Matatar Mai ta Dangote ta karyata zargin cewa tana sayarwa tare da sake sayo mai daga Kasar Togo
Kamfanin Matatar Mai ta Dangote Petroleum Refinery ya yi watsi da zarge-zargen da ke cewa ana fitar da kayayyakin man fetur da ake tacewa a matatar zuwa birnin Lomé na ƙasar Togo, sannan daga baya a sake shigo da su Najeriya. PUNCH Online ta rawaito cewa wasu bayanai da suka yadu a kafafen sada zumunta sun yi ikirarin cewa ana fitar da kayayyakin da matatar Dangote ke samarwa zuwa ƙasashen maƙwabta kafin a dawo da su Najeriya. A wata sanarwa da kamfanin ya fitar ta shafinsa na X ranar Talata, mahukuntan matatar sun bayyana zargin a matsayin marar tushe kuma wanda bai dogara da haƙiƙanin kasuwa
