta ƙara ƙarfafa hukumomin tsaro, tare da samar musu da kayan aiki da dabarun zamani domin tunkarar matsalar cikin inganci. Makarfi ya Kara da cewa, Najeriya na buƙatar haɗin kai tsakan

Nafisa Abdullahi Ta Jawo Ce-ce-ku-ce Bayan Furucinta Kan Aure

Fitacciyar jarumar Kannywood, Nafisa Abdullahi, ta janyo muhawara a kafafen sada zumunta bayan bayyana ra’ayinta game da aure, inda ta ce a ganinta babu wani abu a cikin aure face nauyi da ya fi rataya a wuyan mata. Jarumar ta bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da ya yaɗu a shafukan sada zumunta, inda ta tattauna kan yadda take kallon rayuwar aure da kuma matsayin mata a cikinta. A cewarta, wasu daga cikin abubuwan da mata ke fuskanta bayan shiga rayuwar aure na sa ta ganin cewa akwai nauyi mai yawa da ke kan mata idan aka kwatanta da maza. Kalaman nata sun haifar da martani mabambanta daga

Yakubu Kingsley ya shigar da Donald Duke kara gaban kotu yana kalubalantar zamansa Dan takarar shugaban kasa a jam’iyar PRP

Mai neman takarar kujerar shugaban ƙasa a jam’iyyar PRP, Yakubu Kingsley, ya kalubalanci nasarar tsohon gwamnan Jihar Cross River, Donald Duke, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasar jam’iyyar a zaɓen shekarar 2027. A cikin ƙarar da aka shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/1234/2026, Kingsley ta hannun lauyansa, D.A. Sulyman, ya shigar da ƙara a kan jam’iyyar PRP, Duke INEC a matsayin waɗanda ake ƙara na farko, na biyu da na uku bi da bi. Mai ƙarar na neman kotu ta soke ayyana Duke a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, inda yake zargin cewa tsohon gwamnan ba cikakken ɗan jam’iyyar ba ne kum

Dala Biliyan 6 Na Cikin Tayin Da Amurka Ke Yi Wa Iran

Wani rahoto da kafar yaɗa labarai ta Axios ta wallafa ya ce Amurka na neman Iran ta amince da bai wa masu binciken Majalisar Ɗinkin Duniya damar duba cibiyoyinta na nukiliya, a wani yunkuri na farfaɗo da tattaunawar da ke tsakanin ɓangarorin biyu. Rahoton ya ambato wasu majiyoyi daga yankin da suka ce Washington na son a cimma yarjejeniya inda Iran za ta sake buɗe ƙofofin cibiyoyinta na nukiliya ga masu bincike na ƙasa da ƙasa. An bayyana cewa wasu daga cikin waɗannan cibiyoyi sun taɓa fuskantar hare-hare daga Amurka da Isra’ila a baya, kuma ba a gudanar da irin wannan bincike ba tun watan Yun

Hukumar dake kula da aiyukan Gidajen gyaran Hali, Kashe gobara da civil defence ( CDCFIB) ta karyata rahotonnin dake cewa ta dage daukar sabbin jami'ai

Hukumar Kula da Ayyukan tsaro na farar hula, Gidajen Gyaran Hali, Kashe Gobara da Shige da Fice (CDCFIB) ta karyata wata sanarwar bogi da ke yawo a kafafen sada zumunta wadda ke ikirarin cewa an dage aikin daukar ma’aikatan shekarar 2026. Hukumar ta karyata Labarin ne cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X ranar Lahadi. Hukumar ta bukaci masu neman aiki da daukacin jama’a da su yi watsi da takardar saboda ba ta da inganci. Wannan na zuwa ne bayan hukumar ta saki sunayen wadanda suka samu nasara a jarabawar da hukumar ta gudanar da akayi da kwamfuta a watan nuwanbar 2025. Inda hukuma

muna murnar soyayya, juriya da sadaukarwar da iyaye maza ke nunawa a faɗin Najeriya da ma duniya baki ɗaya - Remi Tinubu

Uwar gidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta taya iyaye maza a Najeriya da ma duniya baki ɗaya murnar Ranar Uba ta Duniya da ake gudanarwa a yau Lahadi. A cikin saƙonta na murnar ranar, ta yaba da ƙoƙari, juriya da jajircewar iyaye maza wajen kula da tarbiyyar ’ya’yansu da kuma ɗaukar nauyin iyalansu. Sanata Oluremi Tinubu ta bayyana cewa iyaye maza na taka muhimmiyar rawa wajen gina tunani, tarbiyya da ƙwarin gwiwar yara, lamarin da ke taimakawa wajen kyautata makomarsu. Ta kuma ce soyayya, jagoranci, kariya da sadaukarwar da iyaye maza ke yi suna taimakawa wajen gina iyalai masu ƙarfi

Hon wanzam Zaki Dan Majalisa a Jihar Bauhci ya rasu a safiyar wannan rana

Dan majalisar dokokin Jihar Bauchi mai wakiltar mazabar Sakwa kuma Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar, Wanzam Zaki, ya rasu. Wanzam ya rasu ne a safiyar ranar Lahadi a garin Bauchi bayan gajeriyar rashin lafiya. Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Abubakar Sulaiman, ne ya sanar da rasuwar cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mukhtar Garba Kobi, ya fitar a ranar Lahadi. Kakakin Majalisar ya bayyana matuƙar alhininsa kan rasuwar, inda ya bayyana marigayin a matsayin jajirtaccen kuma sadaukararren mai hidimar jama'a wanda ya yi wa mazabarsa da Jihar Bauchi hidima ta gari da kwarewa.

Shin da gaske ne Kasar Iran ce ta yi Nasara a yakin gabas ta tsakiya?

Wani sabon bincike da aka gudanar a Isra’ila ya nuna cewa mafi yawan ‘yan ƙasar na ganin Iran ce ta fi cin moriyar rikicin Gabas ta Tsakiya da kuma yarjejeniyar da ta kulla da Amurka. Binciken da jami’ar Hebrew ta Urushalima tare da cibiyar Agam suka gudanar tsakanin 17 zuwa 20 ga watan Yuni ya nuna cewa kashi 92 cikin 100 na waɗanda aka tambaya sun yi imanin cewa Iran ce ta yi nasara ko ta fi amfana da rikicin. kashi 83 cikin 100 sun ce tsaron Isra’ila na dogon lokaci ya raunana sakamakon rikicin. Kazalika binciken ya nuna cewa kashi 72 cikin 100 na mahalarta ba su yarda da ikirarin Firamini

Cutar Ebola ta kashe mutane 200 inda Sama da mutane 900 suka kamu a Afrika

Cutar Ebola cikin Yan kwanaki ta yi ajalin mutane sama da 200, tare da kama jimillar mutane sama da 900, a cikin ƙasashen gabashin Afrika musamman Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo. Dr. Jean Kaseya shugaban na CDC ya ce jiran tallafin magunguna da rigakafi da kuma kayan kariya daga ƙetare na ɗaya daga cikin manyan dalilan da ke ƙara baiwa cutar damar bazuwa la’akari da irin tsahon lokacin da ake ɗauka kafin ƙasashen da ke bayar da tallafi su saki kuɗaden. Lokaci yayi da ya kamata Afrika ta kula da kanta ba tare da jiran masu bayar da taimako ba. Dr Jean ya bayar da misalin irin yadda ƙasashen Tur

MDD Ta Nuna Damuwa Kan Rashin Hukunta Masu Laifi a Najeriya

Wakiliya ta musamman ta Majalisar Ɗinkin Duniya kan ’Yancin Addini ko Imani, Nazila Ghanea, ta bayyana cewa rashin hukunta masu aikata laifuka da kuma raunin aiwatar da doka na daga cikin abubuwan da ke ƙara haddasa zarge-zargen tsanantawa da ma kisan kare-dangi a Najeriya. Ghanea ta bayyana hakan ne bayan wata ziyarar bincike ta tsawon makonni biyu da ta kai Najeriya domin tantance halin da ake ciki dangane da ’yancin addini da zaman tare tsakanin al’ummomi. Ta ce yawaitar hare-haren ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da kuma gaza gurfanar da masu hannu a laifuka na ci gaba da tauye ’yancin add

Hukumar Lafiya a matakin farko Haɗin gwiwa da shugabanin Kananun hukumomin kano sun fito da wani Daftari mai matakai shida na inganta kiwon Lafiya a jihar kano

Hukumar Kula da Lafiya ta Matakin Farko ta Jihar Kano (KSPHCMB) tare da Shugabannin Kananan Hukumomi 44 na jihar sun amince da wani daftarin tsarin aiki mai matakai shida da nufin ƙarfafa ayyukan kiwon lafiya a matakin farko da inganta gaskiya da riƙon amana, da kuma kyautata shugabanci a fannin lafiya a faɗin Jihar Kano. Wannann na cikin wata Sanarwa da Mai magana da yawun hukumar ta Jihar Kano Sa'adatu Sulaiman ta rabawa manema Labarai. An cimma waɗannan matsaya ne a yayin taron rabin shekara da aka gudanar na tsawon kwanaki biyu da aka gudanar a Jihar kaduna Taron ya mayar da hankali kan ne

Christopher Musa Ya Jaddada Muhimmancin ’Yan Jarida a Harkokin Tsaro

Gwamnatin Tarayyar Najeriya na nazarin wani sabon tsari da zai bai wa ’yan jarida damar rakiyar jami’an soji yayin wasu zaɓaɓɓun ayyukan tsaro a sassan ƙasar. Rahotanni sun nuna cewa manufar wannan tsari ita ce inganta yadda ake ruwaito al’amuran tsaro tare da bai wa jama’a damar samun sahihan bayanai kai tsaye daga wuraren da ake gudanar da ayyukan yaƙi da ta’addanci da sauran barazanar tsaro. Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Christopher Musa, ya bayyana hakan a wani taron tsaro na ƙasa da Nigeria Union of Journalists ta shirya a Abuja. Ya ce shirin zai taimaka wajen ƙarfafa alaƙa tsakanin kafa

An Ci Gaba da Kaɗa Ƙuri’a a Zaɓen Gwamnan Jihar Ekiti

Al’ummar Jihar Ekiti da ke yankin Kudu maso Yammacin Najeriya sun fara kaɗa ƙuri’unsu a zaɓen gwamna da ake gudanarwa domin zaɓar wanda zai jagoranci jihar na tsawon shekaru huɗu masu zuwa. Tun da safiyar ranar zaɓen ne masu jefa ƙuri’a suka fara tururuwa zuwa rumfunan zaɓe domin amfani da haƙƙinsu na zaɓen shugabanni. Rahotanni sun nuna cewa ‘yan takara 14 ne ke fafatawa a zaɓen, ciki har da gwamna mai ci, Biodun Oyebanji, wanda ke neman wa’adi na biyu a kan karagar mulki. Haka kuma, zaɓen ya ja hankali saboda kasancewar huɗu daga cikin ‘yan takarar sun zaɓi mata a matsayin mataimakansu, lama

Rikicin Liman da Kwamitin Gudanarwa Ya Jawo Rufe Masallaci a Bauchi

Gwamnatin Jihar Bauchi ta ba da umarnin rufe Masallacin Ibadurrahman da ke unguwar Shingen Abba a cikin garin Bauchi, sakamakon rikicin da ya daɗe yana ci gaba tsakanin limamin masallacin da kwamitin gudanarwarsa. An ɗauki matakin ne domin dakile yiwuwar ɓarkewar rikici da ka iya haddasa asarar rayuka da dukiyoyi a tsakanin al’ummar yankin. Kwamishinan Hisba na Hukumar Shari’ar Musulunci ta Jihar Bauchi, Barrista Aminu Balarabe Isah, ya bayyana wa manema labarai cewa gwamnatin jihar ta ɗauki matakin ne bisa umarnin kotu da kuma la’akari da yanayin rikicin da ya shafe kusan shekaru uku yana gud

Sama da mutum dubu Goma sha uku 13 masu fama da cutar amosanin jini ne ke amfana da kulawa da magani kyauta a karkashin cibiyar Abba Care Sickle Cell Diseases Centre a Jihar Kano.

Sama da mutum dubu Goma sha uku 13 masu fama da cutar amosanin jini ne ke amfana da kulawa da magani kyauta a karkashin cibiyar Abba Care Sickle Cell Diseases Centre a Jihar Kano. Shugabar Hukumar Taimakon Lafiya ta Jihar Kano, Dr. Rahila Mukhtar, ce ta bayyana hakan yayin wani gangamin tattaki da aka gudanar a ranar Asabar, a matsayin wani bangare na bikin ranar wayar da kan al'umma kan cutar amosanin jini. Dr. Rahila ta ce an yi amfani da wannan rana ne wajen jan hankalin jama'a da su kara kaimi wajen ba masu fama da cutar kulawa da goyon baya. Ta kuma yabawa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Y

Sojojin Sama Na Najeriya Sun Kai Hari A Kan Wuraren Ƙarfin ‘Yan Ta’adda A Arewa Maso Yamma

Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya ta ci gaba da gudanar da ayyukan sama masu tsanani a kan ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga a yankin Arewa Maso Yamma a ƙarƙashin Sashen Sama na Operation FANSAN YAMMA Sector 1. A cikin wata sanarwa da Daraktan Hulɗa da Jama’a da Bayar da Bayanai, Air Commodore Ehimen Ejodame ya fitar, an bayyana cewa rundunar ta yi hari mai tsanani a ranakun 18 da 19 ga Yuni 2026, inda aka kai hari a kan wuraren da aka gano ‘yan ta’adda suke, tare da ƙarfafa ayyukan leken asiri, sa ido da kuma bincike mai ɗauke da makamai don tallafa wa ayyukan haɗin gwiwa. Bayan samun bayanan sirr

Sojoji Sun Ceto Mutane 22 da aka Sace a Jihar Sokoto

Rundunar Sojoji ta Sashen 2 na Joint Task Force Northwest Operation FANSAN YAMMA ta ceto mutane 22 da aka sace a wasu ayyuka daban-daban a Jihar Sokoto. Wani bayani da Jami’in Bayar da Bayanai na Rundunar Joint Task Force Northwest Operation FANSAN YAMMA, Laftanar Kanal Aliyu Danja ya fitar, ya ce ayyukan ceton sun biyo bayan bayanan sirri da kiraye-kirayen taimako game da ayyukan ‘yan ta’adda a yankunan da abin ya shafa. A cikin aiki na farko da aka yi a kan hanyar Sabon Birni–Shinkafi a ƙauyen Kura Mota, ‘yan ta’adda sun kai hari kan motocin kasuwanci biyu kuma sun sace fasinjoji da dama bay

Mawaki soja Boy ya kalubalanci salon jagorancin Ali Nuhu

Mawakin ya ce da ace shi aka ba irin wannan kujera, da ya gindaya sharudda ga Shugaban Kasa kafin ya karba, kuma da zai yi murabus idan har bai iya kawo canji mai anfani cikin shekaru uku ba. Ya ce: “Duk inda ba zan iya kawo sauyi mai anfani ba, bana son kasancewa a wurin. Bata lokaci ne kawai.” Soja Boy ya kuma yi zargin cewa babban abin da shugaban Hukumar Fina-finai ta Nijeriya ke yi shi ne halartar tarukan Kannywood a kasashen waje kamar India, Paris, London da Jamus ta hanyar takardun izinin gwamnati (memos), yana daukar hotuna yana wallafawa a shafukansa. Ya yi kira ga masana’antar kirki