Obi ya bukaci shugaban Tinubu ya dage Samar da yansandan jihohi zuwa bayan zaben 2027
Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya dakatar da aiwatar da tsarin kafa ‘yansandan jihohi har sai bayan babban zaɓen shekarar 2027. Obi ya bayyana haka ne bayan majalisar dokoki ta ƙasa ta amince da kudirin kafa ‘yansandan jihohi domin inganta tsaro da rage nauyin rundunar ‘yansandan ƙasa. A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Obi ya ce duk da cewa kafa ‘yansandan jihohi mataki ne mai kyau, akwai fargabar cewa tsarin na iya zama abin amfani na siyasa idan aka fara aiwatar da shi kafin zaɓen 2027. Tsohon gwamnan jihar Anambra ya
