Hana yara shan sukari na inganta lafiyar ƙwaƙwalwarsu
Wani sabon bincike ya nuna cewa rage yawan shan sukari ga yara tun daga haihuwa zuwa shekaru biyu na iya taimakawa wajen kare lafiyar ƙwaƙwalwa har zuwa tsawon shekaru masu yawa. Binciken, wanda masu bincike daga Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Hong Kong suka gudanar, ya yi nazarin tasirin ƙarancin sukari da aka samu a Birtaniya bayan Yaƙin Duniya na Biyu. Sakamakon binciken ya nuna cewa mutanen da suka taso a lokacin da ake taƙaita amfani da sukari a lokacin ƙuruciyarsu sun kasance da ƙananan yiwuwar kamuwa da cutar mantuwa (dementia) da kusan kashi 23 cikin ɗari , idan aka kwatanta da waɗanda s
