AMMASCO RADIO NEWSROOM

Labarai

Sojojin Najeriya Sun Kama Wata Ƴar Chadi Bisa Zargin Kai Wa Boko Haram Miyagun Ƙwayoyi Da Giya

Rundunar Sojojin Najeriya ta bayyana cewa dakarunta na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Operation Hadin Kai sun kama wata 'yar ƙasar Chadi da ake zargi da kai wa mayaƙan Boko Haram miyagun ƙwayoyi, giya da sauran haramtattun kayayyaki. A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar, ya ce an kama matar ne bayan wani aikin sintiri da ya samu nasara sakamakon ingantattun bayanan sirri. Ya ce a ranar 9 ga Yuli, dakarun sun cafke wadda ake zargin, Misis Rachael Samuel, mai shekara 48, 'yar garin Kelo da ke lardin Chari-Baguirmi na Jamhuriyar Chadi. Binciken farko, a cewar r

Wike: Yawancin Ayyukan Da Muka Kammala A Abuja Tsofaffin Ayyuka Ne Da Aka Yi Watsi Da Su

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana cewa mafi yawan ayyukan da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta kammala a Abuja tsoffin ayyuka ne da aka yi watsi da su tun gwamnatocin da suka gabata. Da yake ganawa da manema labarai a Abuja ranar Alhamis, Wike ya ce gwamnatin ta ba da fifiko wajen kammala ayyukan da ta gada kafin fara sabbin ayyuka. Ya bayyana cewa wasu daga cikin ayyukan sun shafe shekaru tsakanin 15 zuwa 16 ba a kammala su ba, amma gwamnatin Shugaba Tinubu ta ba da umarnin a farfaɗo da su domin kada a bar muhimman ayyukan gwamnati su lalace. A cewarsa, kusan kashi 60

Janar Christopher Musa Ya Gargaɗi Jami'an Tsaro Kan Jinkirin Ɗaukar Mataki A Kan 'Yan Ta'adda

Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa, ya gargaɗi jami'an tsaro da su guji jinkiri wajen ɗaukar mataki a kan 'yan ta'adda da masu garkuwa da mutane yayin gudanar da ayyukansu. Janar Musa ya yi wannan jawabi ne a ranar Laraba yayin rabon motocin sulke da sauran kayan aikin tsaro ga hukumomin tsaro a jihar Sakkwato, inda ya sake jaddada aniyar gwamnatin tarayya na ƙarfafa yaƙi da matsalolin tsaro a faɗin ƙasar. Ya ce duk wani jami'in tsaro da aka tura bakin aiki bai kamata ya tsaya jiran wani ƙarin umarni ba idan ya fuskanci barazana daga 'yan ta'adda ko 'yan bindiga. A ce

Sojojin Najeriya Sun Ce Mayaƙan ISWAP Shida Sun Miƙa Wuya A Borno

Rundunar Sojojin Najeriya ta bayyana cewa mayaƙan Boko Haram na tsagin ISWAP guda shida sun miƙa wuya tare da iyalansu ga dakarun Operation Hadin Kai a jihar Borno. Mai magana da yawun rundunar Operation Hadin Kai, Kyaftin Mohammed Goni, ya ce binciken farko ya nuna cewa mutanen sun fito ne daga maɓoyar mayaƙan da ke Guduf Bubayagwa da Chikide a tsaunukan Mandara da ke ƙaramar hukumar Gwoza. A cewarsa, dakarun sun kuma ƙwato dalar Amurka 1,120, wayoyin salula biyu kirar Tecno da wasu kayayyaki daban-daban daga hannun waɗanda suka miƙa wuya. Hakazalika, sojojin sun kama wani mutum da ake zargi

Kotu Ta Tura Tsohon Shugaban Kotun Ɗa'ar Ma'aikata, Danladi Umar, Gidan Gyaran Hali

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Maitama, Abuja, ta ba da umarnin tsare tsohon shugaban Kotun Ɗa'ar Ma'aikata ta Najeriya (CCT), Danladi Umar, a gidan gyaran hali na Kuje. Mai shari'a Peter Kekemeke ne ya bayar da umarnin bayan Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta'annati (EFCC) ta gurfanar da shi kan tuhume-tuhume guda huɗu da suka shafi zargin cin zarafin ofis da kuma karɓar kuɗaɗe ba bisa ƙa'ida ba. EFCC ta yi zargin cewa Danladi Umar ya yi amfani da asusun bankin matarsa a shekarar 2021 wajen karɓar Naira miliyan 5.5 daga wani kamfani da ya samu kwangilar fentin hedi

Iran Ta Ce A Shirye Take Ta Kare Kanta Daga Duk Wani Hari Na Amurka

Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi, ya bayyana cewa ƙasarsa a shirye take ta kare kanta idan har Amurka ta ci gaba da kai mata hare-hare. A wata tattaunawa ta waya da ya yi da Babban Hafsan Sojojin Pakistan, Field Marshal Asim Munir, Araqchi ya bayyana kalaman wasu jami'an Amurka na baya-bayan nan a matsayin abin da ya ce na nuna yiwuwar karya yarjejeniyoyin da aka cimma da kuma ƙara rura wutar rikici. Ministan ya kuma yi Allah wadai da hare-haren da Amurka ta kai kan wasu yankuna a Iran, yana mai cewa hakan ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa da kuma Kundin Tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya

EFCC Ta Gurfanar Da Bello Bodejo Kan Zargin Hada-Hadar Kuɗaɗe Ba Bisa Ƙa'ida Ba

Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta'annati (EFCC) ta gurfanar da shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta ƙasa, Bello Bodejo, a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa zargin gudanar da mu'amalar kuɗaɗe da ta haura dala miliyan 2.63 ba tare da bin tanade-tanaden doka ba. An gurfanar da Bodejo a gaban Mai Shari'a Inyang Ekwo kan tuhume-tuhume guda 12 da EFCC ta gabatar. A cewar EFCC, ana zargin Bodejo da karɓar tsabar kuɗi dala 200,000 daga tsohon Akanta Janar na Jihar Bauchi, Sa'idu Abubakar, a ranar 21 ga Janairun 2022, lamarin da hukumar ta ce ya saɓa wa dokokin da

Atiku Ya Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Kare Peter Obi, Ta Kuma Saki El-Rufai

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta tabbatar da tsaron Peter Obi tare da gaggauta sakin tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai. A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce kare rayuka da tabbatar da 'yancin 'yan adawa nauyi ne da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya ɗora wa gwamnati. Ya ce bai kamata gwamnatin tarayya ta mayar da martani ga korafe-korafen Peter Obi da zage-zage ba, yana mai cewa abin da ya dace shi ne ta yi bayani cikin natsuwa tare da tabbatar da gaski

Sufeto Janar Na 'Yan Sanda Ya Yi Kira Da A Ƙarfafa Haɗin Gwiwar Hukumomin Tsaro Na Duniya

Sufeto Janar na Rundunar 'Yan Sandan Najeriya (IGP), Olatunji Rilwan Disu, ya sake jaddada aniyar Najeriya na ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin 'yan sanda na ƙasashe daban-daban domin bunƙasa zaman lafiya, tsaro da ci gaba mai ɗorewa a duniya. IGP Disu ya bayyana hakan ne yayin halartar Taron Koli na Biyar na Shugabannin Hukumomin 'Yan Sanda na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNCOPS 2026), wanda aka gudanar daga ranar 7 zuwa 8 ga Yulin 2026 a hedikwatar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke birnin New York na Amurka. Taron ya haɗa ministoci, sufetocin janar na 'yan sanda, shugabannin hukumomin tsaro da

Matatar Dangote Ta Fara Jigilar Fetur Kyauta Zuwa Jihohi Shida Da Abuja

Matatar Man Fetur ta Dangote ta fara jigilar fetur kyauta zuwa jihohi shida a faɗin Najeriya, ciki har da Babban Birnin Tarayya, Abuja. Kamfanin Dangote ya sanar da fara wannan shiri ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta na X a ranar Laraba. A cewar kamfanin, shirin na da nufin sauƙaƙa isar da man fetur zuwa sassa daban-daban na ƙasar tare da inganta samar da kayayyakin man fetur ga masu amfani. Sai dai sanarwar ba ta yi cikakken bayani kan tsawon lokacin da shirin zai gudana ko kuma sauran jihohin da za su ci gajiyarsa a mataki na gaba ba. Ana sa ran wannan m

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Naira Tiriliyan 11 A Matsayin Burin Kuɗaɗen Shiga Na Hukumar Kwastam A 2026

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da buƙatar Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) na tara sama da Naira tiriliyan 11 a matsayin kuɗaɗen shiga na shekarar 2026. A yayin nazarin rahoton Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Kwastam da Harajin Kaya, 'yan majalisar sun yaba da irin nasarorin da hukumar ta samu a shekarar kasafin kuɗi ta 2025. Majalisar ta lura cewa Hukumar Kwastam ta zarce burin tara kuɗaɗen shiga da aka sa mata a shekarar 2025, inda ta tara Naira tiriliyan 7.2 maimakon Naira tiriliyan 6.5 da aka tsara, wanda ya nuna ƙarin sama da kashi 10 cikin ɗari. Domin cimma sabon buri na

EFCC Ta Miƙa Kayan Da Aka Kwato Daga Masu Laifi Ga Ma'aikatar Ilimi

Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta'annati (EFCC) ta miƙa wasu kayayyakin da aka ƙwato daga hannun masu aikata laifuka ga Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, domin amfanin ɓangaren ilimi. Kayayyakin sun haɗa da gadajen bene masu hawa biyu guda 501, katifu guda 939 da kuma gadaje na katako guda 12, waɗanda aka ƙwato yayin wani samame na musamman da EFCC ta gudanar kan masu aikata laifukan yanar gizo. Hukumar ta bayyana cewa an danganta kayayyakin da mutane 792 da ake zargi da aikata laifuka, ciki har da baƙi 193 daga ƙasashen waje, waɗanda aka gurfanar a kotu kafin daga bisani a maya

Yan Sanda A Kaduna Sun Kama Mutane Shida Kan Kisan Matafiya Biyu Ta Hanyar Taron Dangi

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kaduna ta yi Allah wadai da kisan wasu matafiya biyu, Muhammadu Sani da abokinsa Aliyu Mohammed, dukkansu mazauna ƙauyen Umar da ke ƙaramar hukumar Igabi, waɗanda wasu fusatattun mutane suka kashe bisa zargin sata. A wata sanarwa da Jami'in Hulɗa da Jama'a na Rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ya ce marigayin da abokinsa na kan hanyarsu ta zuwa Tudun Wada da ke Zariya ne domin duba wani baffansu da ke kwance jinya, inda suke tafiya da sabuwar babur. Sanarwar ta ce wasu mutane sun yi musu kuskuren zargin cewa ɓarayi ne, kuma duk da ƙoƙarin da suka yi na bayyana ka

Majalisar Dattawa Ta Binciki Kashe-Kuɗen Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma

Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da Harkokin Raya Yankuna ya fara bincike kan yadda Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma (NWDC) ke gudanar da harkokinta da kashe kuɗaɗenta. 'Yan majalisar sun nuna damuwa kan yadda aka kashe kusan Naira biliyan 1.19, inda suka yi zargin cewa kimanin Naira miliyan 943, wanda ya kai kusan kashi 79 cikin ɗari na adadin, an kashe su ne wajen biyan alawus-alawus na mambobin hukumar. Kwamitin ya kuma tambayi dalilin da ya sa Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ita ce kaɗai daga cikin hukumomin raya yankuna da ba ta da daraktocin gudanarwa da kuma ma'aikata, duk d

Tinubu Ya Karɓi Baƙuncin Ƙaramin Ministan Harkokin Wajen Daular Larabawa

Alamu na nuna cewa Najeriya da Daular Larabawa (UAE) na ƙara ƙarfafa alaƙar diflomasiyya da tattalin arzikinsu, yayin da ƙasashen biyu ke kammala shirye-shiryen kafa Kwamitin Haɗin Gwiwa na Dindindin domin bunƙasa haɗin gwiwarsu. A wannan ƙoƙari ne Ƙaramin Ministan Harkokin Wajen Hadaddiyar Daular Larabawa, Sheikh Shakhboot Bin Al Nahyan, ya kai ziyarar aiki ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Talata. Ministar Harkokin Wajen Najeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, ce ta raka baƙon ministan zuwa ganawar da shugaban ƙasar. Da take jawabi bayan ganawar, Bianca

Kotun Majistare Ta Yanke Wa Direba Hukuncin Aikin Al'umma Da Tara Saboda Tukin Ganganci

Kotun Majistare da ke Wuse a Abuja ta yanke wa wani direba mai suna Atada Victor hukuncin yin aikin al'umma na tsawon makonni biyu, tare da biyan tarar kuɗi da diyya da suka kai Naira miliyan 1.08, bayan samunsa da laifin tukin ganganci, cin zarafin jami'in Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) da kuma sauran laifukan karya dokokin hanya. A cikin wata sanarwa da Jami'in Yaɗa Labarai na FRSC, Osondu Ohaeri, ya sanya wa hannu, ya ce lamarin ya faru ne yayin da jami'an hukumar ke gudanar da sintiri na yau da kullum a Babban Birnin Tarayya, Abuja. Sanarwar ta ce jami'an FRSC sun yi ƙoƙarin tsayar

Ma'aikatar Tsaro Ta Bukaci Kamfanonin Tsaro Masu Zaman Kansu Su Yi Amfani Da Fasahar Tattara Bayanai

Ma'aikatar Tsaro ta Tarayya ta buƙaci kamfanonin tsaro masu zaman kansu a Najeriya su rungumi amfani da fasahar zamani da tsarin tattara bayanan sirri domin ƙarfafa gudummawar da suke bayarwa wajen inganta tsaron ƙasa. An bayyana wannan kira ne a yayin wani taron yini guda kan harkokin tsaro da aka gudanar a Abuja, inda masana tsaro, masu tsara manufofi da masu ruwa da tsaki suka tattauna hanyoyin sauya tsarin ayyukan kamfanonin tsaro daga dogaro da yawan jami'ai zuwa tsarin da ke amfani da bayanan sirri da fasahar zamani. A cikin saƙon da ya aike wa taron, Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Mohamm

Gwamna Zulum Ya Ƙaddamar Da Noman Damina Na 2026 Da Rarraba Kayan Tallafin Noma A Borno

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ƙaddamar da shirin noman damina na shekarar 2026, tare da fara sayar da takin zamani a farashin da gwamnati ta amince da shi, da kuma raba kayan tallafin noma kyauta ga manoma a faɗin jihar. Tallafin ya shafi ƙananan manoma, masu rauni, matasa, mata da kuma manoman da suka koma garuruwansu bayan sun rasa matsugunansu sakamakon matsalolin tsaro. Gwamnatin jihar ta bayyana cewa shirin na da nufin bunƙasa harkar noma, ƙarfafa samar da abinci, inganta tattalin arziki, samar da ayyukan yi da kuma ƙarfafa zaman lafiya da ci gaban al'ummomi. Haka

Yan Sanda A Bayelsa Sun Kama Uba Da Ɗansa Da Bindigogi Huɗu Ba Bisa Ƙa'ida Ba

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Bayelsa ta sanar da kama wasu mutane biyu, uba da ɗansa, bisa zargin mallakar bindigogi huɗu masu harbi guda (single-barrel guns) ba bisa ƙa'ida ba. A cikin wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, SP Musa Mohammed, ya fitar, ya ce jami'an sashen yaƙi da miyagun laifuka sun kama mutanen ne yayin wani aikin sintiri da binciken ababen hawa a kan titin Igbogene–Tombia da ke Yenagoa. Sanarwar ta bayyana cewa waɗanda ake zargin sun haɗa da Tibi da ɗansa Oyabrade, dukkansu mazauna ƙaramar hukumar Ekeremor ta jihar Bayelsa. Binciken farko ya nuna cewa ana zargin

Farashin Ɗanyen Mai Ya Tashi Bayan Rikicin Tsagaita Wuta Tsakanin Amurka Da Iran

Farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya tashi da sama da kashi biyar cikin ɗari a ranar Laraba, bayan da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsakanin Amurka da Iran ta rushe. Bayan wannan sanarwa, farashin ɗanyen mai na Brent, wanda ake amfani da shi a matsayin ma'aunin kasuwar mai ta duniya, ya haura zuwa dala 78.09 kan kowace ganga. Rahotanni sun nuna cewa masu zuba jari da masu sa ido kan kasuwannin duniya na ci gaba da bibiyar yadda rikicin ke ƙara ta'azzara, saboda tasirinsa ga samar da makamashi da kasuwannin duniya. Tun kafin wannan