Sama da Mutane 10,000 Sun Nemi Guraben Aikin Koyarwa 1,000 a Nasarawa
Sama da mutum 10,000 ne suka nemi guraben aikin koyarwa 1,000 a makarantun firamare da Gwamnatin Jihar Nasarawa ta amince da ɗauka ƙarƙashin wani shiri na musamman da aka tanada domin inganta ilimi a yankunan karkara. Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Nasarawa kan Harkokin Jama’a, Peter Ahemba , ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai na wata biyu-biyu da aka gudanar a Sakatariyar Ƙungiyar Ƴan Jarida ta Nijeriya (NUJ) reshen jihar da ke Lafiya. A cewarsa, ɗaukar malaman ya biyo bayan amincewar gwamnatin jihar da shirin samar da malamai 1,000 domin cike giɓin ƙarancin malamai
