Kwankwaso ya mayar wa Ali Modu Sheriff martani kan kalamansa game da Peter Obi
Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya soki tsohon Gwamnan Jihar Borno, Ali Modu Sheriff, kan ikirarinsa cewa Peter Obi ba shi da ƙarfin samun goyon baya a Arewacin Najeriya. A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Kwankwaso ya ce kalaman Sheriff ba su yi daidai da hakikanin siyasar Arewa ba, yana mai tunatar da cewa Obi ya samu kusan ƙuri'u miliyan 2.8 a Arewa a zaɓen shugaban ƙasa da ya gabata. Ya kuma ce matsalolin tattalin arziki da tsaro da ake fuskanta, tare da abin da ya kira gazawar gwamnatin APC, sun ƙara wa haɗakar tikitin OK ƙarfi
