AMMASCO RADIO NEWSROOM

Labarai

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ingila Za Ta Janye Goyon Bayanta Ga Gianni Infantino

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ingila (FA) na shirin rubuta wa shugaban FIFA, Gianni Infantino, takardar sanar da janye goyon bayan da take ba shi, yayin da yake fuskantar ƙarin matsin lamba kan shirinsa na sayar da hannun jari a gasannin FIFA ga masu zuba jari masu zaman kansu. Matakin ya zo ne a daidai lokacin da UEFA ke barazanar ɗaukar matakin shari'a kan shirin, yayin da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Wales ita ma ta bayyana janye goyon bayanta ga yunƙurin Infantino na ci gaba da shugabancin FIFA. Ana sa ran a watan Maris mai zuwa Infantino zai tsaya takara a karo na huɗu kuma na ƙarshe domin ci gaba d

Newcastle United Ta Sayi Mai Tsaron Raga Lukas Hornicek Daga Sporting Braga

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Newcastle United ta kammala ɗaukar mai tsaron raga Lukas Hornicek daga Sporting Braga kan kuɗi kimanin fam miliyan 25.7. Ko da yake Newcastle ta riga ta ɗauki matashin mai tsaron raga Ewen Jaouen mai shekaru 20 daga ƙungiyar Reims a wannan bazarar, har yanzu ƙungiyar na neman ƙarin gogaggen mai tsaron raga domin ƙarfafa tawagarta. Hornicek, mai shekaru 24, ya isa sansanin horar da 'yan wasan Newcastle da ke ƙasar Spain a ƙarshen mako, inda ya kammala gwajin lafiya tare da sanya hannu kan kwantiragin shekaru biyar. Rahotanni sun bayyana cewa Newcastle ta biya kuɗin da a

Mauricio Pochettino Ya Tsawaita Zamansa a Matsayin Kocin Tawagar Amurka Har Zuwa 2030

Mauricio Pochettino ya cimma yarjejeniya da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Amurka (US Soccer) domin ci gaba da zama kocin tawagar ƙwallon ƙafa ta maza ta ƙasar har zuwa shekarar 2030. Tsohon kocin Tottenham Hotspur da Chelsea, wanda ya karɓi ragamar jagorancin tawagar Amurka a watan Satumbar 2024, ya jagoranci ƙasar zuwa zagayen 'yan wasa 16 na gasar cin kofin duniya, kafin Belgium ta fitar da su daga gasar. Amurka na daga cikin ƙasashen da za su karɓi baƙuncin gasar cin kofin duniya ta FIFA, kuma ana kallon ci gaba da riƙe Pochettino a matsayin wani muhimmin mataki na shirye-shiryen ƙasar na dogon l

Jordan Henderson Ya Koma Chelsea Kan Kwantiragin Shekara Biyu

Ɗan wasan tsakiya na Ingila, Jordan Henderson, ya koma ƙungiyar Chelsea bayan rattaba hannu kan kwantiragin shekara biyu, sakamakon amincewar da aka yi na soke kwantiraginsa da Brentford. Henderson, mai shekaru 36, ya shahara a matsayinsa na kyaftin na Liverpool, inda ya jagoranci ƙungiyar ta lashe gasar Premier League a kakar 2019/2020. Haka kuma ya taimaka wa Liverpool ta lashe UEFA Champions League, FA Cup, League Cup sau biyu, UEFA Super Cup da kuma FIFA Club World Cup. A shekarar 2023 ya koma Al-Ettifaq ta Saudiyya, kafin daga bisani ya koma Ajax ta Netherlands a watan Janairun 2024. Daga

Fulham Ta Sayi Gonzalo Garcia da Cesar Palacios Daga Real Madrid

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Fulham ta kammala ɗaukar Gonzalo Garcia da Cesar Palacios daga Real Madrid, inda dukkansu suka rattaba hannu kan kwantiragin shekaru biyar. Gonzalo Garcia, mai shekaru 22, ya buga wa babbar ƙungiyar Real Madrid wasanni 39 a kakar wasan da ta gabata, inda ya zura ƙwallaye takwas a dukkanin gasa. Ɗan wasan gaban, wanda ya fara wakiltar babbar tawagar Spain a watan Yuni, zai sake haɗuwa da sabon kocin Fulham, Alvaro Arbeloa, wanda suka yi aiki tare a Real Madrid. Rahotanni sun ce cinikin nasa ya kai kimanin fam miliyan 34. Garcia, wanda ya kasance wanda ya fi kowa zura ƙw

Najeriya Ta Tura Sojoji 86 Zuwa Guinea-Bissau Domin Aikin Wanzar da Zaman Lafiya na ECOWAS

Rundunar Sojin Najeriya ta tura jami'ai 86 zuwa ƙasar Guinea-Bissau domin shiga aikin wanzar da zaman lafiya na Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS). A cewar rundunar, matakin na nuna ci gaba da jajircewar Najeriya wajen tallafa wa zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali a yankin Afirka ta Yamma. A cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafukanta na sada zumunta, ta bayyana cewa jami'an sun tashi daga Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, kuma sun isa Guinea-Bissau lafiya domin fara aikinsu ƙarƙashin umarnin ECOWAS. Rundunar ta kuma jaddada cewa Na

Majalisar Dokokin Kano Ta Amince da Ƙudirin Takaita Ƙarin Kuɗin Makarantun Masu Zaman Kansu

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da wani ƙudiri da zai hana makarantu masu zaman kansu ƙara kuɗin makaranta ba tare da samun izini da sahalewar hukuma ba, domin kare iyaye da masu kula da yara daga ƙarin kuɗaɗe ba tare da ƙa'ida ba. Ƙudirin gyaran Dokar Hukumar Kula da Makarantu Masu Zaman Kansu da na Sa-kai ta shekarar 2026 ya tanadi cewa duk wata makaranta da ke son ƙara kuɗin makaranta dole ne ta fara neman amincewar hukumar da abin ya shafa kafin aiwatar da hakan. Rahotanni sun nuna cewa duk wani ƙarin kuɗin makaranta da ya wuce kashi 10 cikin 100 zai buƙaci ƙarin nazari da sahalewa

Ƙungiyar kare haƙƙin bil-adama ta ƙasa da ƙasa, ta koka kan karancin malaman da ke koyarwa a sashin larabci da nazarin addinin muslunci muslunci a jami'ar Jos

Ƙungiyar kare haƙƙin bil-adama ta ƙasa da ƙasa, ta koka kan karancin malaman da ke koyarwa a sashin larabci da nazarin addinin muslunci muslunci na jami'ar Jos. Hukumar ta ce abin takaici ne yadda ake fuskantar koma baya a wannan bangaren, duk da hakkin da dokokin kare haƙƙin bil-adama suka yi tanadi a wannan bangare. Daraktan ƙungiyar kare haƙƙin bil-adama ta ƙasa da ƙasa Ambasada Abdullahi Bakoji Adamu, shine ya bayyana haka a wani sakon murya da aike mana. Ƙungiyar ta bukaci gwamanatin tarayya da sauran masu ruwa da tsaki da suyi duk mai yiwuwa wajen samar da mafita kan wannan kalubale.

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Borno ta kama mutane biyar kan zargin yanka matattun shanu da sayar da namansu ga mutane a birnin Maiduguri

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Borno ta kama mutane biyar kan zargin yanka matattun shanu da sayar da namansu ga ɗaiɗaikun mutane da mahauta masu tsire a birnin Maiduguri. Wannan na cikin sanarwar da Jami'in Hulɗa da Jama'a na Rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya fitar jiya litinin. Sanarwar ta bayyana cewa an kama waɗanda ake zargin ne a tsohuwar kasuwar shanu ta Maiduguri, bayan samun sahihan bayanan sirri, inda ake zarginsu da yanka shanun da suka mutu tare da sayar da namansu ga jama'a. Sanarwar ta ƙara da cewa a lokacin kama su, an same su da gawar matacciyar saniya da ake zargin suna shirin

Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya gargadi mutane kan tsallaka danja kafin ba da hannu

Gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya gargadi al'umma kan tsallaka danja kafin ba da hannu, tare da jaddada muhimmancin bin dokokin zirga-zirga. Daraktan Yaɗa Labaran Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana haka ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau talata. Sanarwar ta bayyana cewa gwamnan ya yi wannan gargaɗi ne yayin da ya shafe sama da awa ɗaya a mahadar Kofar Fanfo yana sa ido kan yadda masu ababen hawa kan bin danja. Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnan ya buƙaci direbobi, masu Adaidaita Sahu da masu tafiya a ƙafa su bi dokokin zirga-zirga domin kare rayuka da dukiy

Gwamnatin Jihar Kano ta yi kira ga yan kasuwa su saka hannun jari a fannin tsaftar muhalli domin inganta lafiyar da tattalin arzikin jihar

Gwamnatin Jihar Kano ta nemi ƴan kasuwa da masu zuba jari su saka hannun jari a fannin tsaftar muhalli domin inganta lafiyar al'umma, samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arzikin jihar. Wannan na cikin sanarwar da Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi naJihar, Dr. Dahiru Muhammad Hashim, ya fitar. Sanarwar ta ce Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da wani shirin haɗin gwiwa kan tsaftar muhalli da aka gudanar a otal din Porto Golf da ke Kano. Ya ce gwamnatin jihar na kallon tsaftar muhalli a matsayin wata dama ta bunƙasa tattalin arziki, inda ya bayyana cewa akwai damar zuba jari a

Sanata Rufai Hanga Ya Fice Daga Jam'iyyar NDC

Sanata Rufai Hanga, mai wakiltar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar NDC, jam'iyyar da tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ke jagoranta. A cikin wasiƙar murabus da ya aike wa shugabannin jam'iyyar ranar 3 ga Agustan 2026, Sanata Hanga ya bayyana cewa ya yanke shawarar barin jam'iyyar ne bayan dogon nazari da tunani kan makomarsa ta siyasa. Ya kuma gode wa shugabannin jam'iyyar da mambobinta a mazabar Dakata da ke ƙaramar hukumar Nasarawa a Jihar Kano bisa goyon baya, haɗin kai da kuma damar da suka ba shi a lokacin da yake cikinta. Sanatan ya

Yawan Maza Masu Ɗaukar Hutun Haihuwa Ya Haura Kashi 50% a Japan

Yawan maza da ke ɗaukar hutun haihuwa a Japan ya haura kashi 50 cikin 100 a karon farko, lamarin da ke nuna sauyin fahimta da al'adun aiki a ƙasar. Ma'aikatar Ƙwadago ta Japan ta bayyana cewa adadin ya ƙaru da kusan kashi 10 cikin 100 a shekarar da ta gabata, inda fiye da rabin maza ma'aikata suka amfana da hutun haihuwa domin kula da jariransu. Tsawon shekaru, gwamnatin Japan na ƙarfafa gwiwar iyaye maza su ɗauki wannan hutu tare da aiwatar da manufofi da shirye-shiryen tallafi domin inganta daidaito tsakanin aiki da rayuwar iyali. Manufar waɗannan matakai ita ce sauya tsohuwar al'adar wurare

KACRAN Ta Yi Allah Wadai da Hare-Haren 'Yan Bindiga a Zamfara, Sokoto da Katsina

Ƙungiyar Fulani Makiyaya ta Kullen Allah a Najeriya (KACRAN) ta yi Allah wadai da hare-haren da 'yan bindiga suka kai a jihohin Zamfara, Sokoto da Katsina, inda aka kashe mutane, aka ƙone wasu da ransu, tare da yin garkuwa da mutane da dama. A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar na ƙasa, Khalil Mohd Bello, ya sanya wa hannu, KACRAN ta bayyana hare-haren a matsayin rashin imani da kuma babbar barazana ga zaman lafiyar al'umma da wadatar abinci a Najeriya. Ƙungiyar ta yi kira ga 'yan bindiga da su gaggauta dakatar da kashe-kashe da sace mutane, tare da sakin duk waɗanda suke riƙe da su ba ta

Spotlight Education and Youth Development Initiative (SEYDI) ta shirya a North West University, Kano.

Taron ya gudana ne a ƙarƙashin jagorancin shirin Drug Abuse Awareness Campus Tour (DAACT), wanda ke yaƙi da wayar da kai kan illar shaye-shaye a jami'o'in ƙasar nan. An gudanar da shi a ɗakin taro na Hafizu Abubakar da ke jami'ar North West University, Kano. Da yake jawabi, shugaban SEYDI na shiyyar Arewa, Dr. Aliyu Bello Jikantoro, ya bayyana cewa an zaɓi jami'ar North West University ne saboda rahotanni da ke nuna cewa Jihar Kano na daga cikin jihohin da ke da yawan matasan da ke ta'ammali da miyagun ƙwayoyi a Najeriya. Masu ruwa da tsaki da dama kan yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi s

Iran Ta Kashe Mutane Biyu Da Aka Samu Da Laifin Yi Wa Isra'ila Leƙen Asiri

Hukumar shari'ar Iran ta sanar da aiwatar da hukuncin kisa kan Omid Behzad da Pouria Safvat a safiyar Litinin, bayan kotu ta same su da laifin yi wa Isra'ila leƙen asiri. A cewar kamfanin yaɗa labarai na ma'aikatar shari'ar Iran, Mizan , mutanen biyu sun kasance suna tattarawa tare da aika wa hukumar leƙen asirin Isra'ila, Mossad , bayanai, hotuna da kuma bayanan wuraren da cibiyoyin soji da na tsaron Iran suke. Mahukuntan Iran sun ce bayanan da aka tattara sun taimaka wajen gudanar da ayyukan leƙen asiri da suka shafi tsaron ƙasar. Sai dai ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama da wasu lauyoyi sun

Soja Da Ɗan Sanda Sun Mutu Yayin Daƙile Harin 'Yan Bindiga A Zamfara

Rundunar Operation FANSAN YAMMA ta ce wani jami'in soja da ɗan sanda sun rasa rayukansu yayin da suke daƙile wani hari da 'yan bindiga suka kai sansanin sojoji da ke Kasuwan Daji, a Ƙaramar Hukumar Kaura Namoda ta Jihar Zamfara. A cewar rundunar, maharan sun yi ƙoƙarin kutsawa cikin sansanin da misalin ƙarfe 1:40 na safiyar ranar 2 ga Agusta, amma dakarun da ke wurin sun gano yunƙurin tun da wuri tare da mayar da martani, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa. Bayan artabun, ƙarin dakaru sun bi sahun maharan, inda suka samu nasarar kuɓutar da mutum tara daga cikin mutanen da aka yi garkuwa

'Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 18, Ciki Har Da Sojoji Huɗu, A Zamfara Da Sakkwato

Aƙalla mutum 18, ciki har da sojoji huɗu, sun rasa rayukansu bayan wasu 'yan bindiga sun kai hare-hare a wasu al'ummomi da ke jihohin Zamfara da Sakkwato, a Arewa maso Yammacin Najeriya. A Jihar Zamfara, mazauna ƙauyen Kasuwar Daji sun ce maharan sun kai hari wani sansanin sojoji kafin daga bisani su kutsa cikin ƙauyen, inda suka yi garkuwa da fiye da mutum 100. Rahotanni sun ce daga baya maharan sun saki matan da suka kama, sai dai har yanzu ana ci gaba da tsare kusan maza 52. A Jihar Sakkwato kuwa, an ce 'yan bindigar sun shafe sa'o'i suna kai hare-hare gida-gida a ƙauyen Lajinge da ke Ƙaram

Mutum Takwas Sun Mutu A Sabbin Hare-haren Isra'ila A Gaza

Aƙalla mutum takwas ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren sama da Isra'ila ta kai cikin dare a sassa daban-daban na Zirin Gaza, kamar yadda jami'an Falasɗinawa suka bayyana. Hukumar Kare Fararen Hula ta Gaza ta ce hare-haren sun afku ne a Gaza City, Khan Younis da Deir el-Balah, inda aka kai hare-hare kan wasu gine-ginen zama. A nata ɓangaren, Sojojin Isra'ila (IDF) sun ce sun kai hare-haren ne kan mayaƙan Hamas, tare da iƙirarin kashe kwamandoji biyu na ƙungiyar, ciki har da ɗaya daga rundunar Nukbha da kuma wani daga Bataliyar Maghazi. Rahotanni sun nuna cewa daga cikin waɗanda suka mu

Hukumar Tace Fina-finai Ta Kano Ta Rufe Shagon Kausar Unique Empire Kan Zargin Talla Da Hotunan Batsa

Hukumar Tace Fina-finai da Ɗab'i ta Jihar Kano ta rufe shagon wani mashahurin mai sayar da magungunan gargajiya, Kausar Unique Empire Ltd , wanda aka fi sani da Kausar Mai Back to Back , bisa zargin amfani da kalamai da hotunan batsa wajen tallata hajojinsa a kafafen sada zumunta. A cikin wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar a madadin shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, an ce matakin ya biyo bayan bayanan sirri da kuma korafe-korafen da jama'a suka kai wa hukumar. Sanarwar ta ce sashen sa ido kan masu sayar da magungunan gargajiya ne ya gano lai