AMMASCO RADIO NEWSROOM

Labarai

Jirgin karshe na yan najeriya mazauna kasar afrika ta kudu dauke da mutane 315 zata isa gida a gobe laraba 15 ga watan yuli,2026

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin Ma'aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Imomotimi Ebienfa , ya sanya wa hannu a ranar Talata. Sanarwar ta ce jirgin Air Peace ne zai gudanar da jigilar, inda zai tashi daga Afirka ta Kudu da ƙarfe 1:30 na safe , inda ake sa ran zai sauka a Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Murtala Mohammed da ke Legas da misalin ƙarfe 6:30 na safe . Tun da farko dai Gwamnatin Tarayya ta gabatar da jirage huɗu na aikin kwaso 'yan Najeriya zuwa gida, inda ta dawo da ɗaruruwan mutane sakamakon hare-haren ƙiyayya ga baƙi (xenophobia) da kuma matsalolin tsaro da suka fa

Gwamnatin kano ta jaddada kudurin hukumar KHETFUN na inganta asibitocin jihar cike da gaskiya da rikon amana wajen kashe kudin hukumar.

Gwamnatin kano ta jaddada kudurin hukumar KHETFUN na inganta asibitocin jihar cike da gaskiya da rikon amana wajen kashe kudin hukumar. Babbar Sakatariyar hukumar ta Kano State Health Trust Fund (KHETFUND), Dakta Fatima Usman Zahraddeen ce bayyana hakan, yayin wata ziyarar tantance ayyukan da aka aiwatar bayan bayar da tallafi a Babban Asibitin Gwarzo, inda aka duba yadda aka aiwatar da ayyukan da darajarsu ta kai Naira miliyan 42,397,000. A yayin ziyarar, Babbar Sakatariyar hukumar, wadda Daraktan Ayyuka na Dakta Lawan Adamu ya wakilta, ta tabbatar da cewa an kammala ayyukan da suka haɗa da s

Najeriya da Amurka sun shirya hadin gwiwa domin karfafa tsaro da yaki da ta'addanci

Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ya gana da Mataimakin Sakataren Amurka, Frank Garcia, domin tattauna hanyoyin ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka. Taron ya mayar da hankali ne kan bunƙasa haɗin gwiwa wajen yaƙi da ta’addanci, inganta musayar bayanan sirri, da kuma ƙarfafa dabarun da ƙasashen biyu ke amfani da su wajen fuskantar barazanar tsaro. Bangarorin biyu sun kuma yi nazari kan irin ci gaban da aka samu a haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen, tare da jaddada muhimmancin ci gaba da haɗa kai domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a

Iran ta ce ta harbo jirgi mara matuƙi na Amurka a Bandar Abbas

Rundunar sojin Iran ta yi iƙirarin cewa dakarun tsaron sararin samaniyarta sun harbo wani jirgi mara matuƙi na Amurka a sararin samaniyar birnin Bandar Abbas da ke kudancin ƙasar. Kamfanin dillancin labarai na Mehr , wanda gwamnatin Iran ke da iko a kansa, ya rawaito cewa rundunar sojin ta ce an gano tare da lalata jirgin ne a yankin da ke tsakanin Bandar Abbas da Hajiabad , bayan tsarin tsaron sararin samaniyar ƙasar ya gano motsinsa. A cewar rundunar, an kakkaɓe jirgin ne yayin da dakarun tsaron sama ke mayar da martani ga abin da ta bayyana a matsayin hare-haren maƙiya da kuma ƙoƙarin kare

Amurka na da ƙarfin ƙwace iko da mashigar Hormuz

Tsohon babban kwamandan rundunar sojin Amurka mai kula da yankin Gabas ta Tsakiya ( CENTCOM ), Janar Frank McKenzie mai ritaya, ya ce sojojin Amurka na da ƙarfin da za su iya ƙwace iko da mashigar Hormuz idan shugaban ƙasar ya ba da umarnin yin hakan. A wata hira da kafar yaɗa labarai ta CBS , Janar McKenzie ya bayyana cewa irin wannan mataki zai buƙaci tura manyan jiragen ruwan yaƙin Amurka zuwa yankin. Ya ce, duk da cewa rundunar sojin ruwan Amurka ba ta nuna aniyar aiwatar da hakan a yanzu ba, tana da cikakken ƙarfin yin hakan idan bukatar ta taso. Kalaman tsohon kwamandan sun zo ne a matsa

Kotun Sudan ta yanke wa jagoran RSF Hemedti hukuncin ɗaurin rai da rai

Wata kotu da ke Port Sudan ta yanke wa jagoran rundunar Rapid Support Forces (RSF) , Mohamed Hamdan Dagalo , wanda aka fi sani da Hemedti , hukuncin ɗaurin rai da rai. Kotun ta yanke hukuncin ne a shari'ar da aka gudanar ba tare da Hemedti ya halarta ba, inda ta same shi da laifukan kisan ƙare dangi, aikata laifukan yaƙi, laifukan cin zarafin bil'adama , da kuma kai hare-hare kan fararen hula. Hukuncin, wanda aka yanke ranar Lahadi, 12 ga Yulin 2026 , shi ne mafi tsauri da aka taɓa yanke wa jagoran RSF tun bayan ɓarkewar yaƙin Sudan a shekarar 2023 . Shari'ar ta fi mayar da hankali kan kisan t

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin ƙara kuɗin jarrabawar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin ƙara kuɗin rajistar jarrabawar WAEC da NECO ga ɗaliban makarantun sakandire, domin ba da damar sake nazarin matakin tare da ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki. A cikin wata sanarwa da Ma'aikatar Ilimi ta Tarayya ta fitar, ta ce an ɗauki wannan mataki ne bayan shawarwari da ra'ayoyi da aka samu daga jama'a kan shirin. Tun da farko, ma'aikatar ta sanar da aniyar ƙara kuɗin rajistar jarrabawar daga naira 27,000 zuwa naira 50,000 , wanda aka shirya fara aiwatarwa daga shekarar 2027 . Ma'aikatar ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki da sauran matsalo

Sama da mutum 2,700 sun mutu sakamakon tsananin zafi a Ingila da Wales

Wani sabon bincike ya nuna cewa sama da mutum 2,700 sun rasa rayukansu sakamakon tsananin zafin rana da aka fuskanta a Ingila da Wales tsakanin watan Mayu da Yuni na wannan shekara. Masu bincike daga Jami'ar Imperial College London , tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da Yanayi ta Birtaniya da kuma Makarantar Kula da Lafiyar Al'umma ta London , sun bayyana cewa sauyin yanayi ya taka muhimmiyar rawa wajen tsananta zafin da ya haifar da waɗannan mace-mace. A cewar rahoton, mafi yawan mace-macen sun faru ne a lokacin da aka samu mummunar guguwar zafi a watan Yuni, lokacin da yanayin zafi ya kai di

Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa ta gano wasu 'yan ƙasashen waje uku da ke cikin mayaƙan ƙungiyar ISWAP

A cikin wata sanarwa da rundunar Operation Hadin Kai , mai yaƙi da Boko Haram da ISWAP a Arewa maso Gabashin ƙasar ta fitar, ta ce an gano mutanen ne bayan da sojoji suka ƙwato wata kyamara a yayin wani artabu da mayaƙan ISWAP a yankin Cross Kauwa da ke Jihar Borno. Sanarwar ta ce hotuna da bayanan da ke cikin kyamarar sun taimaka wajen gano mutanen uku. Daga cikinsu akwai wani Bafalasɗine mai suna Abu Ishaq , wanda rundunar ta ce shi ne babban mai horas da mayaƙan ƙungiyar. Haka kuma, an gano wani mai suna Abu Thaiba , wanda aka bayyana a matsayin likitan ISWAP. Sai kuma wani mutum na uku, wa

Birtaniya ta sanya rundunar IRGC ta Iran cikin jerin ƙungiyoyin ta'addanci

Gwamnatin Birtaniya ta sanar da sanya Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) cikin jerin ƙungiyoyin da aka haramta tare da ayyana ta a matsayin ƙungiyar ta'addanci. Matakin, wanda aka shafe shekaru ana muhawara a kansa a Birtaniya, ya biyo bayan kiraye-kirayen da wasu 'yan majalisa da 'yan siyasa suka dade suna yi na ɗaukar irin wannan hukunci. Gwamnatin ta ce ta ɗauki wannan mataki ne bayan wasu hare-hare da aka kai kan Yahudawan Birtaniya, tare da amincewar majalisar ƙasar da sabuwar dokar tsaron ƙasa da Firaminista Keir Starmer ya yi alƙawarin aiwatarwa. A baya, dokokin Birtaniy

Yawan adaden danyen man da Nijeriya ke samarwa yakaru da kaso mafi girma cikin sama da shekaru shida

Adadin ɗanyen man da Nijeriya ke samarwa ya kai mataki mafi girma cikin fiye da shekara shida a watan Yuni, inda ya zarce kason da ƙungiyar OPEC ta ware wa ƙasar. Rahoton Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya bayyana cewa ƙididdigar da hukumomin da ke sa ido kan fannin haƙo mai suka fitar a ranar Lahadi ta nuna cewa wannan ƙaruwa ta samo asali ne sakamakon daidaituwar ayyukan haƙo mai da kuma inganta tsarin bututun mai. A cewar rahoton, Nijeriya ta samar da gangar ɗanyen mai miliyan 1.56 a kowace rana a watan Yuni, adadin da ya haura gangar mai miliyan 1.5 a rana da OPEC ta amince ƙasar ta

Ina da burin komawa jami'a domin ci gaba da karatu bayan ya kammala harkokin kwallon kafa - Victor Osimhen

Tauraron ƙungiyar Super Eagles ta Najeriya, Victor Osimhen , ya bayyana cewa yana da burin komawa jami’a domin ci gaba da karatu bayan ya kammala rayuwarsa ta buga ƙwallon ƙafa. Osimhen ya ce duk da irin nasarorin da ya samu a harkar ƙwallo, ya yi imanin cewa ilimi na da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da rayuwa mai kyau bayan ritaya daga wasanni. Ya bayyana cewa yana son samun digirin jami’a domin ƙara ilimi da kuma shirya kansa don rayuwa bayan ƙwallon ƙafa. Dan wasan ya ƙarfafa matasa da sauran ‘yan wasa da su mai da hankali kan ilimi tare da sana’arsu, yana mai cewa ƙwallon ƙafa ba ta dawwa

Jamian yan sanda sun shirya gurfanar da Adeniyi adeyemi mutumin da ya kirkiri hukumar bogi da sunan fadar shugaban kasa

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya za ta gurfanar da Adeniyi Adeyemi a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ranar Talata bisa zargin kafa wata hukumar bogi da ya danganta da Fadar Shugaban Ƙasa. Ana zargin Adeyemi da bayyana kansa a matsayin Darakta Janar na wata hukuma mai suna Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC), wadda hukumomi suka ce ba ta da wata halastacciyar amincewa daga gwamnati. Shi da wasu mutum biyu na fuskantar tuhume-tuhume guda takwas da suka haɗa da ƙirƙirar takardun bogi, yin sojan gona da sauran laifuka masu alaƙa da yaudara. Binciken ‘yan sanda ya nuna c

Gwamnatin kano ta sha alwashin hukunta duk wanda aka samu da zagon kasa ga kokarinta na wadata asibitocin kano da magunguna

Shugaban hukumar Samar da magunguna ta Jihar Kano Pharm. Ghali Sule ne ya bayyana hakan ga manema Labarai, a yayin kaddamar da shirye shiryen da hukumar ta shirya don gudanar da bikin cikar Gwamna abba shakera uku da kokarin wadata Jihar kano da magunguna masu sauki a asibitoci. Bikin da hukumar ta Fara a safiyar yau a harabarta dake nan Kano, da aka soma da saukar Alfur'qani mai girma, don Nasarar Gwamnan da wanzuwar zaman lafiya a kano. Pharm. Ghali ya Kara da cewa, a ranar 14 za a gabatar da taron wayar da Kan mutane Kan aiyukan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya Samar a Jihar Kano a fannin lafi

Gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin kara kudin jarrabawar WAEC da NECO ga daliban sakandire ta kasar

Gwamnatin Tarayya ta sanar da dakatar da shirin ƙara kuɗin jarabawar Hukumar Shirya Jarabawar Kammala Makarantun Sakandare ta Yammacin Afirka (WAEC) da ta Hukumar Shirya Jarabawar Kammala Sakandare ta Kasa (NECO), domin sake nazarin batun tare da tuntubar masu ruwa da tsaki. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta fitar, inda ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne domin bai wa gwamnati damar yin cikakken nazari kan shirin kafin yanke hukunci na ƙarshe. Tun da farko, ma’aikatar ta sanar da aniyar ƙara kuɗin jarabawar daga N27,000 zuwa N50,000 , wanda aka shirya zai

FIFA na duba yiwuwar fadada gasar Kofin Duniya zuwa kasashe 64

Shugaban Hukumar Kwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA), Gianni Infantino, ya bayyana cewa hukumar na duba yiwuwar faɗaɗa gasar Kofin Duniya ta FIFA zuwa ƙasashe 64 masu halarta. Infantino ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da kafar yaɗa labarai ta Blue News ta ƙasar Switzerland, inda ya ce kwamitocin da abin ya shafa a cikin FIFA za su yi nazari tare da tattauna wannan shawara nan gaba kaɗan. A cewarsa, hukumar za ta bi dukkan matakan da suka dace kafin yanke hukunci kan yiwuwar ƙara yawan ƙasashen da za su halarci gasar. Idan aka amince da wannan shiri, zai kasance wani babban sauyi a tar

Dakarun Najeriya sunyi nasarar hallaka fitaccen dan bindiga a Zamfara Kachalla Sani Yellow

Sojojin Najeriya sun hallaka fitaccen jagoran ’yan bindiga, Kacalla Sani Yellow, a yayin wani mummunan artabu da suka yi da ’yan bindiga a Ƙaramar Hukumar Anka da ke Jihar Zamfara. Rahotanni sun ce an kashe Sani Yellow ne a lokacin wani samame da sojojin suka kai kan maboyar ’yan bindiga a yankin, inda aka yi musayar wuta mai tsanani tsakanin ɓangarorin biyu. Baya ga Kacalla Sani Yellow, rahotannin sun nuna cewa sojojin sun kuma kashe wasu daga cikin mabiyansa a wannan farmaki. Sai dai har yanzu ba a fitar da cikakken adadin ’yan bindigar da aka kashe ba. Har zuwa lokacin wallafa wannan labari

Kara kudin jarabawar WAEC da NECO zai kara yawan yaran da ba sa zuwa makarant a Najeriya- Atiku

Tsohon mataimakin Shugaban kasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya soki rahotannin da ke cewa Gwamnatin tarayya ta amince da sanya kuɗin jarabawar WAEC da NECO zuwa N50,000 ga kowane ɗalibi daga shekarar 2027. A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce wannan mataki tare da ƙarin kuɗin makarantun Unity Colleges zai ƙara jefa iyaye cikin wahala tare da hana miliyoyin yara samun ilimi. Ya bayyana cewa Najeriya na daga cikin ƙasashen da ke da mafi yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, yana mai cewa ƙara

Wannan kamen ya biyo bayan wani kwantan ɓauna da maharan suka yi wa jami'an tsaro, amma dakarun suka fatattake su.

Hukumomin tsaron Jamhuriyar Nijar sun sanar da samun nasara a yankin Diffa da ke kudu maso gabashin kasar, inda dakarun haɗin gwiwa suka yi nasarar cafke wasu ƴan bindiga 8 da suka kai hari. Wannan kamen ya biyo bayan wani kwantan ɓauna da maharan suka yi wa jami'an tsaro, amma dakarun suka fatattake su. Baya ga kama mutanen, jami'an tsaron sun yi nasarar kwace miyagun makamai masu tarin yawa, da sauran kayan yaki da ƴan ta'addan ke amfani da su wajen addabar al'ummar da ke makwabtaka da tafkin Chadi. An gudanar da wannan aiki ne a yankin kan iyaka da Najeriya, biyo bayan harin da aka kai wa o

Jami'an tsaro a zamfara sun kashe kacalla sani yellow, kasurgumin Dan ta'adda

Mafarauta da hadin gwiwar rundunar JTF sun kashe wani fitaccen shugaban ‘yan bindiga da aka fi sani da Kachalla Sani Yellow. An kashe shugaban ‘yan bindigar a ƙaramar hukumar Anka ta Jihar Zamfara bayan musayar wuta, inda suka jami'an tsaron suka dakushe wani hari da ‘yan bindigar sukayi yunkurin kai wa. Kachalla Sani Yellow na daga cikin manyan kwamandojin ‘yan bindiga masu tasiri da suka addabi ƙananan hukumomin Anka, Bukkuyum da Maru a Jihar Zamfara. An ce marigayi Kachalla Sani Yellow yana cikin kwamandojin ‘yan bindigar da suka jagoranci hare-haren haɗin gwiwa kan Mutanen da basu ji ba ku