AMMASCO RADIO NEWSROOM

Labarai

FIFA Ta Fara Bincike Kan Rikicin Da Ya Biyo Bayan Wasan Ƙarshe Na Kofin Duniya

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) ta sanar da fara bincike kan rikicin da ya biyo bayan wasan ƙarshe na gasar cin Kofin Duniya. Hukumar ta ce ta miƙa batun ga kwamitinta na ladabtarwa domin gudanar da cikakken bincike kan abin da ya faru a filin wasa na MetLife bayan kammala wasan. FIFA ta bayyana cewa idan binciken ya tabbatar da laifin wani ɗan wasa ko jami'in tawaga, za a ɗauki matakin ladabtarwa da ya dace bisa tanadin dokokinta. Haka kuma, ana iya ɗaukar mataki kan Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Argentina idan an tabbatar da cewa tawagarta ta karya ƙa'idojin gasar. Rahotanni sun ce bayan Spa

Shugaban La Liga Ya Yi Kira Ga Gianni Infantino Ya Sauka Daga Muƙaminsa

Shugaban gasar La Liga ta Spain, Javier Tebas, ya yi kira ga Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA), Gianni Infantino, da ya sauka daga muƙaminsa. Tebas ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da jaridar La Gazzetta dello Sport ta Italiya, inda ya zargi Infantino da ɗaukar wasu matakai da, a cewarsa, ke iya yin illa ga tafiyar hukumar FIFA. Ya kuma soki wasu sauye-sauyen da aka yi a gudanar da wasanni, ciki har da yawaitar hutun shan ruwa, wani ƙarin hutu da aka yi a wasan ƙarshe bayan kammala mintuna 45 na farkon wasa, da kuma batun janye jan katin da aka bai wa ɗan wasan Amurka, Fol

Macron Ya Yaba Da Dokar Hana Ƙananan Yara Amfani Da Kafafen Sada Zumunta A Faransa

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya yaba da amincewar Majalisar Dokokin ƙasar da wata doka da za ta hana yara masu ƙasa da shekara 15 amfani da kafafen sada zumunta. A cikin wani saƙo da ya wallafa tare da wasu bidiyo da ke nuna wasu matsalolin da matasa ke fuskanta, ciki har da matsalolin lafiyar kwakwalwa da na cin abinci, Macron ya ce Faransa ta ɗauki matakin ne domin kare yara daga illolin da ke tattare da amfani da kafafen sada zumunta. Ya ƙara da cewa ƙasar na ƙoƙarin jagorantar sauran ƙasashen Turai wajen samar da ingantattun matakan kare matasa a duniyar intanet. A ƙarƙashin dokar, k

Rahotanni Sun Ce Amurka Da Saudiyya Sun Cimma Yarjejeniya Kan Makamashin Nukiliya

Kafafen yaɗa labarai na Amurka sun ruwaito cewa gwamnatin Shugaba Donald Trump ta cimma wata yarjejeniya da Saudiyya kan haɗin gwiwa a fannin makamashin nukiliya, kuma ana sa ran za a bayyana cikakkun bayananta nan ba da jimawa ba. Rahotannin sun nuna cewa yarjejeniyar za ta iya bai wa Saudiyya damar bunƙasa sarrafa sinadarin uranium domin amfani da shi wajen samar da makamashin nukiliya. Batun yarjejeniyoyin makamashin nukiliya tsakanin ƙasashe ya daɗe yana haifar da muhawara, musamman dangane da matakan da ake ɗauka na hana amfani da fasahar wajen ƙera makaman nukiliya. Wasu daga cikin 'yan

Nijar, Mali Da Burkina Faso Sun Nemi Karɓar Baƙuncin AFCON 2032

Ƙasashen Jamhuriyar Nijar da Mali da Burkina Faso sun miƙa takardar haɗin gwiwa ta neman karɓar baƙuncin gasar cin Kofin Nahiyar Afirka, AFCON, ta shekarar 2032. Jami'an ƙasashen uku sun gabatar da takardar buƙatar ga Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF), Patrice Motsepe. Ganawar ta gudana ne a birnin New York na Amurka, inda shugabannin hukumomin ƙwallon ƙafa na ƙasashen uku suka halarta tare da Kanar Djibrilla Hima Hamidou, wakilin Nijar a Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA). Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Mali (FEMAFOOT) ta sanar da wannan mataki a ranar Talata, tana mai cewa manufar ne

Kotu A Ghana Ta Daure Wani Matashi Kan Yunƙurin Satar Motar 'Yan Sanda

Wata kotu a Ghana ta yanke wa wani matashi mai shekara 26, Ebenezer Frimpong, hukuncin ɗaurin wata ɗaya a gidan yari bayan samunsa da laifin yunƙurin satar motar 'yan sanda. Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a watan Afrilu lokacin da matashin ya shiga wata motar sulke ta 'yan sanda tare da fara tafiya da ita, bayan direban motar, Joshua Denkyi, ya tsaya a wani kantin sayar da magunguna domin saye. Direban motar ya bayyana cewa matashin ya yi amfani da damar da ya samu yayin da ya fita daga motar, inda ya yi ƙoƙarin guduwa da ita. Sai dai jami'an 'yan sanda sun bi motar tare da kama matashin

Gwamnatin Tarayya Ta Gargadi Jama'a Kan Wata Farar Kumfa Da Ta Bayyana A Hanyar Kaduna–Abuja

Gwamnatin Tarayya ta gargadi jama'a da su guji taɓa wata farar kumfa da ta bayyana a gefen babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja, bayan zargin cewa wata mota mai ɗaukar kaya ta zubar da wani sinadari a wurin. Hukumar Kula da Ka'idojin Muhalli ta Ƙasa (NESREA) ta ce ta fara bincike domin gano musabbabin samuwar kumfar da kuma tabbatar da ko tana da haɗari ga lafiyar jama'a ko muhalli. A cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktan Yaɗa Labarai ta hukumar, Nwamaka Ejiofor, ta fitar, an ce jami'an NESREA daga ofishin Kaduna sun ziyarci wurin domin gudanar da bincike. Sanarwar ta ce tawagar ta gana da Kw

Farashin Ɗanyen Mai Ya Ƙaru Sakamakon Fargabar Rikicin Gabas ta Tsakiya

Farashin ɗanyen mai na ci gaba da ƙaruwa a kasuwannin duniya yayin da rikici ke ƙara tsananta a yankin Gabas ta Tsakiya. A yau Talata, farashin mai ya ƙaru da kusan kashi biyu cikin ɗari, inda ya kai matakin da ba a gani ba cikin makonni biyar. Rahotanni sun nuna cewa farashin ɗanyen man Brent ya haura dala 92 kan kowace ganga, yayin da na West Texas Intermediate, wato WTI, ya haura dala 84 kan ganga. Masana sun danganta wannan hauhawar farashi da fargabar yiwuwar tangarɗa ga samar da makamashi daga yankin Gabas ta Tsakiya, sakamakon rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran, da kuma barazanar da

Majalisar Wakilai Ta Ƙaddamar da Tsarin Ƙara Bai Wa Mata Damar Shiga Siyasa – Tajudeen Abbas

Kakakin Majalisar Wakilan Tarayya, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, ya bayyana cewa Majalisar ta samar da wani tsari na musamman da ke da nufin ƙara bai wa mata damar shiga harkokin siyasa da kuma tsayawa takara a Najeriya. Abbas ya ce sabon tsarin zai bambanta da yadda ake gudanar da tsarin takara ga sauran ’yan siyasa, inda za a fara aiwatar da shi a matsayin gwaji na wasu shekaru kafin a tantance tasirinsa da yadda ya dace da tsarin siyasar ƙasar. Ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin Majalisar na inganta wakilcin mata a matakan shugabanci da kuma ƙarfafa shigarsu cikin harkokin siyas

Rabiu Musa Kwankwaso Ya Ce Peter Obi Ya Amince Zai Yi Wa'adi Ɗaya Idan Ya Ci Zaɓe

Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar a zaɓen 2027, Peter Obi, ya sanya hannu kan wata yarjejeniya da ta tanadi cewa zai yi wa'adi ɗaya kacal idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa. Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi a shirin Politics Today na tashar Channels Television a ranar Litinin. A cewarsa, yarjejeniyar na daga cikin tubalan haɗakar siyasar da jam'iyyar ta gina domin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027. Ya kuma bayyana cewa yana da cikakken yaƙinin Peter Obi zai

Drake Ya Yi Asarar Dala Miliyan 1.5 A Caca Bayan Hasashen Argentina Ya Faskara

Fitaccen mawakin Kanada, Drake, ya yi asarar dala miliyan 1.5 bayan hasashen da ya yi cewa Argentina za ta lashe gasar cin Kofin Duniya ta FIFA ta 2026 bai cika ba. Rahotanni sun ce Drake ya sanya wannan kuɗi ne a caca kafin wasan ƙarshe, yana goyon bayan Argentina. Sai dai Sifaniya ta yi nasara a wasan, lamarin da ya sa ya rasa kuɗin da ya saka. Bayan kammala wasan, mutane da dama a shafukan sada zumunta sun sake tayar da batun abin da ake kira "Drake Curse" , wato zargin cewa duk ƙungiya ko ɗan wasa da Drake ya nuna wa goyon baya a manyan wasanni kan gamu da rashin nasara. Sai dai babu wata

Fantami Ya Bayyana Abin Da Zai Fi Ba Muhimmanci Idan Ya Zama Gwamnan Gombe

Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya bayyana cewa idan ya samu damar zama Gwamnan Jihar Gombe, zai mayar da hankali wajen amfani da ilimi da fasahar zamani domin magance matsalar rashin tsaro da kuma bunƙasa ci gaban jihar. Pantami ya ce gwamnatin da zai jagoranta za ta yi amfani da ƙwarewa da fasaha wajen inganta tsaro, jawo masu zuba jari, bunƙasa tattalin arziki da samar da damarmaki ga matasa. Ya kuma bayyana cewa gogewar da ya samu a matsayin shugaban Hukumar NITDA da kuma Ministan Sadarwa za ta taimaka masa wajen aiwatar da manufofin ci

Iran Ta Yi Iƙirarin Kashe Sojojin Amurka A Hari Da Ta Kai Jordan

Rundunar Juyin Juya Halin Iran (IRGC) ta yi iƙirarin cewa harin da ta kai kan wani sansanin da sojojin Amurka ke amfani da shi a yankin Rukban na ƙasar Jordan ya yi sanadiyyar mutuwar wasu sojojin Amurka. A cikin wata sanarwa, rundunar ta ce harin na daga cikin ayyukan soja da take ci gaba da gudanarwa kan wuraren da ake jibge sojojin Amurka a yankin, sai dai ba ta bayyana adadin waɗanda ta ce sun mutu ba. A nata ɓangaren, Ma'aikatar Tsaron Amurka (Pentagon) ta tabbatar da mutuwar sojojin Amurka uku da kuma jikkatar kusan sojoji 100 sakamakon hare-haren da Iran ta kai. Sai dai gwamnatin Amurka

Cutar Ebola Ta Bazu Zuwa Yankuna 47 A Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo

Cutar Ebola da ke ɓulla a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ta bazu zuwa yankunan kiwon lafiya 47 da ke faɗin larduna biyar na Adja a lardin Ituri, a cewar hukumomin lafiya. Alƙaluman da aka fitar a ranar 19 ga Yuli sun nuna cewa an tabbatar da mutum 2,423 sun kamu da cutar, yayin da mutum 967 suka rasu, lamarin da ya sa adadin mace-macen ya kai kusan kashi 39.9 cikin 100. A cikin sa'o'i 24 da suka gabata, an samu sabbin mutum 79 da suka kamu da cutar, tare da mutuwar mutum 37, inda mafi yawansu suka fito daga lardin Ituri. Rahotannin sun nuna cewa yankunan Bunia, Nizi, Rwampara da Adja ne suka

Tinubu Ya Amince Da Naɗin Sabbin Shugabanni Da Mambobi A Hukumomin Tarayya

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da naɗin sabbin shugabanni da mambobi 26 a hukumomi da kwamitocin gwamnatin tarayya guda 10. Daga cikin waɗanda aka naɗa akwai tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose, wanda zai jagoranci Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Karkara (REA). Haka kuma, Manjo Janar Junaid Bindawa ya zama shugaban Hukumar Albashi da Tsarin Albashin Ma'aikatan Ƙasa. Sauran naɗe-naɗen sun haɗa da Dr. Abuh Mohammed a matsayin Darakta Janar na Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa (NPC), Dr. Akinola Odeyemi a matsayin shugaban Kamfanin Ciniki da Wutar Lantarki na Najeriya (NBET), da kuma Dr. A

ICPC Ta Gurfanar Da Wani Likita Bisa Zargin Ƙirƙirar Rahoton Lafiya Na Bogi

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta gurfanar da Farfesa Bello Abubakar a gaban kotu bisa zargin ƙirƙirar rahoton lafiya na bogi. A cewar hukumar, ana zargin Farfesa Bello Abubakar, wanda aka bayyana a matsayin likitan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da ƙirƙirar rahoton ne domin tallafa wa El-Rufai wajen kauce wa gurfana a kotu. ICPC ta ce an shigar da ƙarar ne bisa zargin aikata laifukan da suka shafi gabatar da takardun bogi da kuma kawo cikas ga tsarin shari'a. Ana sa ran kotun za ta ci gaba da sauraron shari'ar domin tantance zarge-zargen da ake yi, yayin da ake ci g

Gwamnan Jigawa Ya Nuna Rashin Jin Daɗi Kan Rashin Zuwa Aiki Da Wuri

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya nuna rashin jin daɗinsa kan rashin halartar aiki da wuri da wasu manyan jami'an gwamnati suka yi bayan wata ziyarar bazata da ya kai Sakatariyar Gwamnatin Jihar da ke Dutse. A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Garba Muhammad, ya fitar, an ce gwamnan ya tarar da ofisoshin wasu manyan jami'ai a kulle, yayin da da dama daga cikinsu ba su halarci aiki ba har zuwa misalin ƙarfe 11 na safe. Sanarwar ta ce ziyarar na daga cikin rangadin sa ido da gwamnan ke yi domin duba yadda ma'aikata ke kiyaye lokaci, halartar

NSCDC Ta Bankado Jami'ar Bogi A Wani Gida Mai Dakuna Uku A Legas

Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) ta bankado wata jami'ar bogi da ke aiki a cikin wani gida mai dakuna uku a yankin Ilado, da ke ƙaramar hukumar Olorunda LCDA a Jihar Legas. Hukumar ta ce ta ceto matasa 106 da ake zargin an yaudare su da sunan ba su gurbin karatu, tare da kama wanda ake zargi da kasancewa mamallakin cibiyar bayan gudanar da binciken sirri da ya kai ga kai samame a safiyar Litinin. Binciken farko ya nuna cewa cibiyar ba ta da rajista, ba ta da sahihin suna ko harabar jami'a, amma tana tallata kanta ta intanet a matsayin cibiyar koyon karatu ta nesa mai alaƙ

Tinubu Ya Bukaci ECOWAS Ta Ɗauki Mataki Kan Hare-haren Ƙyamar Baƙi A Afirka Ta Kudu

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci ƙasashen da ke ƙarƙashin Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) su haɗa kai wajen yin Allah wadai da hare-haren ƙyamar baƙi da ake kai wa 'yan Najeriya da sauran 'yan Afirka a ƙasar Afirka ta Kudu. Tinubu ya ce ya kamata ECOWAS ta gabatar da batun a gaban Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) domin a ɗauki matakin gaggawa kan lamarin. An bayyana wannan matsaya ne ta bakin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, yayin taron shugabannin ECOWAS karo na 69 da aka gudanar a birnin Freetown na ƙasar Saliyo. A cewarsa, gwamnatin Najeriy

Kwamishinan 'Yan Sandan FCT Ya Gargadi Jama'a Kan Binciken Wayoyi Ba Bisa Ka'ida Ba

Kwamishinan 'Yan Sandan Babban Birnin Tarayya (FCT), Ahmed Sanusi, ya gargadi mazauna Abuja, musamman matasa, da kada su amince jami'an tsaro su binciki wayoyinsu yayin sintiri ko tsayawa domin bincike a kan hanya ba tare da bin ka'idojin doka ba. Ya ce umarnin Sufeto Janar na 'Yan Sandan Najeriya ya haramta wa jami'an 'yan sanda binciken wayoyin jama'a ba tare da bin ƙa'ida ba, sakamakon yadda wasu ke amfani da hakan wajen cin zarafi da kuma karɓar rashawa. Ahmed Sanusi ya bayyana cewa binciken waya na iya gudana ne kawai idan an kama wanda ake zargi da aikata laifi bisa tanadin doka, sannan