EFCC ta yi alkawarin lada har kashi 5% ga masu tona asirin dukiyar Najeriya
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (EFCC) ta ce mutanen da suka bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen gano dukiyar Najeriya da aka wawure tare da ɓoye ta a ƙasashen waje, na iya samun lada har zuwa kashi 5 cikin 100 na ƙimar dukiyar da aka ƙwato. Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya yi kira ga mutanen da ke da bayanan sirri kan inda aka ɓoye kuɗaɗe da kadarorin Najeriya a ƙasashen waje da su fito su miƙa bayanan ga hukumomin da abin ya shafa. Olukoyede ya bayyana hakan ne yayin wani taro kan laifukan tattalin arziki da aka gudanar a Cambridge, Ingila, inda ya ce a ƙarƙashin
