AMMASCO RADIO NEWSROOM

Labarai

Sarkin Kano Sanusi II ya jagoranci Sallar Gani a karon farko

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II , ya jagoranci Sallar Gani a birnin Kano a karon farko, yayin da ɗaruruwan mahaya dawakai suka fito domin gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W). Sallar Gani wata tsohuwar al’ada ce da Masarautar Kano ke gudanarwa domin tunawa da zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W), tare da nuna al’adun gargajiya da tarihin masarautar. A bana, an gudanar da hawan na tsawon kwanaki biyu, inda Sarkin Kano ya zagaya sassa daban-daban na birnin tare da rakiyar masu sarauta da mahaya dawakai, yayin da dubban mutane suka fito domin kallon bi

Turkiyya, Saudiyya da Pakistan sun fara tattaunawar yarjejeniyar tsaron juna

Ministocin harkokin waje da manyan jami’an tsaro daga Turkiyya, Saudiyya da Pakistan sun gudanar da taronsu na farko a Istanbul ranar Litinin, 31 ga Agusta, kan yarjejeniyar tsaron juna da ƙasashen suka rattaba hannu a kanta a Makka. Taron ya samu halartar manyan jami’ai da suka haɗa da Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan , Ministan Harkokin Wajen Saudiyya Faisal bin Farhan , da Ministan Harkokin Wajen Pakistan Muhammad Ishaq Dar , tare da manyan jami’an tsaro da hafsoshin sojojin ƙasashen uku. Kasashen sun rattaba hannu kan Yarjejeniyar Tsaron Juna ta Makka kimanin makonni uku da suk

An sayar da kujerun aikin Hajjin 2027 gaba ɗaya a Kano

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da cewa an sayar da dukkan kujeru 3,050 da aka ware wa jihar domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2027 . Babban Daraktan Hukumar, Abubakar Ibrahim Matawalle , ya ce an samu nasarar ne bayan da hukumar ta buƙaci maniyyatan da ke buƙatar kujerun su gaggauta biyan kuɗaɗen Hajji tare da kammala dukkan takardun da ake buƙata. Ya bayyana cewa akwai sama da mutum 200 da ke jiran samun gurbi idan wasu daga cikin waɗanda suka samu kujeru suka gaza cika sharuddan tafiya. Matawalle ya kuma gargaɗi waɗanda suka biya kuɗin Hajji amma ba su gabatar da fasfo

IRGC: Babban jirgin dakon mai ya taka nakiyoyi biyu a mashigar Hormuz

Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran, IRGC, ta ce wani babban jirgin dakon mai ya kama da wuta tare da tsaya wa cak, bayan ya taka nakiyoyin ruwa guda biyu a kudancin mashigar Hormuz. A cewar rundunar, jirgin na ƙoƙarin bin wata hanya da ta ce an haramta amfani da ita. A wata sanarwa da kafafen yaɗa labaran Iran suka wallafa, IRGC ta ce duk wani jirgin ruwa da ya karya dokokin tsaron da ta gindaya a mashigar Hormuz na iya fuskantar irin wannan sakamako. Har yanzu ba a bayyana sunan jirgin dakon man ba, ko kuma ƙasar da yake ɗauke da tutarta. IRGC ta jaddada cewa dukkan jiragen ruwa da k

Ambaliyar Nepal: Mutum 903 sun mutu, 4,247 sun ɓace

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon mummunar ambaliyar ruwa a Nepal ya kai 903, yayin da wasu 4,247 suka ɓace. Hukumomin ƙasar sun tabbatar da mutuwar aƙalla mutum 903, yayin da ake ci gaba da aikin ceto da kuma neman dubban mutanen da har yanzu ba a san inda suke ba. Hukumomin kula da bala’o’i na Nepal sun ce adadin waɗanda suka ɓace ya ƙaru sosai, daga mutum 2,502 da aka sanar a ranar Lahadi zuwa 4,247. Daga cikin mutanen da ake nema akwai ’yan ƙasar Nepal 3,655 da kuma baki 592. Ambaliyar ta yi mummunar barna a yankunan da ke kusa da iyakar Nepal da China, inda ta lalata gidaje, hanyoyi d

Fiye da mutum 2,000 sun koma PDP daga APC, ADC da NDC a Yobe

Fiye da mutum 2,000 ne suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar PDP daga jam’iyyun APC, ADC da NDC a ƙaramar hukumar Nangere da ke jihar Yobe, gabanin babban zaɓen shekarar 2027. Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa an karɓi sabbin mambobin ne a wani taro da aka gudanar a Sabon Garin Nangere. Mamban kwamitin amintattu na PDP, kuma tsohon ɗan takarar Sanatan Yobe ta Kudu, Halilu Mazagane, ya ce mutum 500 daga cikin waɗanda suka sauya sheƙar sun fito ne daga APC, 1,300 daga ADC, yayin da 225 suka fito daga NDC. Mazagane ya yi kira ga sabbin mambobin da sauran magoya bayan jam’iyyar da su kasance m

Tinubu Ya Nemi Afirka Ta Ƙarfafa Haɗin Kai Da Tsaron Nahiyar

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga ƙasashen Afirka da su ɗauki matakan ƙarfafa haɗin kai, samar da mafita daga cikin gida da kuma inganta tsaron nahiyar. Tinubu ya bayyana waɗannan shawarwarin ne a taron musamman na Tarayyar Afirka (AU) da aka gudanar a Luanda, babban birnin Angola , inda Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya wakilce shi. A cewar Abdulaziz Abdulaziz, ɗaya daga cikin masu magana da yawun Shugaba Tinubu, shugaban na Najeriya ya gabatar da wasu shawarwari da ya ce za su taimaka wajen magance matsalolin tsaro da rikice-rikicen da ke addabar wasu ƙasashen A

Atiku Ya Soki Tafiyar Tinubu Zuwa Turai, Ya Ce Ƙasa Na Bukatar Shugabanci

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a zaɓen 2027, Atiku Abubakar, ya soki tafiyar Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zuwa Turai, yana mai cewa shugaban ƙasar ya zaɓi yin hutu ne a lokacin da Najeriya ke fuskantar manyan ƙalubale. Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa, inda ya ce yanayin da ƙasar ke ciki na buƙatar shugaban ƙasa ya kasance tare da al’ummarsa domin fuskantar matsalolin da suke addabar su. Ya ce duk da cewa shi ma ya taɓa yin tafiye-tafiye tare da zama a ƙasashen waje, akwai babban bambanci tsakanin tafiyar mutum mai zaman kansa da kuma ta shugaban ƙasa mai ci.

An kama wata mata Mrs. Iyabo Sowunmi, da zargin kokarin shigar da haramtattun miyagun kwayoyi gidan gyaran hali dake jihar Ogun

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya reshen Jihar Ogun ta kama wata mata, Mrs. Iyabo Sowunmi, bisa zargin ƙoƙarin shigar da wasu ƙwayoyi da ake zargin haramtattu ne zuwa Cibiyar Tsare Fursunoni da ke Ibara, Abeokuta, domin ɗanta, Dare Sowunmi, wanda ake tsare bayan yanke wa hukuncin kisa. Mai magana da yawun Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya, reshen Jihar Ogun, Olayinka Odukoya, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin. Odukoya ya ce an kama Sowunmi da misalin ƙarfe 1:33 na rana ranar Juma'a, 28 ga Agusta, 2026, yayin da ake gudanar da bincike

Karamar Hukumar Funtua ce ke kan gaba a yawan waɗanda ake zargin sun kamu da cutar mashako a Jihar Katsina

Karamar Hukumar Funtua ce ke kan gaba a yawan waɗanda ake zargin sun kamu da cutar mashako a Jihar Katsina, yayin da rahotannin cutar suka fito daga ƙananan hukumomi 29. Wannan na cikin sanarwar da Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Jihar Katsina ta fitar bayan taron manema labarai da aka gudanar. Sanarwar ta bayyana cewa, bayanan da aka tattara zuwa ranar 28 ga Agustan da muke bankwana da shi sun nuna Funtua ce ke da rahotannin da suka fi yawa, sai Kankia, Bakori, Katsina, Mashi da Daura. Mukaddashiyar Shugabar Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Jihar, Dr. Shaima’u Kabir Abba, t

An tsinci wata jaririya Sabuwar haihuwa da aka jefar da ita a cikin kwali a Benue

An tsinci wata jaririya da ake zargin an yi an jefar da ita a kwali jim kaɗan bayan haihuwarta a dajin Ashar da ke cikin yankin Wuese na Ƙaramar Hukumar Konshisha ta Jihar Benue. Rahotanni sun bayyana cewa an gano jaririyar, wadda ake kyautata zaton ta shafe kusan kwanaki uku a cikin dajin, a ranar Asabar inda wani mazaunin yankin, Madam Mbakasev Yisa, ta gano ta bayan da ta ji alamun cewa akwai alamun motsi a cikin kwali. An nade jaririyar da tufafi sannan aka sanya ta cikin kwali, inda ake zargin an samu tsutsotsi a kusa da jikinta, yayin da wani wari mai tsanani ke fitowa daga cikin kwalin.

Operation FANSAN YAMMA sun kashe wani babban mataimakin shugaban 'yan ta'adda tare da kwato bindigogi a jihar Katsina

Dakarun rundunar hadin gwiwa ta Arewa maso Yamma, karkashin Operation FANSAN YAMMA, sun yi nasarar ajalin wani babban mataimakin shugaban 'yan ta'adda tare da kwato bindigogi, alburusai da babura yayin wani samame a karamar hukumar Matazu ta jihar Katsina. An gudanar da samamen ne jiya asabar yayin da dakarun Sector 2 suka kutsa cikin wasu maboyar 'yan ta'adda da aka gano a yankin. A wata sanarwa da jami'in yada labarai na rundunar hadin gwiwar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya fitar yau Lahadi, ya ce dakarun sun fuskanci turjiya mai tsanani daga 'yan ta'adda dauke da makamai yayin samamen. Sai

Shugaba Tinubu zai bar Abuja a yau domin tafiya Turai don fara hutun makonni uku cikin hutunsa na shekara - shekara

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja a yau domin tafiya Turai, inda zai fara hutun makonni uku a matsayin wani bangare na hutunsa na shekara-shekara. Birnin Landan na Birtaniya ne zai kasance zangonsa na farko a wannan tafiya. Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar yau Lahadi. Sanarwar ta ce ana sa ran Tinubu zai dawo Nijeriya bayan kammala hutun, domin shiga cikin harkokin yakin neman zaben 2027.

’Yan Sandan Jigawa sun ƙwato shanu, babura da wasu kayayyaki a samame da suka gudanar a sassan jihar

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta kama mutane 17 kan zargin aikata laifuka daban-daban, tare da ƙwato shanu, babura da wasu kayayyaki a samame da ta gudanar a sassan jihar. Wannan na cikin sanarwar da Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa, SP Shiisu Lawan Adam, ya fitar. Sanarwar ta bayyana cewa, an kama mutanen ne a samame daban-daban da aka gudanar a ƙananan hukumomin Malam Madori, Gwaram, Garki, Kiyawa, Taura, Birniwa, Dutse, Ringim, Miga, Kazaure da Roni, bisa zargin sata, fasa shaguna, satar shanu, lalata kadarori da fashi da makami. Rundunar ta ce, daga cikin kayayyakin da aka ƙwa

Gwamnatin Jigawa ta fara gudanar da jarabawar da ta tsara ta kwamfuta ga mutum 2,370 da za a dauka malaman tsangayu

Gwamnatin Jihar Jigawa ta fara gudanar da jarabawar da ta tsara ta kwamfuta ga mutum 2,370 da aka tantance domin ɗaukar malaman makarantun Tsangaya 500 a faɗin jihar. Babban Sakataren Hukumar Ilimin Tsangaya ta jihar, Dokta Abubakar Maje Hamisu, ya ce mutane kusan 9,000 ne suka nemi aikin, amma aka tantance 3,500 bisa la’akari da wuraren da makarantun Tsangaya suke. Ya bayyana hakan ne yayin da ake gudanar da jarabawar, yana mai cewa an shirya ta ne domin tabbatar da ɗaukar ƙwararrun malamai da za su taimaka wajen shirin farfaɗo da tsarin ilimin Tsangaya. Ya ce daga cikin malaman 500 da za a ɗ

Ayatollah Mojtaba Khamenei na Iran, ya yi gargaɗi ga ƙasashen Larabawa kan dabarun rarrabuwar kai da amurka ke amfani da shi a yankin

Jagoran Juyin Juya Hali na Iran, Ayatollah Mojtaba Khamenei, ya yi gargaɗi ga ƙasashen Larabawa, inda ya bayyana cewa ƙasashen Amurka da Isra'ila na yin amfani da dabarun haifar da rarrabuwar kawuna domin raunana haɗin kan Musulmi. A cikin wata sanarwa ta musamman da ya fitar, jagoran ya jaddada cewa maƙiya suna amfani da farfaganda da maƙarƙashiya domin ganin sun gurɓata tsarin zamantakewar al'umma, musamman bayan fuskantar ƙalubale da suka sha a fagen fama. Tun bayan hawansa karagar mulki, sabon jagoran ya mayar da hankali wajen ƙarfafa dakarun ƙasar da kuma yin kira ga ƙasashen da ke maƙwab

Wani sabon rahoto ya bayyana cewa Najeriya ce ke kan gaba a fannin zuba jarin mai da iskar gas a Afirka,

Rahoton ya ce Najeriya ce ke kan gaba a fannin zuba jarin mai da iskar gas a Afirka, wanda jimillarsa ta kai dala biliyan 221 a faɗin nahiyar. Wannan ci gaba na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasashen duniya ke faɗi-tashin neman ingantaccen makamashi, lamarin da ke sake tabbatar da matsayin Najeriya a matsayin jagorar fannin makamashi a Afirka. Rahoton wanda kamfanin binciken makamashi na Industrial Info Resources ya fitar, ya nuna cewa a halin yanzu ana bin diddigin manyan ayyukan samar da mai da iskar gas sama da 800 a ƙasashen Afirka daban-daban. Wannan rahoto ya nuna yadda manyan kamfanonin ƙ

Kungiyar likitoci ta kasa ta bayyana fargabar ficewar wasu dalibanta dake daf da kammala karatunsu zuwa kasashen waje

Kungiyar Likitocin Najeriya (NMA) ta bayyana cewa wasu daliban likitanci na fara shirin barin Najeriya zuwa kasar waje tun kafin su kammala karatunsu, sakamakon rashin kyakkyawan yanayin aiki da makoma a fannin lafiya. Shugaban NMA, Farfesa Afekhide Omoti, ya ce wasu daliban na fara rubuta jarabawar cancantar aiki a kasashen waje tun lokacin koyon aikin likitanci, domin su samu damar yin hijira bayan sun kammala rajista. Omoti ya ce akwai bukatar Gwamnatin Tarayya ta inganta albashi, tsaro, kayan aiki da jin dadin likitoci domin dakile yawan barin kasar da kwararrun ma’aikatan lafiya ke yi. Sh

INEC ta fitar da Jerin sunayen mutane 12 dake neman takarar kujerar Gwamnan jihar Kwara a zaben 2027

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC ta bayyana sunayen ’yan takarar kujerar gwamnan Jihar Kwara guda 12 da mataimakansu, domin zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar a shekarar 2027. Hakan ya ya baiwa Yan takarar damar fara shirye-shiryen yakin neman zabe gabanin babban zaɓen ƙasa. INEC ta bayyana jerin sunayen ne a ofishin hukumar da ke Ilorin, babban birnin Jihar Kwara, a ranar Asabar, inda ’yan takarar suka fito daga jam’iyyun siyasa daban-daban. Hukumar ta bayyana Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kwara, Yakubu Danladi-Salihu, a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC, yayin da Bello

Yadda Yan bindiga suka save Sarkin Noman Kano Alhaji Yusuf Nadabo tare da kashe mutane uku a Chiromawa

’Yan bindiga sun kashe mutane uku, sun raunata biyar tare da sace Sarkin Noman Jihar Kano, Alhaji Yusuf Nadabo Chiromawa, a wani hari da suka kai garin Chiromawa da ke Karamar Hukumar Garun Malam. Shugaban Karamar Hukumar Garun Malam, Alhaji Aminu Salisu Kadawa, ya tabbatar da faruwar lamarin. Kadawa ya ce, ya samu rahoton shigowar ’yan bindigar garin da misalin ƙarfe 11:00 na daren Asabar, inda suka nufi gidan Sarkin Noman tare da yin harbe-harbe kan mai uwa dawabi, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane uku da raunata wasu biyar. Shugaban Karamar Hukumar ya bayyana cewa, waɗanda suka jik